← Book details Man Of The World Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 23

Sashe 22

Man Of The World Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwance yake akan tamfatsetsen italian bed ɗinsa idanunsa a lumshe kamar me bacci tsaki yayi haɗe da buɗe sexy eyes ɗinsa yace"anya ko wannan yarinyar ba mayya bace ba kuwa meyasa dana rife ido ba abinda nike gani se ita gaskiya inko ba mayya bace ƙila ta haɗa iri dasu take ƙoƙarin cinyeni koma dai menene Allah yafiki stupid kawai".
ƙara sakin wani tsakin yayi yaƙara lumshe idanunsa nanma still ba abinda yike gani se ita tsaki yaƙara yi yaji an turo ƙofa anshigo wasu english wears ne jikinta wando da riga wandon iyakarsa guiwarta jeans baƙi se rigar sky blue me ratsin net daka gurin ƙirjin baƙaramin kama jikinta kayan sukayi ba tasha uban kitson atarch har ɗuwawu tana tafiya ko ina na jikinta na motsawa hannunta ɗauke da cup ɗin coffe jikin drawer ta nufa da niyyar aje coffeen dake hannunta caraf idanunta ya sauka kan faffaɗan ƙirjin Abdallah dake cike da gashi irin na jaruman maza masu ji da class se ɗaukar ido gashin keyi shedar yana shan gyara tana ajewa ta juya idanunta ya rife ta kai hannu da niyyar taɓawa taji ya dakamata tsawa haɗe da cewa"ke wacece irin tinkiya ce mara tarbiyya waya baki izinin shigomin part da har kika wuce falo kika shigomin bedroom with out my permission dakin bari wannan ƙazamun hannun naki ya taɓamun jiki da sekin raina kanki domin wallahi da sena nunamiki true colour ɗina ".
sosai yayimata kwarjini lokaci É—aya ta diririce murya na rawa tace"dama Yah Abdallah coffee na haÉ—omaka".
batare daya buɗe sexy eyes ɗinsa ba yace"nacemiki ina buƙata ne da zaki shigowa mutane bedroom bako sallama saboda rashin hankali ko da ke kike bani coffee ɗin ko ancemiki ni inashan coffee ɗin kowanne tom and jerry ne irinki kinfice da tsiyarki kinbani guri ko sena tashi stupid kawai mara aji".
saurin ɗaukar coffen ta tayi jiki na rawa ta fice tana fita yayi tsaki ya miƙe tare ɗaura towel ya nufi toilet.

4:00pm
Hauwah na shirin shiga gidansu Inteesar wasu haɗaɗun motoci guda huɗu suka yi parking biyu hilux biyu Parado baƙaƙe se ɗaukar ido suke parking suka yi daidai ƙofar gidansu Inteesar wasu haɗaɗun matane dattijai wanda bazasu gaza shekaru 50 ba suka fito daka mota ɗaya su biyu amma inkagansu seka ɗauka ƴan shekaru talatin da biyar ne saboda yadda jikinsu ya nuna kana ganinsu kasan sun jiƙu da naira ɗaya motar kuma wasu matane su huɗu matasa masu jini a jika suka fito masu tsananin kama da Zaid musamman ma ƙaramar cikinsu sauran hilux ɗin biyu kuma shaƙe suke da akwatuna wani daɗine yakama Hauwah ta nufi inda suke cikin girmamawa tace"Ina yininku".
"lafiya ƙlau badai kishiyar tawa bace daiko data kwacen miji na bace ko" .
cewar É—aya daga cikin dattijan dariya Hauwah tayi tace"Babah ba ita bace Æ´ar uwarta ce ita tana can gidan".
tafaɗa ta me nuni da gidansu sosai taji daɗin jin wannan kalaman daka bakin wannan matar hakan ne yaƙara tabbatarmata da dangin Zaid suna son aminiyartata nan tayimusu jagora zuwa cikin gidan ɗaya daga cikin matasan matannan ce tace"amma dai sister zaki kaimu inda amaryar tamu take ko".
"insha Allah zankaiku".
"yauwa Jabeer ku shishigo da kayan ".
"toh ranki shidaÉ—e".
cewar Jabeer nan suka shige gidansu Inteesar .

Bayan sun gama gaisawa ne su Jabeer suka fara shigo da haɗaɗun akwatuna seda suka shigo da akwati sha biyu nan aka shiga buɗa akwatunan dake shaƙe da kaya tsadaddun kayane ƴan ubansu a ciki kowanne da takalminsa da mayafinsa da jakarsa sosai murna gurinsu Khadijah da Hauwah ba'ah cewa komai tun suna ƙirga kaya har suka dena domin Zaid yayi ƙoƙari sosai nan Momynsu Hauwah tasa su Hauwah su fito da snacks ɗin da sukayi aka aje a gabansu da kuɗin tukuicin da Abban Hauwah ya bayar dubu goma aka basu har an aje akasa aka kaisu mota Hauwah tayiwa wannan budurwar rakiya zuwa gidansu suga Inteesar .

Kwance take tana karatu littafi taji shigowarsu Hauwah ba tare data tashi daka inda take ba ta amsa sallamar su Hauwah shiga sukayi suna shiga ƙanwar Zaid a zuciyarta tace"wow gaskiya dole bro ya gigice amma gaskiya ta haɗu ko ni mace nasan ta haɗu balleshi da yike namiji kalli gashinta dan Allah har gadon baya".
tana cikin zancen zucin taji Hauwah tace"Besty ga ƙanwarki tace tana son taga wadda ta susutamata Yayanta".
rife fuska Amna tayi tana dariya tace"Aunty ina yini".
murmushi Inteesar tayi tace"lafiya ƙlau Amna ko".
ɗagamata kai tayi bayan sun gaisa suka kawomata ruwa tasha suka ta miƙe nan suka mata rakiya a bakin get ɗin gidansu Hauwah Inteesar ta tsaya tare da ɗagamata hannu alamun bye-bye sannan ta juya.

Ɓangaren Uwar gwarama ko tunda taga irin dukiyar da Zaid ya kashe a lefen Inteesar hankalinta yaƙara tashi takasa zaune takasa tsaye ko gurin lefan bataje ba saboda tsananin baƙin cikin dake damunta ga Jameelah ta tasata a gaba se kuka takemata kan ita har yau bataga alamun Zaid baze auri Inteesar ba hankalinta inyayi dubu ya ɓaci ta rasa inda zata saka kanta taji daɗi.

Washe gari suna tashi suka tafi gurin aiki da wurwuri suna isa Comphanyn kowacce ta nufi gurin aikinta a hankali take tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki yayinda zuciyarta ke dukan uku-uku sakamakon tayi fashi bata sanarmasa ba a hankali ta tura ƙofar office ɗinsa yayinda zuciyarta tashiga bugawa da sauri -sauri kanta a ƙasa tashiga!!!!!!

_*Ga meson karanta book two ɗin MAN OF THE WORLD nafara post ɗinsa a paid group ɗina domin book two na kuɗine akan farashi mafi sauƙi naira #300 domin neman ƙarin bayani ki tuntuɓi wannan number koda kuɗinka seda rabonka 08108362334.*_

Votes and Comments
Plz share to others

_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_anen Gwa🌻 *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)

*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*

HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…

*BOOK 1*

*PAGES* 3️⃣3️⃣➡️3️⃣4️⃣

Samun office ɗinsa tayi bakowa a ciki se ƙarar a.c dake ta faman aiki da mayataccen ƙanshin turarensa daya kama office ɗin waige-waige tashiga yi gani tayi bataga alamar yazo ba sosai tayi mamakin rashin zuwansa da wuri domin tasan yana rigata zuwa duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta tayi taga har goma tayi zuciyarta ce tacemata"ke meye naki na damuwa dan wannan mara mutuncin bezo ba aikyama fi sakewa da binki da yikeyi da wa'innan mayun idanun nasa masu firgita mutum".
tana gama faɗin haka a zuciyarta ta taɓe ɗan ƙaramin pinky lips ɗinta ta wuce toilet tashiga aikinta tana gama wankin toilet tashiga goge chairs and tables ɗin dake cikin office tana gamawa ta share ko ina fes ta gyara ko ina yazama neat ta nufi gurin zaman sakatariya ta zauna ta shiga duduba takardun dake kan tables ɗin kamar an tsikareta ta miƙe tare da kallon tamfatsetsen agogon dake manne a office ɗin ta nufi cikin office ɗinsa tana shiga ta nufi drower dataga room freshners ta ɗauki ɗaya daga cikinsu tashiga fesawa ko ina na gurin ta wani toshe hanci tana cikin mitarta Hauwah ta shigo bakinta ɗauke da sallama amsamata tayi ta cigaba da fesa room freshner ɗinta ƙarasawa inda take Hauwah tayi tare da cewa"Besty wai yanaga kinata faman toshe hanci sekace wadda taji wari bakiji yadda kika cika room freshnern nanba har hawa ka yikeyi ".
"ai warinne domin turaren wannan mutumin har hawa kai yikeyi sabo da rashin daɗin ƙamshinsa har tasarmun da zuciya yikeyi wallahi inji kamar zanyi amai ".
"hhh Besty banda dai sharri dandai kuna faɗa dashine shiyasa kika tsaneshi amma ai Sir Abdallah komai nasa na daban ne ni tunda nike bantaɓa jin irin ƙamshin turarensa jikin wani kinsanfa shiɗin duniya ne ".
taɓe baki Inteesar tayi haɗe da cewa "Besty Allah bazancen sharri bakuma tsanarsa nayi ba kawai halinsa na tsana na girman kai da ɗagawa da nuna shi wanine uwa uba rashin tarbiyya da rashin ganin girman nagaba dashi ko kunya bayaji mutanen da suka girmesa suyita duƙawa suna gaishesa sekiga seya ɗauki lokaci saboda isa da izza sannan ze amsa wa'innan halayen nan nasa na mugun ɓatamun rai wallahi shi ko kunya bayaji isa kamar wani basarake".
"hhh ni banga wata izzaba kedai kawai dan bakwa shiri dashine shiyasa kike ganin kamar bashi da kirki amma Sir Abdallah yanada kirki sosai ga sanin yakamata".
zaro sexy eyes ɗinta tayi haɗe da cewa"wannan mutumin ne yasan yakamata tabɗi a rashin samun wa'inda suka san yakamata ƙila a ɗaukeshi domin wannan mara tarbiyyar mutumin ko hanyar inda yakamata tayi bebi ba".
"to maida wuƙar bani nakar zomon ba rataya aka bani Besty ba wannan yakawoni ba gani nayi har 12pm tayi so nike yau mutafi da wuri saboda mufara tsare-tsarenmu ina tinanij daka yau ba lallai bane muƙara zuwa office ba inaso a gyarawa Uncle Zaid ke sosai dan karya rainamun ke ".
"dama nima yanzu nagama tinanin hakan yau tunda na tashi gabana keta faÉ—uwa na rasa dalili kome yake faruwa oho jinike kamar wani abu ze faru dani".
" insha Allahu Besty ba abinda ze faru dake se Alkhairi kinji Bestyna kedai kawai idan kinji haka ki riƙa Innalillahi wa'innah ilaihi raji'un ki yawaita addu'ah wajan biyu zamu tafi kisan dabarar da zakiyiwa Sir Abdallah".
sauke numfashi Inteesar tayi cikin sanyin murya tace"nagode Bestyna Allah yabarmu tare keÉ—in mahaÉ—in rayuwata ce Besty kinmun komai na rayuwa kullum baki da burin daya wuce kisani farinciki Besty nagode da kulawarki gareni Allah nima kabani ikon temakon wannan baiwa taka ".
taƙarasa zancenta hawaye na niyyar zubowa daga lulu eyes ɗinta girzgizamata kai Hauwah tayi alamun kar tayi kuka tace"Besty banason godiyar nan da kikemun domin nasan inke kike da damar da nike da ita da ba abinda bazakimunba toni meyasa bazan mikiba bayan inada halin yi domin keɗin kin wuce ƙawa a gareni ƴar uwata ce dan Allah duk abinda zanmiki kidenamun godiya".
saurin rungumeta Inteesar tayi haÉ—e da fashewa da kuka seda sukayi kuka me isarsu sannan suka saki junansu Hauwah tace"Besty bara na koma gurin aiki".
kai kawai Inteesar ta iya É—agamata saboda kukan datasha nan Hauwah ta tafi tabarta jiki bakwari ta koma mazauninta na sakatariya a zuciyarta tana mamakin rashin zuwan Namijin duniya.
Chapter 22 · 0% Book details