← Book details Man Of The World Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 23

Sashe 6

Man Of The World Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A farfajiyar Comphany ɗin taga Hauwa'uh tsaye tana jiranta ƙarasawa tayi inda take tare da dafata tace"sorry sweetheart nabarki ke kaɗai tunɗazu".
sauke wata ajiyar zuciya Hauwa'uh tayi tare da cewa"bakomai ina nan ina tinanin Allah yasa ba wani abun yayimikiba dan bakiji yadda ƙirjina yariƙa dukan tara-tara ba tunda kika shiga".
tinanowa tayi da ya haɗa bakinsa da nata saurin tofar da miyawun bakinta tayi tare da saurin aro jarumta dankar Hauwa'uh tagane tace"kwantar da hankalinki ƙawata ba abinda yayimun kidena ɗaga hankalinki kinji".
"masha Allah se yanzu naji hankalina ya kwanta muje to gurin da ake bawa koya takardar can muji position É—inmu dakanan semu biya gidan É—inkinmu dan karmu rasa É—inki next week ne bikin Muneera Musa".
"toh muje".
nansuka nufi gurin da ake rabawa suna zuwa ana kiran sunan Hauwa'uh ansa tayi b tare data buɗaba tana jiran akira Inteesar a ƙarshe aka kira Inteesar suna ganin mutane nata farinciki zasu bar gurin sukaji wata mata tana cewa ƴar uwarta"daɗina da Comphany ɗinnan indai mutum yayi karatu to zesamu muƙami babba idan kuma iya matakin secondry gareka shine za'ah ɗauke a irinsu cleaners haka da massengers Comphany ɗinnan akwai adalci".
matsawa can gefe da mutane sukayi kowanne cikinsu yashiga buɗe takardarshi gabanta ya buga damm sakamakon cin karo da sunanta a matsayin cleaner ɗin office ɗin Namijin duniya wasu zafafan hawayene suka shiga sinitiri a idanunta cikin murna Hauwa'uh ta ɗago da niyyar magana taga halin da ƙawarta take ciki tayi saurin fisge takardar hannun Inteesar ta duba sosai taji bataji daɗiba cikin tausayin ƙawartata tace"kinga irin abinda nike faɗamiki ko a lokacinnan kika zage kikayimasa rashin kunya san ranki dama na faɗamiki baze barkiba wallahi duk gurinnan ba wanda yazo da karatun dayakai naki amma seyasa aka sakaki a matsayin cleaner a office ɗinsa".
"Sweetheart bana taɓajin ina danasani a abunda nayiwa wannan sakaran sema ƙaramun karsashi da yikeyi muje kinji".
tafaÉ—a tare da share hawayen dake zubomata "toh muje".
"congratulation Sweetheart kice kinzama sakatariyar Adam".
"nagode".
hararta Inteesar tayi nansuka jera suka tafi a bakin Comphany ɗin suka tsaya samun napep basu wani jima da tsayuwaba wata jibgegiyar mota tayi parking a gabansu wani matashin gentle guy ne yafito daga motar tare da zagayawa indasu Inteesar suke fuskarsa ɗauke da murmushi ba ƙaramun kyakyawa bane bakinsa ɗauke da sallama ya isa garesu haɗa baki sukayi gurin cewa"Wa'alaika salam".
"Æ´ammata ina zuwa haka be kamata haÉ—aÉ—É—un Æ´ammata kamarku suna tsaye rana na dukansuba bayan daka ganinku ba kalar shiga ranar bane".
murmushi sukayi gabaki É—ayansu Hauwa'uh tace"waya faÉ—amaka haka Malam".
"hmmm aiba se wani ya faÉ—amunba bayan ga zuciyata a kusa dake dole insani".
yaƙarasa zancensa yana kallon Inteesar dariya Hauwa'uh tayi tace"inko hakane kayi dace da zuciya mr kyau".
"aidama nasan zuciyata me kyauce kuzo muje inkaiku namanta ban faÉ—ama zuciyata sunanaba sunana Zaid".
"a'ah mungode me napep muke jira".
Inteesar da ke tinanin muzantata da Namijin duniya yike ce ta sauke wata ajiyar zuciya wadda tasa su Zaid saurin kallonta yace"dan Allah ku shiga nakaiku kinga dakanan nasan gidansu zuciyata".
Inteesar na shirin cewa a'ah taga Namijin duniya da anbuÉ—emasa mota ze shiga yana kallonsu tace"toh mushiga Hauwa'uh".
nanya buɗewa Hauwa'uh baya ita kuma ya buɗemata front seat tana ɗaga ido caraf idonsu ya sarƙe dana Namijin duniya ta taɓe baki tashige ya rife ya zaga ya shiga yajasu sauke ajiyar zuciya Namijin duniya yayi a zuciyarsa yace" to wannan kuma meye haɗinta dashi da har suka shiga motarsa kenan duk abinda nayimata bataji haushi ba kenan aiko dole da sake dukda bankai ƙarshen plan ɗinba".
ɗaukar wayarsa yayi ya tura text bayan 30mins wayarsa tayi ringing ɗagawa yayi tare da yin shiru daga ɗaya ɓangaren Ahmad yace"nagani amma kasan wani abu yarinyar nan taji haushi sosai ganinka ne yasa ta nunamaka bataji haushiba plan ɗinmu yafara tafiya sucessful wallahi".
"ok to semu cigaba".
nansukayi sallama ya kashe tare da cewa driver"mu tafi".
nansuka É—auki hanya.

Ɓangarensu Inteesar ko sun ɗanyi tafiya sannan Zaid yace"wacce unguwar zankaiku gimbiyata".
"Suleja".
"ok amma baki faÉ—amun sunanki ba".
"sunana Inteesar".
"nice name ".
shiru tayi sukaita hirarsu shida Hauwa'uh tayimasa kwatancen gurin me É—inki seda suka biya yabiya musu kuÉ—in É—inkinsu dukda basusoba suka yimasa godiya sannan suka É—auki hanyar gidansu daidai kwar gidansu ya tsaya yana gama parking suka buÉ—e suka fito hakan yasashi shima fitowa yana wasa da É—an key É—in dake hannunsa yace"Hauwa'uh se gobe kuma".
"eh Uncle Zaid".
"a'aaah godiya nike ƙawarmu ".
nantayimusu sallama ta wucetashiga gida kallon Inteesar yayi dake niyyar tafiya yace"ranki shidaÉ—e kitsaya inada magana".
"toh inajinka".
"da farko sunana Zaid a unguwar Garki nike sunan mahaifina Cheif Judge Muhammad Abdurrahman nagankine na yaba da nutsuwarki tunda naganki nafara murna nasamu muradin zuciyata ina fatan zaki karɓi soyayyata".
dammm gaban Inteesar yabayar lokaci ɗaya wasu hawaye da take ƙoƙarin ɓoyewa suka shiga silalomata domin tinda take ba'ah taɓa furtamata kalmar so ba se a ranar ganin haka Zaid bakaramun gigicewa yayiba yaɗauka bata sonsa cikin karayar zuciya yace"Inteesar karki cemun bakya sona ko ammiki miji".
wani murmushin farinciki dabata shirya yinsaba ya suɓucemata tayi saurin juyamasa baya tace"ba'ah mun miji ba ka kwantar da hankalinka nima ina sonka".
cikin jin kunya zata ruga kenan ya riƙe gefan hijab ɗinta tsayawa tayi murmushi Zaid yayi yace"godiya nike gimbiyata gobe wuraren ƙarfe nawa zaki fita gurin aikin".
shiru tayi seda taÉ—au lokaci da alama tinani take sannan tace"around 9:30 haka".
"okay gimbiyata kijirani nazo nakaiku sena wuce office".
"tom mungode".
"no wayarkifa".
"bani da waya".
"okay to bara na baki ƙaramar wayata kafin nasan yadda zanyi".
"toh".
nanya shiga mota ya ɗakko haɗe da bandir ɗin 1k ya miƙamata ƙin amsar kuɗin tayi seda ya zari guda biyar yabata sannan ta amsa sukayi sallama tashiga gida.

Ruƙayya da Uwar Gwarama dake raɓe tace"Innah kinga arziƙi ko gaskiya kisan yadda zakiyi inasonsa dan Allah kisan yadda zakiyi".
"kwantar da hankalinki Ruƙayya indai wannan mejan kunnen ne sekin aureshi hauka nike inbari ɗiyar Amina tayi aure gidan hutu aiko zan rasa zanin ɗaurawa bazata auri wannan mutumin arziƙinba zakisha mamaki kidena wani ɗaga hankalinki aure dake dashi kamar da ƙasa muje ciki".
"yauwa Innah ta haka nike sonki Allah yabarmanake".
"Ameen".
nansuka shige tin daka zaure Uwar Gwarama take cewa"Malam! Malam!! Malam!!!".
fitowa Abbah yayi daka ban ɗaki a zabure hanunsa riƙe da buta yace"lafiya".
"inafa lafiya yanzu naga wannan me baƙin jinin da wani a mota yana lallatseta basusan ina kallonsu ba naga yabata dunƙulin kuɗi ta amsa ba sharri nikemata ba zakaga hannunta da kuɗi".
kallonta Abbah yayi zatayi magana yace"rifemun baki sakaran yarinya baki isa kin ɓatamun suna a gari ba ana ganin ƙimata ko waye yike tattaɓakin gobe kice indai dagaske yike sonki ya turo".
fuskarta na zubar da hawaye ta É—agamasa kai zata wuce kenan Abbah yace"munafuka kinbani kuÉ—in ko sena tattakaki".
miƙamasa tayi ya amsa ta wuce ɗakinsu .

AFTER ONE DAY

9:20min
Zaune take kusa da Khadija wayar da Zaid yabata tayi ƙara gabda zata tsinke ta ɗaga tare da cewa"Salamu Alaikum".
"wa'alaiki salam gimbiyata ina waje ina jiranku".
"toh gamunan".
nanya kashe miƙewa tayi tare da kallon Hauwa'uh daketa magana da Khadija tace"sarkin surutu yazo".
"toh muje".
nansuka yima Ummah sallama suka fita tadda shi sukayi tsaye gaisar dashi sukayi sannan suka hau motar suka nufi Comphany Namijin duniya dalilin traffic da suka samu basu suka isa ba se wuraren 10 yana saukesu sukayi sallama suka nufi cikin ma'aikatar a compound É—in gurin suka rabu kowa ya nufi gurin aikinsa.

Tana isa ƙofar da sakatariya take zaune taji mararta tashiga tsunkunamata cikin dakiya da dauriya ta buɗe ƙofar haɗa ido sukayi da sakatariya daketa shan ƙamshi tana ganin Inteesar ta haɗe rai tsaki Inteesar tayi tare da wucewa fuuu danna ƙofar tayi ta buɗe shiga tayi kanta a ƙasa tace"Salamu Alaikum".
ba tare daya amsa sallamartaba ya ɗago sexy eyes ɗinsa da sukayi kamar na mejin bacci ya zubamata cikin gadara da isa yace"yakamata kisan gurin aiki ba gurin nanaye bane da zaki riƙa hawa motar wani ƙato yana kawokiba sannan dama irin wannan lokaci yakamata cleaner yazo yayi aikinsa?".
sosai ciwon mararta ke ƙara ƙaruwa cikin sanyin jikin da ita kanta batasan tana dashi ba tace"kayi haƙuri traffic muka samu ne".
a gadarance yace"traffic ba uzuri bane da kin fito da wuri traffic ɗin ze tsaidake ne dan haka wannan ba uzuri bane dama ke ba albashi ɗaya zan riƙa biyanki da cleaners ba su dubu hamsin ne ke kuma dubu ashirin na zari kuɗin makarar da kikayi zan baki dubu sha shida gobema kinga bazaki ƙara bari ki makara".
yana ƙarasa faɗar haka ya miƙe ya fita tashi tayi dakyar saboda ciwon yafara cin ƙarfinta tashiga share gurin dukda taga alamar anyi shara ta goge tana cikin goge wata haɗaɗɗiyar farar kujera fara tass da ita ta miƙe kenan taji tana jin jiri saurin zama tayi kan kujerar tana maida numfashi bazato taji anbuɗe ƙofa saurin miƙewa tayi ganin Namijin duniya waigawar nan da zatayi taga duk tayi staining ɗin inda ta zauna da jini!!!!!!!

*Daka wannan update É—in zaku jini shiru saboda zamu fara exam bani zan koma rubutuba se 18/1/2022 dan Allah ku tayani share dan masu karatu su sani ngd.*

Votes and Comments
Plz share to others fisabilillah

_*Daga Alƙalamun ƴ🌻 *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)

*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*

HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…

*BOOK 1*

*PAGES* 0️⃣9️⃣➡️1️⃣0️⃣

Cikin matsanancin tashin hankali tayi saurin komawa ta zauna lokaci ɗaya zufa yashiga ketomata a zuciyarta tace"nashiga ukuna ni Aishatu na ɓatawa wannan jarababben mutumin kujera yazanyi wayyo Allah na Allah ka temakeni karya gani Allah kaɗaine yasan irin hukuncin dazemun wayyo Allah na haka nanma ya alah cika da wannan masifaffen mutumin bare na ɓatamasa farar kujerarsa Allah kaɗai yasan irin muzantani dazeyi Allah ka temakeni nashiga uku".
tana cikin zancen zucinnan É—aga idonnan da zatayi caraf suka haÉ—a ido da Namijin duniya yana jifanta da wani
irin wulaƙantaccen kallo me cike da zallar ƙyama da ƙasƙanci Step biyu zuwa uku ya taka zuwa inda take kafin ya tsaya tare da harɗe hannuwansa aƙirji yayinda sexy eyes ɗinsa suka kaɗa sukayi jawur dasu saboda tsananin ɓacin rai se huci yike kamar wani mayunwacin zaki ya tsaya a gabanta .
Chapter 6 · 0% Book details