← Book details Man Of The World Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 23

Sashe 13

Man Of The World Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

8:30Pm
Suka iso gurin dinner kallon Inteesar Hauwa'uh tayi ta ce"amma gaskiya besty kinga yadda kika yi kyau kuwa kamar bake ba kodon bakya make-up shiyasa yau da kika yi ya yi mugun yi miki kyau".
Hmm besty kenan niko kunyar fita nike yi cikin mutane da wannan kwalliyar sabo da idan naga ana kallona duk se in tsargu bakiga yadda kika yi kyau ba Wallahi besty".
"au nice banyi kyau ba kenan ko Aunty?".
Sorry my Khady nina isa in ce da wannan shagaɓaɓɓiyar ƙanwar tawa bata yi kyauba? Kinfi kowa yin kyau".
Yauwa Auntyna muje".
nan suka fita Inteesar ji take kamar tsirara take sakamakon rashin saka gyale da batayi ba kanta a ƙasa sabo da wata irin kunya da take ji haka sukabi layin da akai na shigar da amarya suka shiga tanƙanemen hall ɗin da ya gaji da haɗuwa suka fara tafiya kiɗa na tashi har suka raka amarya da ango mazauninta dafa Inteesar Hauwa'uh tayi cikin ƙasa da murya ta ce"kinsanko waye angon Asma'uh".
"a'ah waye".
"Sir Adam ne".
dammm ƙirjinta ya bayar lokaci ɗaya zuciyarta tashiga bugawa da sauri-sauri ga yawun bakinta daya ƙafe ƙaf murya na rawa ta ce"what?".
"Eyi".
Wani gumi ya shiga ketomata suka samu seat suka zau na ta ce"amma baku kyauta mun ba da kuka hanani saka gyale ko wanne tom and jerry ya gama kallemun jiki a banza".
Nan Hauwa'uh taita kwantarmata da hankali aka shiga gabatar da program.

Suna cikin hirarsu da Khadija taji muryar m.c na ce wa"muna buƙatar aminiyar amarya me suna Aishatu domin tazo ta gabatar mana da tarihin amaryar".
a gigice ta É—ago ta ce"Hauwa'uh kinga irin abin da nike gudu ko da kun barni nasa gyalena ai da duk haka bata faru ba".
"Sorry besty gani muka yi idan kika sa zaki lalata kwalliyarki kiyi haƙuri kije kiyi kin san Asma'uh bazata ji daɗi ba".
"Ba bu 'in da zani ".
Ji suka yi m.c ya ƙara kiran sunan Inteesar hakan yasa Khadija ce wa"Aunty dan Allah kiyi in baki yi ba kamar kin watsawa Aunty Asma'uh ƙasane a ido ta wuce kowa ta zaɓeki plz Aunty".
taƙarasa zancenta tare da saka hannunta alamar roƙo kamar zata yi kuka hakan yasa Inteesar ce wa"sorry my Khady karkiyi kuka bara naje".
"yauwa Auntyna maganin kukana".
nan Inteesar tafara tafiya cikin nutsuwa take tafiya kanta a ƙasa hankalin kowa kanta ya koma sakamakon m.c daketa koɗata tun daga nesa ya kafeta da shanyayyun idanunsa da sukayi kama dana me bacci gani yike kamar ita kamar ba itaba hakan yasashi tanfatsar da glass cup ɗin dake hannunsa hakan yaja hankalin mutanen dake kusa da gurin yi ke suka kalle shi ba tare daya sani ba a zuciyarsa ya ce"why zuciyata da zaki dameni da tunanin wannan kucakar yarinyar ne da kowacce nagani ganinta nike kamar ita why anyako wannan yarinyar ba mayya bace takamani".
yana wannan tunanin harta ƙarasa gurin m.c ta tsaya saurin dawowa ya yi daga tunanin daya tafi gani ya yi ba Imergination ɗinta daya saba yi bane ita ce tasha gayu tagaji da haɗuwa se ƙamshi take bazawa!!!!!!!!!

meson shiga group É—in wannan novel É—in tayimun magana ta wannan number 08108362334

Votes and Comments
Plz share

_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_r Mutanen Gwarzo.*_🌻 *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)

*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*

HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…

*BOOK 1*

*PAGES* 1️⃣9️⃣➡️2️⃣0️⃣

Cikin amsa kuwwa m.c yace "masha Allah ga babbar aminiyar amarya amma gaskiya tahaɗu kwarai dagaske bara muji taƙaitaccen tarihin babbar aminiyartata".
yaƙarasa zancensa tare da miƙawa Inteesar laudspeaker amsa tayi tare da ɗago da kyakyawar fuskarta wadda tayi mugun kyau domin inba farin sani kayimataba ba lallai bane ka ganetaba saboda kwalliyar tayi mugun amsar jikinta kamar ka saceta ka gudu jin abinda m.c yafaɗane yasashi ƙara tabbatarwa da kansa tabbas ba gizo tayimasa ba itance dai zuciyarsa ce tacemasa"to a ina tasamu kuɗinda harta iya saka wannan tsadadden material ɗin domin nidai a iya sanina bamasu hali bane".
wata zuciyarce tace"wataƙila saurayinnan natane ya siyamata".
tsaki yayi saboda lokaci ɗaya yaji wani mugun ɓacin rai yadirarmasa lokaci ɗaya yaji duniyar tayimasa zafi Mimah dake zaune kusa dashi ce tace"wow Hubbi ammafa ƙawar amaryarnan kyakyawace ajin farko".
taɓe baki Namijin duniya yayi kamar wanda yaga kashi ya waigar da kansa gefe yadda bama zaka ɗauka yaga Inteesar ba.

Cikin zazzaƙar muryarta me tafiya da zuciyar duk wani ɗa namiji me lafiya tashiga zazzaga speach kamar wata baturiya yadda take ba kowacce kalma haƙƙintane yasa taƙara burge mutanen gurin uwa uba kuma a natse take komai nata bayan ta gama da yaren turanci ta juya larabci yadda take fitar da harufa bazaka taɓa ɗauka ba balarabiya bace tana gamawa gabaki ɗaya gurin ya kaure da tafi saboda baƙaramun tafiya da hankalin mutane tayiba ta juya zata tafi m.c yace"ranki shidaɗe kitsaya babban abokin ango yazo yabada biography ɗin ango sannan ku zauna a seat ɗin da aka tanaza dominku munason ganin babban abokin ango ɗaya tamkar da dubu uban gayya Sir Abdallah Namijin duniya ".
damm ƙirjin Inteesar yabayar jin sunan wanda aka kira lokaci ɗaya hankalinta yayi mugun tashi amma dayike miskilace bazaka taɓa fuskanta ba tafi gurin ya ɗauka alamun Namijin duniya ya miƙe a hankali ta ɗago lulu eyes ɗinta da suka cika da tsoronsa ta saukesu akansa ɓangaren Namijin duniya ko yanajin abinda m.c yafaɗa yaƙara shan kunu ya ɗauki glass cup ɗin dake kusa dashi kenan yaji wasu abokan kasuwancinsu ɗaya na cewa ɗaya"wow amma gaskiya wannan babe ɗin ƙarshe ce anyako bazan raɓa ba kuwa".
"gaskiya dai Muhseen kayi maza ka raɓa domin tahaɗu yarinyar tunkafin wani ya rigaka domin irin wa'innan sune irin matan da ake layi gurin neman aurensu se me tsananin rabo kesamun aurensu kagafa ga kyau ilimin addini da boko ga nutsuwa uwa uba hankali kai Muhseen inka sameta kagama morewa wlh ga dirin jiki".
"ai da wuri zanyi sauri inje ana tashi zanje insanarmata da kudirin zuciyata ko Allah zesa insamu shiga da aduniya zanga nafi kowa sa'ah".
lokaci ɗaya yaji wani ɓacin rai ya lulluɓesa idanunsa sun canza kala saboda tsananin ɓacin ransu yayi saurin ɗaukar glass cup ɗin ya shanye ruwan tas kozeji sauƙin zugin da zuciyarsa kemasa amma wani canji ga wani abu daya tsayamasa a zuciya na ganin irin shigar dake jikinta .
Chapter 13 · 0% Book details