← Book details Man Of The World Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 23

Sashe 19

Man Of The World Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɓangaren Namijin duniya ko Doctor na gama gyarawa Inteesar ƙafa cikin yanayin caring Doctor Shahid yace"princess gaskiya kinada dauriya da watace da yanzu tana nan ta cika ɗakinnan da ɓararrako".
wani sansanyan murmushi Inteesar tayimasa wanda yayi mugun tafiya da zuciyar Doctor Shahid tace"nagode".
"ba godiya a tsakanin princess kedai kawai ki kula da shan maganinki insha Allahu nanda kwana uku zakiji ƙafar ta saki".
yaƙarasa zancensa yana sakarmata wani shu'umin murmushi ,murmushin itama ta mayarmasa itama cikin siriyar muryarta dake tafiya da zuciyar ɗa namiji tace"insha Allah zankiyaye".
wani ƙullutun baƙin cikinsu ne ya tokarewa Namijin duniya maƙogoro ganin yadda Inteesar keyiwa Doctor Shahid murmushi tsaki yayi a karo na uku sakamakon jin Doctor Shahid na niyyar ƙara jan Inteesar da hira murya aɗan daƙile cikin basarwa ya katse Doctor Shahid tare da cewa" Mallam kayi abinda ke gabanka".
"sorry Sir".
nan Doctor Shahid ya tsuke bakinsa saboda yana ɗagowa yaga Namijin duniya na jifansa da kallon kashiga taitayinka beƙara cewa da Inteesar komai ba ,ɓangaren Inteesar ko wani ƙullutun baƙin cikinsa taji tashiga itako metayiwa wannan mutumin da bayason yaga wani ya raɓeta bayason yaga wani yana nunamata kulawa tana farinciki tana cikin tinani taji muryarsa a ɗan daƙile yana cewa da Doctor"thanks".
saurin dawowa tayi daga duniyar tinanin data tafi taji ƙamshinsa a gabda ita waigawa tayi taganshi befi saura taku biyu ya iso inda take ba saurin miƙewa tayi dukda zafin da ƙafarta kemata ta haɗe girar sama data ƙasa dan karya kaimata wargi tashiga aikamasa da harar wutsiyar ido tafara tafiya tana ɗingishi murmushin gefan baki yayi ganin yadda ta wani haɗe rai yabi bayanta yarigata zuwa gurin mota hakan yasashi yana isa ya buɗemata murfin motar har tayi niyyar wucewawarta taga idanun mutanen gurin gabaki ɗaya yadawo kansu hakan gefe guda kuma wata zuciyar tace mata"kishiga har yanzu kina ƙarƙashin ikonsa tunda baku tashi daka gurin aikiba".
hakan yasata jiki a sanyaye ta shiga ya mayar ya rife ya zaga yashiga mazaunin driver yaja motar suka bar gurin yana fita daka get ɗin gurin ya cilla hancin motarsa titi ya ware a.c ɗin dake motar ya kunna karatun Alqur'ani megirma ƙira'ar Sudais tashiga tashi a cikin motar suratul Muhammad ba tare daya ƙara bi takanta ba yashiga bin ƙira'ar da daddaɗar muryarsa me daɗin sauraro .

Ɓangaren Inteesar ko juyar da kanta tayi tana kallon titi hakan datayine yabashi damar ƙarewa fuskarta kallo ɗan motsawa tayi hakan yasashi saurin ɗauke kansa daga gareta cikin nutsuwa yake tuƙi ganin hankalinsa ya karkata akan tuƙin taga ya nufi hanyar cikin gari da ita saurin kallonsa tayi gani tayi ya wani make kamar besan metake nufiba sosai ranta yakai ƙololuwar ɓaci da abubuwan da yikemata ta aro jarumta cikin tsiwa tace"Malam ajeni anan".
yi yayi kamar badashi take ba hakan daya yimata baƙaramin ƙara tunzurata yayiba a harzuƙe tace"Malam ka ajeni anan".
ƙara banza da ita yayi hakan yasa takai hannu cikin ɓacin rai zata murɗa handle ɗin motar kafin taƙarasa taji ƙarar sa lock ɗinsa hakan yasa ta koma ta zauna tare da jingina da jikin kujerar ta lumshe oily eyes ɗinta cikin kwanciyar hankali ya cigaba da tafiyarsa harya isa wani tanƙamemen mall mesuna MAN OF THE WORLD SHOPPING MALL da manyan baƙi ƙarasa shiga gurin yayi tare da yin parking a tanƙamemen parking space ɗin gurin yana daidaita parking ɗinsa yaɗan saci kallonta gani yayi har bacci ya ɗauketa a haka jiyayi wani murmushin dabe shirya yinsa ba ya kuɓucemasa ganin yadda ta duƙunƙune ne yasashi gane a.c tayimata yawa yaɗan ragemata haɗe da kwantar mata da kujerar ya gyaramata kwanciyarta ya buɗe ya fita tare dasa lock ta waje ya nufi cikin gurin bejima da shiga ba yafito bayansa da masu aiki a gurin sanye da riguna da kaya niƙi-niƙi a bayansa danna key ɗin motar yayi har zasu zuba a boot ya dakatar dasu yayimusu nuni da gidan baya cikin girmamawa suka zuba yashiga motar yaja seda sukayi tafiya me nisa rasa hanyar dazebi yakaita gidane yasashi juyawa ya kalli inda take gani yayi ta tashi taɓe baki yayi haɗe da cewa"ina zankaiki".
ba tare data kalli inda yike ba tace"Suleja amma a titi zan sauka".
ba tare daya tankamata ba ya juyar da kansa ya cigaba da tuƙinsa cikin kwanciyar hankali yaƙara volume yashiga bin karatun Alqur'ani taɓe baki tayi a zuciyarta tace"ashe su wa'eeh an iya abun mutane".
jin muryarsa tayi kamar a mafarki yace"keeeh dawa kike".
se lokacin tagane a fili tayi maganar tsuke bakinta tayi har suka isa bakin titi kamar yadda tace dashi yayi parking gefan titi ba tare daya kalleta ba yasa hannu ya jawo ɗaya daka cikin ledojin da yasa aka saka a baya ya buɗa ya fito da wasu rantsatsun abayas masu ɗaukar hankali ya zaro ɗaya daga ciki ya buɗa ba tare daya kalleta ba yace"daka yau wa'innan kayan zaki riƙa sawa da safarsu da niƙab ɗinsu dan bazan lamunci saka wannan banzan gyalen da kikeyi ba domin Comphany ɗina ba gurin nanaye bane da mutum zaki riƙa saka wa'innan fugaggun gyaluluwan naki masu kama da matacin koko a ciki akwai hijabs kowanne kowanne kaya da kalar niƙab ɗinsa da hijab ɗinsa su zaki riƙa sawa".
wata dariyar rainin hankali tayimasa tare da taɓe baki ta aro jarumta tace"waikai meyasa kake son takurawa rayuwata ne sekace wani mijina ina ruwanka da kayana kuma da kake cewa gyalena kamar matacin koko meye naka a ciki naga tundaka gidanmu nasawo kayana meyasa su basu yimun maganaba sekai kuma kai bakaga irin shigar da Sakatariyarka take ba se tawa saboda ni kaɗai ka tsana to bazan dena sawa ba banason kayan kakaiwa matarka tasa domin ni a ganina ita zakaiwa wannan kullen baniba".
taƙarasa zancensa tare da ture rigar daka jikinta cikin isa yace"ke wacece da zanyimiki kyauta ki mayarmu dame kike taƙama baki isa kin karyamun record ba dole ki ansa".
wani kallon tara saura kwata tayimasa cikin tsiwa tace"mutum ce kamarka kai waye da baza'ah mayarmaka ba masha Allah kaga seka aje record akaina anyi rejecting É—in kyautarka domin ni wallahu bazan ansa ba ka adana zasu yimaka amfani gun matarka".
taƙarasa zancen tare da saurin murɗa handle ɗin ƙofar cikin sa'ah tajishi a buɗe tayi saurin fita ganin ya kawo hannunsa da niyyar cafkota tafice cikin sauri dukda tanajin zafin ciwon da ƙafarta ke mata karo na farko a rayuwarshi daya yi murmushi dukda rashin kunyar data tayimasa beja motar ba har seda yaga ta tsallaka titi tahau napep sannan ya tada motarsa yabar gurin a guje.

8:30pm
Tsaye yake a ƙofar gidansu yanata dialing number ta amma amsar ɗaya switch off sosai hankalinsa yayi mugun tashi ɗaga kannan da zeyi yaga Hauwah ta fito daka gidansu tunkaro inda yike tsaye sosai yaji wani irin sanyi ya ziyarci zuciyarsa bakinta ɗauke da sallama taƙarasa murmushin daya ƙara masa kyau yayimata cikin girmamawa Hauwah tace"Uncle Zaid anyini lafiya".
"inafa lafiya banji zuciyata ba ina zakijini naga ta lafiya".
sosai Hauwah daɗin kalamansa akan ƙawarta nanta labartamasa duk abinda yafaru a iya yadda tasani sosai hankalinsa ya tashi sosai takejin daɗin yadda yake caring ɗin ƙawarta tace "Uncle ka kwantar da hankalinka bara inshiga insanar musu seka shiga ka ga jikinta".
"aiko da kin temakeni domin bakiji yadda hankalina yayi mugun tashiba dukda kin faɗamun amma hankalina yaƙi kwanciya in naganta hankalina yafi kwanciya".
"tom bara naje".
nanta shiga .

A tsakar gida tasamu Abbah da Uwar Gwarama zaune Abbah yana cin tuwo Uwar Gwarama tana ƙuƙula magungunan mata da take siyarwa abinka dame sana'ah goma maganin me gasa ƙarasawa tayi inda suke cikin girmamawa tace"Abbah sannunku da hutawa".
"yauwa Hauwah ya mutanen gidan naku".
"lafiya ƙlau Abbah dama Zaid ne yazo zamuje gidansu shine nike faɗamasa Inteesar ɗin batada lafiya ……".
bata ƙarasa abinda take son cewa ba cikin zalama Abbah ya tari numfashinta da cewa "meyasa to baki ce yashigo ciki yagaida itaba aida kince ya shigo aishima yanzu yazama ɗan gida ko Tsahare".
tsilum Uwar gwarama tace"aiko dai Malam".
jin abinda Uwar Gwarama tace sosai yabawa Hauwah mamaki tace"ai Abbah nacemasa bara inyimasa iso yashigo".
"toh! toh!! toh!!! kin kyauta ki sanar dasu suÉ—an gyatta seki shigo dashi".
"toh".
nanta nufi É—akinsu Inteesar zaune tasamesu Khadijat na karantawa Inteesar wani littafin Real eeshow mesuna ZANJIRATA sosai suke jin daÉ—in littafin domin yana kaimusu Umman su kuma tana kan sallaya tana lazumi hararsu Hauwah tayi tace"yanzu nan saboda rashin mutunci shine kuka cigaba da karantawa koku kirani inason jin yadda zata kaya tsakanin Amatujjabar da Yayah Mahmud saboda dramar su nakaimun ".
"ya haƙuri Aunty Hauwah zan karantamiki kema seda nace tabari kizo taƙi kinsan Aunty da gauƙa yanzu ma kuma muka fara".
"toh ƴar ƙanwata takaina ".
taƙarasa zamcenta ta nufar gurin Ummah duƙawa tayi ta sanar da ita zuwan Zaid sannan tasa suka ɗan kintsa dukda ɗakinsu fes-fes yike basu da lalaci nanta fita tashigo dashi.

Uwar Gwarama na ganin fitar Hauwah ta kalli Abbah daketa sukurkuta lomar tuwo yana santi tace"Malam bara inɗanje inɗan kunna turaren wuta sirikinmu bayazo yanaɗan jin bashi -bashi ba kadai sanni da iya karramar baƙo bare kuma babban sirikinmu".
"aiko dai da kin kyauta".
wani shu'umin murmushi tayi ta wuce É—akinta tana shiga ta iske Jameelah tana waya da saurayinta cikin azama tace"ke banza kina nan kina shashsnci Allah yakawo mana dama Zaidu yanzu ze shigo ya duba waccan tsinau É—in ki tashi ki É—ebo rushi kizuba magain nan".
tsalle Jamilah ta buga tare da miƙewa cikin jin daɗi tace"I love you Mamah na maganin kukana".
ta fice cikin sauri murmushi Uwar Gwarama tayi ta tafi ta É—akko maganin da boka yabata ta fito waje a tsakar gida suka haÉ—u da Jameelah ta ebo wuta a marfin langa nanta jiki na rawa ansa Uwar Gwarama tayi tana murmushi tace"yimaza kije kiÉ—an kintsa jikinki karya ganki kamar wata Æ´ar jaka".
"toh".
nanta wuce ita kuma ta buÉ—e maganin ta zuba .

Zaid na shigowa ƙamshin turarennan ya bugu hancinsa lokaci ɗaya yaji kansa yashiga saramasa dakyar yake iya ɗaga ƙafa yake tafiya har suka isa!!!!!!!!

Votes and Comments
Plz share to others

_*Daga Alƙalamun 🌻 *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)

*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*

HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…

*BOOK 1*

*PAGES* 2️⃣9️⃣➡️3️⃣0️⃣
Chapter 19 · 0% Book details