← Book details Man Of The World Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 23

Sashe 20

Man Of The World Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Inda Abbah ke zaune yaƙarasa tare da zama kan sallayar da aka shimfiɗamasa ya zauna cikin girmamawa yace"Abbah ina yini".
"lafiya ƙlau ya wajen iyayen naka".
"lafiya ƙlau Abbah suncema suna gaisheku".
"masha Allah Hauwah yimasa jagora zuwa gurin mejikin".
"toh Abbah".
taƙarasa faɗa tana kallon Zaid da bashi da niyyar miƙewa ɓangaren Zaid ko ji yayi duk bayako son ganinta daurewa yayi ya miƙe da nufin bin bayasan sukaji muryar Uwar Gwarama dake fitowa daka ɗaki cikin shiga ta alfarma jiki na rawa Zaid yayi saurin duƙawa yace"Ummah ina yini".
ganin yadda jikinsa yaketa faman tsuma baƙaramun daɗi taji ba a zuciyarta tace"kai gaskiya Boka Tsula aikinka na kyau jibi yadda jikin wannan shu'umin yaron daya wulaƙantani yaketa faman karkarwa kamar mazari kaɗanma kagani ɗan shegiya zaka kwashi kashinka a hannu domin seka gane shayi ruwa ne seka zama tamkar raƙumi da akala domin Jameelah se yanda tayi dakai badai kai ƙaramin tsageraba hadda wani cewa dani ni Inteesar nike itakuma har wani gwalli takeyi wai ita zatayi aure gidan jindaɗi maga yadda za'ayi ayi auren matsawar ina numfashi bazan taɓa barin ɗiyar Aminah taji daɗin duniya ba kamar yadda na hanasu jin daɗin gidannan haka bazan taɓa barinku kuji daɗin gidan mijiba sede ku ƙare a bauta matsawar ina numfashi ".
katsemata zancen zucin da takeyi Zaid yayi murya na rawa yakuma cewa"Ummah ina yini".
wani gauron numfashi ta sauke haɗe da dawowa daga duniyar tinanin data lula tace"lafiya ƙlau yaron kirki ya wajen magabatan naka".
baki har ɓari yikeyi yace"lafiya ƙlau Ummah sunama gaisheku",.
a wani yatsune Uwar Gwarama tace"muna amsawa ɗiyar kirki ƴan makaranta kifito ga yayanku yazo ku gaisa ko duk hadda ce har yanzu kiriƙa barin kwakwalwarki ta huta dan Allah darenma ace mutum baze hutaba sekace al'huda-al'huda aikya fito ku gaisa inyaso seki koma kicigaba da karatun".
Jameelah dake ɗaki tana chart ɗinta da saurayinta ce tayi gyaran murya alamun bata kai ayaba ta cigaba da danna wayarta bayan 5mins cikin fi'ili tayi kabbara sannan ta miƙe taƙara feshe ko ina na jikinta da turare sannan ta gyara zaman hijab ɗinta tashiga tafiya cikin yanayin ɗaukat hankali.

Ganin yadda jikin Zaid keta faman ɓari baƙaramun mamaki hakan yaba Hauwah ganin yadda bakinsa har rawa yike gurin gaida Uwar Gwarama tinani tashiga yi a zuciyarta tashiga tinanin ita a iya saninta Zaid baya shiri da Uwar Gwarama to kuma meyasa taga jikinsa har ɓari yikeyi kanta rasa wanda zebaa amsa ne yasata tsuke bakinta tana mamakin iyayi irin na Uwar Gwaramaa zuciyarta tace"hmmm iska na wahal dame kayam kara ko a ina Jameelah ta taɓa shiga class oho Allah dai yasa ba wata kitumurmurar suka haɗa ba".
tana cikin wannan zancen zucin taji ƙamshin turaren Jameelah ya bigi hancinta saurin ɗagowa tayi caraf sukayi ido huɗu da Jameelah daketa faman zuba ƙamshi tasha kwalliya kamar wadda zata gasar kyau baƙaramun ɗaurewa kanta yaƙara yiba da mamakin abinda take gani ganin abun take kamar almara wata uwar harara Jameelah ta bankamata suna haɗa ido da Zaid tasakarmasa da wani narkakken murmushi wanda yasashi suman wucin gadi lokaci ɗaya yaji wani mugun sonta na fisgarsa jiyike duk duniya bashida wani abu da yikeso kamarta martanin murmushin data yimasa ya mayarmata wani sanyine ya ratsa zuciyarta inda takejin wata muguwar ƙaunarshi na ƙara ninkuwa a cikin zuciyarta jitake kamar taje ta rungumesa haka takeji .

Uwar Gwarama ce ta kalli Zaid cikin iyayi tace"kaganta nan Zaidu kullum aikin kenan daka hadda se zuwa makaranta koda yike tafi masu rataya jaka kullum kamar wanzamai aje can aje nan duk wani lungu na garinnan inkabi seka gansu kamar wa'inda akaimusu hakika da kare shiyasa ƙilama shiyasa aka rasa mashinshini".
murmushi Zaid yayi yace"masha Allah sister yanzu izunki nawa".
farr Jameelah tayi da mitsi-mitsin idanunta da suka ƙara narkar da Zaid cikin ƙaunarta zatayi magana kenan caraf Uwar Gwarama tace"hmm ai dake tayi sauka Hafizah ce bakaga yadda ƴan unguwa suke zuwa ɗaukar karatu gurinta ba".
"wow masha Allah ashe ƙanwar tawa Malama ce kenan a daɗa bada himma watarana zakiga amfanin abun ".
"insha Allah Yayah".
Hauwah dake gefensu dakyar ta tare dariyar data kusa kuɓucemata tace"muje Uncle Zaid kaga me jikin".
taƙarasa maganarta tana niyyar yin dariya sauke numfashi Zaid yayi danshi har yama manta da abinda ya kawosa lokaci ɗaya yaji wani irin abu yazo ya tsayamasa a zuciyarsa jiyike kamar ya zura da gudu saboda yadda kansa ke mugun saramasa dakyar ya yaƙi zuciyarsa gurin cewa"ok muje".
nan tayi gaba yabi bayanta ɓangaren Hauwah ko baƙaramun mamakin su Uwar Gwarama take ba tana wannan tinanin har suka isa ɗakinsu Inteesar.

Suna shiga yaji kansa ya daɗa juyewa yanajin wata irin muguwar tsanarta na shigarsa a zuciyarsa yanajin inda za'ah bashi wuƙa a lokacin ace ya kashe maƙiyinsa to ba makawa Inteesar ze kashe dakyar ya yaƙi zuciyarsa ya duƙa yagaida Umminsu Inteesar ba yabo ba fallasa ya gaidata Khadijah tagaidashi a ciki-ciki ya amsa cike da mamakin yadda taji ya amsa gaisuwar Khadijat ta ɗago idanunta ta kalleshi gani tayi yana bin ko ina na ɗakin da kallon ƙasƙanci da zallar tsana gami da kyama sosai abun yashiga bata mamaki tana cikin mamakin abinda idonta ke ganemata taji muryar Umminsu tace"Khadijah kawomasa ruwa".
cikin yatsuna yace"a'ah nagode Ummih".
murmushin manya Ummih tayi suka fice suka barsu ragewa gurin yayi daka Inteesar seshi a hankali ta miƙe tana tunkaro inda yike abun mamaki setaga ya miƙe zumbur kamar wanda aka tsireshi da allura ya miƙe yana toshe hanci ya fice waje da sauri dube-dube tashiga yi taga ko ina tsaf yike na ɗakin ba abinda ɗakinsu yike se ƙamshin turare a zuciyarta ta tambayi kanta"to meyasa yake toshe hanci kamar wanda yakejin wari".
rasa me bata amsa ne yasa wata zuciyar cemata "ƙila ƙamshin turaren ne bemasa ba to amma kuma meyasa yake binmu da irin kallon danaga yana binmu dashi ".
rasa me bata amsa ne yasata saurin bin bayansa.

Ɓangaren Zaid ko yana fita ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya lokaci ɗaya yaji wata fresh air na shigarsa ya nufi gurin dasu Abbah ke zaune cikin girmamawa ya duƙa a gaban Abbah yace"Abbah ga wannan a siyawa me jiki magani".
washe haƙora Abbah yayi irin na zalamammun iyaye masu tsananin son abun duniya yace"toh!toh!! toh!!! angode Malam Zaidu kaidai baka gajiya da abun arziƙi angode Allah ya saka da Alkhairi".
"Ameen Abbah ni zan wuce sauri nike".
"toh madallah ka gaida magabatan naka".
"toh zasuji".
yaƙarasa faɗa yana duben ta inda zeganta caraf suka haɗa ido da Jameelah dake ɗauke da tray a hannunta cikin karairaya take tafiya harta isa gabansa ta aje tray ɗin dake hannunta haɗe da waro mitsi-mitsin idanunta tace"badai Yayah har zaka tafi ba".
"eh Sis sauri nikeyi meeting É—in gaggawa ne ya tasomun".
"okay to amma dai ko jus É—in kasha dai".
"anya Sis sauri nike kibari watarana nasha".
kukan shagwaɓa Jameelah tashigayi harta buga ƙafa hakan baƙaramun ƙara burge Zaid yayiba yaƙara lula cikin duniyar ƙaunarta yace"sorry Sis bani insha".
"yauwa Yayana".
nanta zubamasa yasha baƙaramun ɗaurewa kan kowa na gurin yayi Uwar Gwarama tana haɗa ido da Jameelah ta ɗagamata hannu alamun aikinta na kyau nan yayimusu sallama kota kan Inteesar dayaga tana tahowa bebiba ya fice da sauri saurin bin bayansa tayi amma me tana zuwa yana barin gurin a guje ko kulata beyiba zubewa tayi a gurin tare da fashewa da wani marayan kuka jitayi an dafata tabaya hakan yasata saurin goge hawayenta tayi saurin ɓoye damuwarta tayi ta juya haɗe da cewa"Besty tinanin yadda za'ayi gobe nike narasa meza'ah tarbi ƴan kawo kayannan dashi".
"shine kuma zaki duƙa kamar wadda wani abun ke damunta kodai ƙafar ce ta motsa muje nagama tsara abubuwan da zamu siyo semuyi snacks da drinks se chickens ina ganin ya isa".
"eh ya isa ammafa ni a hannuna befi 6k ba ina tinanin har su sai lemo susai chicken ga uwa uba snacks".
"muje inada kuÉ—i a account É—ina semuyi amfani dashi".
"toh ke bakida amfanin da zakiyi dasu da zaki ce ga wasu a gurinki".
"ai Besty ko inada amfanin da zanyi dashi na fasa meye ranar inada shi ban temakekiba ai abun bemun rana ba haba Besty a tinanina in inada abu tamkar kema kinada shine muje dan Allah musan abunyi".
"hakane kam Besty nagode Allah ya saka da Alkhairi yabarmu tare".
harar wasa Hauwah tayimata haÉ—e da cewa"ameen Bestyna Allah ya shiryeki Bestyna inban miki ba wazan yiwa".
"Ameen dai Besty".
nansuka shiga dan tsara abubuwan da zasuyi domin tarbar Æ´an kawo kaya.
Chapter 20 · 0% Book details