← Book details Lokaci Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 15

Sashe 3

Lokaci Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To Allah ya kyauta dai, ni bari in wuce, daman na zo ne na ji ko kin sami wani labari ne a kanta.?" Ta ida zancan tana mai mi
ewa tsaye.

"Sai anjima Asabe, Allah ya kyauta lamarin." ta sake furtawa.

"A sauka lafiya, na gode." Asabe ta yi furucin.

Har lokacin ba ta motsa daga in da take a zaunen ba.
****
Kakarin aman da ta jiyo daga
akin ne ya dawo da ita daga nahiyar tunanin da ta jima da lulawa.Cikin sauri ta iske
akin ta isa gareta tare da fa
"Lafiya?

Me ya faru.?"
Ba ta iya bata amsa ba illa ma ci gaba da aman da take yi.

A daidai lokacin ne Musbahu ya yiwa gidan dirar mikiya, ganin abin da ya ke wakana ya sa shi saurin fa
"Aunty mai zai hana mu je asibiti, na ga jikin nata kamar ba sau
Ba tare da ta kalleshi ba ta ce,
"Ina ga abin da za ayi ke nan, dan ni ma naga alamun haka, ma za jeka fito da mota mu wuce."
Juyawa ya yi ba tare da ya ba ta amsa ba ya wuce aikata abin da ta umarce shi.

Ka mata ta yi da nufin su wuce.

"A'a Aunty ki barni a hakana domin kuwa a yanzu ba abin da na fi
auna irin na ga na bar duniyar dan Allah."
Ta furta hakan cikin galabaita tare da
arin komawa ta zauna.

"Ba ki da ikon yankewa kan ki wani hukunci cikin
addarar da Allah ya iya kanta miki, ina so ki sa ni duk wani
an Adam da irin ta sa gwagwarmayar, ban san me ya faru da ke ba amma sai na ke jin matsalarki mai sau
i ce a kan ta wasu.

Ki yi ha
uri muje asibitin koma mene ne daga baya kya yi shi in dai har zai samawa zuciyarki da ruhinki salama." Aunty ta ce.
tana ji tana gani Aunty ta tasa ta a gaba suka wuce ,daman hausawa sun ce "Wai fa
an da ya fi
arfinka sai ka mai da shi wasa."
Mai_
osai
*LOKACI NE*
Mai_
osai
FCWA
San da suka isa asibitin ba su wani sha wahala ba, kasancewar akwai likitan da suka saba gani wanda shi ya zame musu tamkar likitansu.

Wasu
an tambayoyi ya mata kafin ya dangana ga yi mata wasu
an gwaje-gwaje, da ciki suka ha
a harda na hawan jini, jin cewar tana fama da jiri da matsanancin ciwon kai.

Gwajin farko ya tabbatar da hawan jinin sai kuma ciwon gyanbom ciki da kuma zazza
in maleriya.

Sai da ya yi
an rubuce-rubucensa na wasu
an sakanni kafin ya kallesu ya ce,
"A bisa bincike na da na yi ya nuna min tana da hawan jini wanda shi ne musabbabin da ya sa take jin jirin akai-akai.

Sai kuma zazza
in maleriya da kuma ulcer(ciwon gyanbom ciki).

Amma alhamdulillah zan
orata kan magunguna sai dai zan
an ri
etana tsawon kwana biyu koma fiye da haka zuwa dai ganin yanayin jikin nata."
Aunty ta sauke ajjiyar zuciya kafin daga bisa ni ta ce,
"To likita mun gode sosai ba damuwa a yi duk abin da ya kamata dan Allah."
Kamar yadda ya ce musu zai ri
eta hakan ce ta faru, kwanciya ya ba ta tare da saka mata robar
arin ruwa.

Kallonta kawai Aunty ta ke yi tana mai kuma nazartar ta, ba ta san meke damunta ba, ba ta san wace ce ita ba, ba ta san daga ina take ba , abu
aya kawai ta sa ni tsinto ta da suka yi lokacin da suke gab da ka
eta a kan tsakiyar titi, ganin kamar ba ta cikin nutsuwarta ya sa su
aukarta zuwa gida wanda shi ya kawo su wannan ranar.

Ta fice daga asibitin tana mai kuma jinjina tausayinta cikin ranta.

Washe gari da safe bayan ta
arasa asibitin, har ma ta tarar da ita ta
an sami wani
an sassauci daga jiya zuwa yau.

Bayan ta samu da
yar da ci abinci cikin san sake kwantar mata da hankali ta soma furta mata lafuza ma su da
"Ban san mece ce damuwarki ba, ban san ke wace ce ba amma ina so ki sakawa zuciyarki nutsuwa da salama ki manta da komai ki mayar da komai na ki ga Allah subhanahu wata'ala, wanda shi ne maji
ancin dukkan wasu al'amura, kuma sarki
aya jal!

Sarki buwayi gagara misali na tabbata ki ka yi haka to lallai ba zai barki haka ba zai da fa miki."
Ta share hawayen da suka gangaro a kan kumatunta
tana mai kallon Aunty da Musbahu da ya shigo a lokacin ka na ta ce,
"Tabbas kun min halaccin da ba zan ta
a mantawa da ku ba ko da bayan raina ku na ma
ale a cikin zuciyata.

Bakina ba shi da abin da zai gode muku sai dai na ce Allah ya biya ku da gidan aljanna.

In sha Allahu kuma a yau ba gobe ba zan baku labari na za ku san ko ni wace ce, kuma za ku ji irin rawar da
addarata ta taka cikin rayuwata.

Ba ta ba su damar magana ba ta ci gaba da furta,
"Suna na Hajara Hashim
Jama'are.

Duk da cewa na sami sunan mahaifina a bakin mahaifiyata.

Ni
in haifaffiyar
ar garin Kano ce.

Ni da mahaifiyata muna zaune a unguwar Ja'in.

Ni ka
ai ce 'ya wajen mahaifana duk da cewa ban rayu da mahaifina ba sai mahaifiyatana ta so cikin so,
auna da kulawarta.

A yadda
na ji Mamana na fa
a tun ina yarinya ba ni da wani farin jini dan kuwa yara ba su fiya zuwa gareni ko da da sunan yin wasa ba, kuma na kasance miskila ta bugawa a jarida abar kwatance, da fari ta yi tunanin ko dan miskilanci na ne amma daga baya sai ta fahimce sam ba haka ba ne ba.

Bari na
an yi muku gwa-gwa-gwa cikin tafiyar kamar yadda mai koyan tafiya ke yi.

Mama na yawan ba ni labarin su
in ba mazauna nan ba ne ko na ce ta kance ita ba
ar nan ba ce hasalima zuwo ce, ita ka
ai ta zo garin Kano sai tsohon ciki, wanda bada jimawa ba bayan zuwanta ta haifeshi in da ya kasance ta sami
iya mace ranar suna ko yankan da ake yiwa yara na rago
ba ta yiwa 'yar ba tunda babu hali ta ra
a mata suna HAJARA wato ni ke nan.

Ta kan ce min iya gata da nuna kulawa tana
arin ba ni ,haka zalika ma tana
ari wajen ganin ta inganta tarbiyata
ta sama min karatu, inda ta kai ni makarantar Allo da ke nan kusa da in da muke.Duk da cewa Unguwar babu irin wa
annan makarantun sosai amma mu Ja'in
in in da muke zaune kamar 'yan gargajiya haka mu ke, I! to haka ne mana tunda duk ba mu da ku
i sai rufin asirin Allah da wadatar zuciya.
fara zuwa makarantar Allon sannu-sannu , Allah buwayi mai raba ni'imominsa ga bayinsa da ya tashi raba ta masu
walwa sai ya raba da ni ni ma na sami kaso na.

Duk abin da zan yi in dai fannin karatu ne to zan
auke shi a kaina duk yawansa.

Lokacin da na fara wayo sosai da sosai na kai shekara biyar na fara haddace al
ur'ani wanda na yi wajen izu biyu, idan na dawo gida Mama kan min bita kuma mu kan yi bita tare da ya ke tana da nata ilimin daidai gwargwado.

Lokacin da na shiga shekara ta takwas a duniya ta yi iya bakin
arinta wajen saka ni a makarantar boko, Mama tana yin aikatau cikin wani gidan masu hannu da shuni, ta kan je da ni gidan a lokacin akwai wata yarinyar Hajiyar gidan tana so na , za mu yi wasa tare duk da cewa ta girme ni a shekaru , hakanan ko a jikin girma ba za ka ha
amu ba domin ta fi ni nesa ba kusa.

Wannan duk ina gaya muku ne ta jinsa da na yi bakin Mama duk da dai ni ma ina
an tuna wani abun cikin yarintar rayuwata.

Ba ta basu damar magana ba ta
ora da,
"Haka rayuwa ta ke ta garawa yau da da
i gobe babu, idan ya kasance ni da Mama ba mu halacci gidan aikin ba to Safina
ar Hajiya za ta saka a kawota ta yinar ma na, ko a zo har gida a tafi da ni wajenta.

Sai dai bamu san meke faruwa ba
a iya wasu
an watannin da muka
auka da su babu wani sauyi amma lokaci guda sai muka soma ganin canji wajen Hajiyar, zaman mu da su sai ya koma shigen kalar na ma
iya mu koma zaman doya da manja.

Guiwoyinmu ba sukammala sakewa ba sai da muka wayi gari Hajiyar na sanar da mu ta sami wasu
an aikin dan haka ta sallame mu, ina kuka Safina na kuka mu ka rabu.

Mai_
osai
*LOKACI NE*
(Gajeran Labari)
Mai_
osai
FCWA
Biyar.

Rayuwa sannu a hankali ta soma yi mana zafi dan babu wani aiki da mu ke yi ko sana'a
da za ta saka mu sami ku
i.

Sai da mu ka yi a
alla sati uku a haka sannan Mama ta fara ka sa min kayan yara na soma zama a waje ina saidawa ana ciniki sosai kasancewar yaran da ke unguwar, amma wani abin mamaki lokaci guda kuma sai cinikin ya
auke wuta
Ganin haka sai ya sa Mama ta koma saida
osai ,ni ce mai zubawa idan anzo siya, ni zan kai mata marka
e da sanyin safiya, sai ya zamana karatuna ya fara wulagigi.

Kamar wasa shi ma sai ciniki ya soma habbaka siya ake yi ba kama hannun yara.
Chapter 3 · 0% Book details