← Book details Man Of The World Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 23

Sashe 17

Man Of The World Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka take tafiya domin idanun mutanen gurin gabaki ɗaya na kanta jiki a sanyaye taƙarasa step ɗin kanta a ƙasa ɓangaren Namijin duniya ko tunda ta fito ya kafeta da mayun idanunsa dake mugun bata tsoro harta tsaya a step ganin yadda tayi ƙasa da kanta ne yasa Namijin duniya taɓe baki a zuciyarsa yace"wai ita ala dole ace tanada kunya da tarbiyya".
a hankali ta ɗaga golden eyes ɗinta dake masifar tafiya da zukatan mutane taɗan saci kallon inda yike caraf suka haɗa ido gani tayi ya taɓe baki saurin janye idanunta tayi daga garesa zungurarsa Ahmad yayi yace"bakaga yadda mutuniyarka tayi bane dubeta a haka kamar mutuniyar kirki se rashin tarbiyya kala-kala a cikinta kamar kuɗin cizo batasan munkusa zuwa ƙarshen game ɗinba".
wani killer smile ya saki nan Adam ya cigaba da kiran sauran mutane ba sunan Feenerh ko ɗaya sede canzamata muƙami da akayi takoma sakatariyar Adam .

Ɓangaren Sakatariya Feenerh da Zuby ko mutuwar zaune sukayi ganin abubuwan da suke faruwa sosai ran Feenerh yakai ƙololuwar ɓaci tana huci ta zunguri Zuby da kamar zatayi kuka tace"nidai na rasa mena tsarewa wannan tsinanniyar yarinyar ne da bata da wani burin daya wuce taga bayana ƴar kujerar da nike taƙama da itama seda ta rabani da ita a tinanina da wannan kujerar yakamata nayi amfani gurin shawo kansa shine saboda ita tambaɗaɗɗiya ce tayimun haka dole wannan karon ta ɗanɗana kuɗarta domin sena nunamata na rigata zuwa duniya ko ta halin ƙaƙa senaga bayanta tsinanniya ƴar gidan masu dattin hula ƴar matsiyata ko nawane a shirye nike dana kashe matsawar zanga bayan wannan ƴar iska yarinyar".
"amma gaskiya kinyi sake wallahi Feenerh banyi zaton abun yayi ƙamari har haka ba aida nina ɗauki matakin dakaina amma ko yanzu bamu makaraba itaɗin banza duka yarinyar nawa take dako da ƙissa baki koreta ba saboda sakarci irin naki yanzu gashinan ta nunamiki ɗan hakin daka raina shike tsokalemaka ido domin koke kinƙi ɗaukar mataki akan wannan ƴar iskar yarinyar doleni naɗauka dan bazan taɓa barin wannan cin kashin data yimana ya tafi a banza ba wallahi".
taƙarasa zancenta cike da tsananin fusata hakan yasa Feenerh jin wani mugun sanyi a zuciyarta dan ita a tinaninta Zuby baƙaramin sonta take ba ganin yadda hankalin Zuby yayi mugun tashi hakan yasa Feenerh cike da kulawa da sigar lallashi tace"ki kwantar da hankalinki ƙawata muje gida muyi shawara da Ummah muga ta inda za'ah ɓullowa al'amarin".
wani shu'umin murmushi taƙara yi tare da cewa"kidena ma tinanin zanƙi ɗaukar mataki akan duk wani abu da yike niyyar yimun shamaki da samun farincikina muradin zuciyata wanda nikejin kamar danni akayisa a shirye nike dana kauda duk wani abu dake niyyar nisantani dashi ko ƙanwata Zarah ce tayimun haka wallahi senasa anɓatarmun da ita daka doron ƙasa domin a yadda nike jina yanzu haka na ƙuna bana tsoron ƙaure akan Namijin duniya banƙi inɓata da kowa ba".
cikin sigar kwarewa da harkar bariki Zuby ta ware ƙananun idanunta da suke kamar ankwantali duma tace"ƙawata kina nufin kenan zaki iya rabuwa dani".
"gaskiya Zuby baki da hankali kefa nacemiki ko iyayenane sena raba gari dasu bare wata ke tin yaushe da zanmanta dake infara sabuwar rayuwa matsawar zan mallaki Man of the world da dukiyarsa".
sosai maganganun Feenerh suka ɓatawa Zuby rai dake ƴar bariki ce seta nunamata kamar bataji komai ba ta ƙaƙalo wani munafikin murmushi wanda iyakacinsa fatar bakinta tace"maida wuƙar aminiyata nima da wasa nike miki aini ko da baki kika nuna abu kinaso bazan taɓa son abunba ko nawane abun ni me iya barmiki ce kinji tawan".
murmushin jindaÉ—i Feenerh tayi tace"godiya nike babbar aminiyata ".
wani shu'umin murmushi Zuby tayi wanda ita kaÉ—ai tasan ma'anarsa suka cigaba da hira.

Ana tashi daga taron Inteesar ta nufi gurin Hauwah jiki a sanyaye tace"anyako Besty ba wani abun suke shirya ba kuwa mutuminnan ba alheri a tare dashi inaji a jikina kamar wata muguntar suka shiryamun".
"banaso Besty kina munanawa mutum zato banajin sun baki wannan muƙamin dansu tozar taki face sedan kin cancanta ki kwantar da hankalinki tawan ki cigaba da addu'ah ba wanda ya isa yayimaka abinda Allah bemaka ba".
"hakane kam Bestyna nagode sosai da kulawarki gareni Allah yabarmu tare".
"Ameen ya Allah muyi mu tafi mu shirya kar Uncle Zaid yazo yayita jiranmu".
"toh aiko kinsan shi sede ya jiramu badai mu jirasa ba bara naje na tambayesa koda abinda zan masa".
"ok hakan yanada kyau nidai nariga da munyi sallama da Oga Ahmad bara injiraki a can".
taƙarasa zancenta ta maimata nuni da wata ƴar rumfar shaƙawata.
"toh".
nan kowaccensu ta tafi.

Bakinta ɗauke da sallama tashiga office ɗin jin shiru se ƙarar a.c daketa aiki yasata ɗagowa tashiga bin ko ina na office ɗin da kallo har lulu eyes ɗinta ya sauka kan wani tanƙamemen hofonsa sanye da wata haɗaɗɗiyar black arman suit sumar kansa tayi luf-luf da ita se ɗaukar ido take ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya bazato taji murmushin ya suɓucemata a hankali tashiga tafiya harta isa gurin ɗage tashiga yi ko hannunta zekai kan hoton dake hoton yaɗanyi sama sosai yasa dukda ɗagen datayi hannunta bekai ba shiru tayi harta juya sekuma ta fasa ta nufi gurin wata haɗaɗɗiyar resting chair ɗinsa me tayoyi ta turata daidai saitin photon ta tuɓe takalminta ta taka tsayinta yayi daidai da tanƙamemen photon lallausan hannunta tasa tashafa hoton cikin wani irin yanayin da batasan kona menene ba takai bakinta daidai saitin bakinsa tasakarmasa wani hort kiss tasaki wani sansanyan murmushi tare da ƙara kai lallausan hannunta kan photon daidai saitin hancinsa tace"sturborn kaidai baka da girma ko kaɗan sena jikinka".
taƙarasa zancenta tana mai ƙara sakarmasa wani hort kiss zata janye bakinta daga jikin photon kenan taji lion voice ɗinsa ta daki dodon kunnenta yace"inkin gama kiss ɗin kya iya sakkowa anga ɗan sangiri saurayi ba kamar ƙolon saurayinki ba ".
a ruɗe ta juya jiki na rawa zata sakko hakan yasa kujerar da take ta tafi zuuu zata faɗi sauri rife golden eyes ɗinta tayi domin tagama sadaƙarwa da zata faɗi tajita a jikin mutum ƙamshin turarensa ne ya tabbatar mata da shine a hankali tashiga buɗe oily eyes ɗinta ta saukesu kan kyakyawar fuskarsa kallon-kallo suka shiga yi na tsawon 5mins yayinda iskar damuna tashiga kaɗawa hakan yasa gabaki ɗayansu suka tsunduma cikin duniyar tinani buɗo ƙofar da akayi ne yasasu dawowa daga duniyar tinanin da suka shiga ganinsu a haka yasa ran Meemah yayi mugun ɓaci .

Ɓangaren Namijin duniya ko kallo ɗaya yayiwa Meemah data banko musu ƙofa ya ɗauke kansa jin Inteesar nata mutsu-mutsun ya sauketa yasashi ƙara matseta a faffaɗan ƙirjinsa gefe guda kuma cike da mugunta ya takemata ƙafa da haɗaɗɗen takalminsa sosai taji azabar yadda ya takemata ƙafa amma hakan be hanata mamakin abinda yikemata ba a zuciyarta tace"anyako wannan mutumin kanshi ɗaya kuwa".
lokaci ɗaya bugun zuciyarsa su yaƙaru saboda yadda ƙirjinsu ya haɗe guri ɗaya tana cikin zancen zuci taji muryarsa cikin wani shegen salo da batasan yanada shiba yace"sannu My Angel kiriƙa yimun a hankali da jikinki kinsan banaso kina wahalarmun da kanki saboda keɗin rayuwata ce badon nazo a lokacin daya dace ba daya kike tinanin za'ayi".
yaƙarasa zancensa tare da kashemata sexy eyes ɗinsa baki buɗe Inteesar ke kallonsa fuskar ɗauke da tsananin mamaki ganin yadda tayine yasashi gyaramata zama a ƙirjinsa yashiga caring ɗinta kamar kwai yayinda gefe guda kuma yaketa mitsitsikemata ƙafa ɓangaren Inteesar ko ba abinda take se al'ajabin abinda yike mata.

Ganin ƙofa a buɗe bakowa ne yasa Zuby cewa"yauwa Feenerh mushiga kawai ki basa haƙuri in wani abun kika yimasa yayi haƙuri ya maida ke muƙamunki ina ganin hakan zefi kuma a ganina wannan shine stage na farko da yakamata mubi domin se muna haɗawa da ƙissa Allah ma ya temakemu wannan makirar yarinyar bata nan komai zezomana da sauƙi".
"mu wuce kawai gobe na shawo kwalliya speacial domin bashi haƙuri".
cike da zaƙuwa Zuby tace"a'ah muje yanzu".
"toh tunda kin matsa mushiga É—in".
Feenerh taƙarasa zancenta suna shigewa cikin office ɗin sandarewa suka yi sakamakon ganin Namijin duniya rungume da Inteesar yana caring ɗinta itakuma tayi luf a faffaɗan ƙirjinsa kamar wata ƴar baby yayinda daka ƙasa kuma yake ƙara mutsitsike mata ƙafa.

Ɓangaren Namijin duniya ko yi yayi kamar besan da mutane a gurin ba hakan baƙaramun ƙara ɓatawa su Meemah da sukayi mutuwar tsaye rai yayi ba shiko ɗan gogan cigaba yayi da caring ɗin abarsa kamar wata matarsa saurin yin baya su Feenerh sukayi cikin tsananin ɓacin rai yayinda Meemah ma tabi bayansu zuciyarta na tafarfasa ta buga musu ƙofa da ƙarfi .

Mutsu-mutsu takeyi cike da tsananin ɓacin ran abinda yayimata a gaban mutane yayinda wasu hawaye suka shiga sintiri a kumatunta a zuciyarta tashiga tinanin wanne irin kallo mutanen nan zasu yimata ƙin sakinta yayi hakan yasa ta ƙara lafewa a ƙirjinsa wani ƙasaitaccen murmushi ya saki ganin yadda ta sakankance taƙara lafewa a jikinsa hakan yasa cike da mugunta ya hankaɗata ta faɗi ƙasa jikake ƙass ƙarar kashin ƙafarta yayi ƙara yayinda lokaci ɗaya ƙafar ta kaure da zugi ga tsamin da tayi cikin yanayi na jin zafi tace"ochhhhhh".
murmushin mugunta a gadarance yace"matsamun da wannan ƙazamun jikin naki dayasha taɓawar ƴan bariki kin wani lefe jikin mutum kina yin pretending kamar wata ta Allah bayan kuma a zuci ba haka bane kina wani kakkare jiki kamar wata uwar mata mezan gani abu kamar kwan kurciya".
yaƙarasa zancensa tare da ƙara shan mur kamar bashi yayi maganar ba ya wani ƙara haɗe rai ɗaga idonnan da zeyi sukayi ido huɗu da!!!!!!!!!

*Sorry my fans kuyi haƙurin da rashin typing yafaru ne saboda wani uzuri daya tasomun me ƙarfi amma yanzu na dawo normal zamu fara wasa kullum insha Allahu zaku fara samu update sau ɗaya ko biyu a rana matsawar zaku bani haɗin kai ta hanyar suburbuɗamun comments and votes zaku sha mamaki domin yanzu zan tsoma hannu cikin labarin dan shimfiɗa mukayi yanzu zamu fara wasan.*

Votes and Comments
Plz share to others

_*Daga Alƙalamu🌻 *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)

*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*

*BOOK 1*

*PAGES* 2️⃣5️⃣➡️2️⃣6️⃣
Chapter 17 · 0% Book details