← Book details Man Of The World Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 23

Sashe 21

Man Of The World Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune suke a gaban Boka sun gama zayyanemasa duk abinda ke faruwa tsakanin Inteesar da Man of the world wata uwar dariya Boka Kutsugu yayi lokaci ɗaya ya haɗe rai tare da cewa"tunkafin kuzo nan nasan da zuwanku wannan yarinyar da kuke gani ba'ah zaune take haka kawai ba domin yarinyar nan da kuke gani ba ƙaramar hatsabibiya bace dole sekinyi da gaske sannan zaki kamota".
"kinji ko dama na faɗamiki yarinyar nan baƙaramar hatsabibiya bace dama ni ina ganinta nasan ba haka nan take zaune ba ".
"Boka yanzu ayi duk yadda za'ayi a cire yarinyar nan ta fita daka zuciyarsa asamasa soyayyata a zuciyarsa".
wata uwar dariya Boka kutsugu yaƙara kecewa a karo na biyu yaƙara haɗe rai ya ɗaga hannu sega wani abu ya bayyana duk jini a jikinsa me kama da zuciya yana hurawa ya miƙawa Feenerh irin ɗari-ɗarinnan ta riƙa yi da kyankyami ta ansa a yaƙune wai ita me kyankyami aiko garin yaƙuna abu ta sille tafaɗi batt ba aba ba labarinta dariya Bokan yaƙara yi haɗe da cewa"kinga wannan abar dana baki da kin cinyeta da shikenan kigama da wani Abdallah domin zuciyarsa gabaki ɗaya na ciro na baki kika wulaƙanta".
dafe ƙirji Feenerh tayi cikin kiɗima tace"kayi haƙuri Boka bansan zuciyarsa bace aida tini na cinyeta dukko da jinin da yike jikinta yanzu ka ƙara bani wata zan cinye yanzu yanzunnan".
"hhh ai aikin gama yarinya ya gama bakin alƙalami ya bushe sau ɗaya muke bada zuciyar ga mutum saura magani na biyu idan kinsamo aikinki zeyi kyau".
wani daÉ—ine ya mamaye zuciyar Zuby ganin aminiyarta tayi loosing É—in Man of the world hankali tashe Feenerh tace"yanzu Boka ba yadda za'ayi abani zuciyar yanzu kenan".
"babu zancen zuciya yanzu sede kije ki samo hantar ɓauna kuma ki tabbatar da kanki kika soketa ki yanko da ita za'ai mahaɗin maganin".
a gigice Feenerh tace"hantar ɓauna kuma Boka nashigesu ni Nafi ina zansamu wata hantar ɓauna kuma".
wani daɗine yaƙara kama Zuby a zuciyarta tanata farinciki a fili ko ta nunawa tayi kamar tana alhinin abinda ke damun Feenerh murya na rawa Feenerh tace"Boka to meze hana nabaka kuɗi a samo hantar ɓaunar ko nawa kake so a shirye nike dana kashe ko nawane matsawar nidai buƙatata zata biya ".
"hhh ke zaki samo da kanki inba haka ba maganin bazeyi aiki ba dole da kanki zaki nemo".
"toh zan gwada samowa".
"yauwa ammafa karki kuskure kisa wani ya samomiki akwai matsala gagaruma akan hakan kome yaje ya dawo ki kuka da kanki".
"bama zansa kowa ya samo ba da kaina zansamo".
"yadaifimiki idan kin samo kin kawo dashi zan haÉ—a miki magani ".
"toh".
nansuka miƙe Feenerh ta aje kuɗin dake hannunta suka fita suka tafi ɗan warewa gefe sukayi da Zuby tace"aiko Ummah dole nakomo gobe ni yabani zuciyar na cinye sede taji a salansa domin idan nasamu shiga gurin Namijin duniya nunawa zanyi bansanta ba wallahi zan koyawa yarinyar nan hankali seta gane shayi ruwa ne ai Ummah naji daɗi da bata ci zuciyar ba wallahi".
"kibari mukoma gida karta jimu".
"toh".
nan suka tsuke bakinsu suka cigaba da tafiya.

Washe gari tunda ta tashi da asuba bata komaba kamar yadda tasa ba kullum ta share gidan tass tayi wanke-wanke tana gamawa ta nufi gidansu Hauwah!!!!!!!

Votes and Comments
Plz share to others

_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_ƴar Mut🌻 *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)

*MALLAKIN*
*REAL EESHOW*

HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…

*BOOK 1*

*PAGES* 3️⃣1️⃣➡️3️⃣2️⃣

Tana cikin tafiya taji muryar Jameelah daka bayanta tana cewa"Aunty Inteesar nima zanbiki ayi aikin dani".
juyawa inda take Inteesar tayi zatayi magsna cikin tsiwa taji Khadijah tace"bama gayya a ƙara gaba ke bama kiji kunyar cewa zaki bita ba saboda ke ɓera ce karfa ki manta itace wadda kuka tsana ɗinnan kuka hanata sakat a rayuwa wadda bakwason ganin cigabanta itacefa wannan karuwar da kuke cewa wadda kuke cewa bawani karatu se yawon tazubar duk wannan be isheku ba saboda ke ɓeran masallacci ce ba kunya bare tsoron Allah kika wani yayimo wani tsumma jikinki wai zaki bita to ba inda zakije bama gayya umma tagaida Ashsha ki ƙara gaba hanyar jirgu daban ta mota daban kuma karki ƙara kiran yayata da Aunty kije can ki nemi Aunty a can badai nanba".
juyawa Jameelah tayi jiki ba kwari saurin kamo hannun ta Inteesar tayi tace"rabu da ita Jameelah kizo muje kekuma banason iskancin banza ko ke tace zatabi da zaki wani sakawa mutane baki taho mutafi bakomai sister".
"nagode Aunty Intee".
"bakomai sister".
"ai gaskiya ce dole infaɗamiki maƙiyinka har abada maƙiyinka ne ko ya zo ya nuna yanasonka ƙarya yike kullum bashi da burin daya wuce yaga bayanka shine saboda ke damo ce sarkin haƙuri mutum yagama takaki yadda ransa yikeso yazo kuma ya shigemiki ki ansheshi lokaci ɗaya ba dolema mutum gobema yaji daɗin hayemiki ba ai yaci ace ki nunamata kurenta koda zaki ansheta".
wata uwar harara Inteesar ta bankawa Khadijah ta kama hannun Jameelah suka shige gidansu Hauwah suka barta nan tsaye baki buÉ—e ta wuce cikin gida tanata masifa.

Suna shiga suka samu su Hauwah dasu Momynta sun kammala aikin snacks ɗin har sun fara celling ɗinsu da raping sheet turus tayi haɗe da kama haɓa ta ware fararen sexy eyes ɗinta tace"badai har kun gamaba Momy".
hararta Hauwah tayi tace"da jiranki zamu tsaya yi ne alanƙosa aida mun tsaya jiranki da ƙila sede muji kunya domin ke ɗinnan yadda kike da nawa ina tinanin a gidanki Uncle Zaid zesha fama dake".
damm ƙirjin Jameelah yabayar sakamakon tinowa datayi yau za'ah kawo lefen Zaid da wata bada itaba har yau be kirata ya sanarmata da yanason ta ba tana cikin wannan tinanin taji muryar Inteesar cikin shagwaɓa tace"Momy kinji Hauwah tana cemun wai alanƙosa".
murmushi Momy tayi tace"rabu da ita ƴar albarkana itace alanƙosa domin itama yanzunnan fitowarta kenan ta zauna ba abinda takeyi se aikin ci daka ni se Hindatu mukayi aikin komai kuma ma inban dage na fitar da ɗiyata kunya ba wazan fitar rabu da ita".
gwalo Inteesar tayiwa Hauwah haÉ—e da cewa"muje Jameelah".
"toh Aunty".
nan suka tafi sosai su Momyn Hauwah suka yi mamakin ganin Inteesar da Jameelah amma sesuka make zama suka yi suka tayasu raping É—in kayan suna gamawa Inteesar tace"Jameelah ki iba ki É—anÉ—ana".
"toh Aunty".
nanta É—auki komai É—aya taci itama Inteesar ta É—auka ta É—anÉ—ana suka taya Hindu me aiki kai kayan cikin gida bayan sun gama kamar gaske Jameelah tace"Aunty bara naje gida na shirya tunda naga har angama aikinma".
"toh sis".
nanta fita sukuma suka nufi ɗakin Hauwah suna shiga suka zauna kan ɗan madaidaicin gadon Hauwah taɓa Inteesar Hauwah tayi tace"wai Besty ya akai naganki da wannan yarinyar ne".
"wacce yarinya fa".
"hmm gaskiya Besty rainin hankalinki yawa ne dashi wacce yarinya nike nufi bayan Jameelah naga yarinyar nan ba wadda ta tsana sama dake kika wani jawomana ita ke bakya tinanin ko turota akayi dantaga abinda mukeyi ba".
"hmm keda Khadijah kuna bani mamaki wallahi na taho zanzo nan gidan yarinya tacemun zata bini so kuke na koreta shi ɗan adam ba'ah masa haka bakasan ranar da zemaka ba shi ɗan adam rana garesa ko biki taɓa karanta littafin marubuciyar nan ba Real eeshow mesuna BAR RAINA ALLURA (Itama ƙarfe ce) labarin ya ƙayatar dani sosai saboda marubuciyar ta nuna duk yadda mutum yakai da ƙinka a rayauwa be isa ya hanaka samun rabonka ba duk ƴinshi dakai ita rayuwa haka take zakaga kaƙi mutum ƙarshe shiɗin dai daka raina gaba shize temakeka gaskiya zan turomiki da littafin ki karanta zaki faɗakantu sosai labarin Sajida duniya ne".
"eh dai naji amma kinsan wani abu idan kika cigaba da wannan haƙurin naki mutane zasuyita cutarki saboda yarinyar nan da uwarta inda za'ah basu wuƙa ace su kashe wani abu da suka tsana wallahi ke zasu kashe nifa na tsanesu wallahi".
"dan Allah mubar wannan zancen batashi nike ba tin jiya narasa gane kan Zaid tunda yabar gidanmu na kirashi ya ɗaga ko magana be bari nayi ba yacemun wai aiki yikeyi idan yagama ze kirani shiru-shiru inata jira ya kirani be kirani ba dana daɗa kiranshi be ɗauka ba har zuwa yau idan na kirashi baya ɗauka na biki yadda nikejin zuciyata ba na riga na saba da waya dashi wallahi jiya se wajen huɗu bacci ya ɗaukeni hankalina har yanzu yaƙi kwanciya wallahi".
dariya Hauwah tayi ta kama baki tace"oh su Besty anyi nisa ba'ah jin kira wannan irin ƙauna haka harda ƙinyin bacci lallai Uncle ɗina ya iya love irin wannan mutuwa haka da kikayi kansa haka sefa kina mishi uzuri tunda kinsansu masu kuɗinnan sunada sabgogi a gabansu bare kuma satin biki yakama dole sekinmasa uzuri romeo".
"eh najin inban damu da mijin dazan aura ba wa kikeso na damu dashi amma aida baya iya bacci har seya yimun addu'ah na kwanta sannan muke sallama a waya shiyasa jiya nakasa bacci".
"hhh dole Besty ki kasa bacci tunda yariga yagama shagwaɓaki dole kice kinkasa bacci niko Allah muntuba aini gani nike ba'ah yo mutumin dazan kasa bacci ba dominsa ba gaskiya".
"hmm haka dai kikace dandai har yau baki haÉ—u da wanda kike so bane shiyasa wayasanma ke me zaki gwarama ni anga nawa".
"hhhh".
nan suka cigaba da hirasu da Æ´an tsare-tsaren ansar kaya.
Chapter 21 · 0% Book details