← Book details Lokaci Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 15

Sashe 14

Lokaci Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin hanzari Umma ta janyota zuwa jikinta tana mai rungumeta.

" Mun yafe miki
iyarmu."
"Alhamdulillah godiya ga ubangiji da ya kawo
arshen wannan al'amari, abu na gaba kuma batune a kan auren Likita da ya ke san yi ga KHAUSAR." Alhaji Musbahu ya ce.

Khausar, Hajara ,Musbahu sai da suka zabura kamar wa
anda a ka tasa
daga barci, a ba zata suka ji maganar Alhaji.

In ka cire sauran jama'ar ban da Umma da Baba da alama kenan sun san da zancen.

"Bari na warware muku zare da abawarsa."
"Bayan dawowarmu daga Jama'are mun yi Magana da likita ya shaida min cewa ya na san aurenki ,amma sai na dakatar da shi ta hanyar fa
ya bari muje ga iyayenki wanda shi ne shi ma ya ce zai bimu.

Na sanar da iyayenki ukun dan ya kamata su san da maganar kuma sun yi farin ciki sosai.

Yanzu kuma zamu ji ta bakin iyayenki biyu da kuma ke.

Ina fata za ki amince da bu
atarsa dan na san ba za ki wula
anta ba.

In kuma na yi ba daidai ba to kugafar ce ni."
Cikin farin ciki Baba ya soma fa
"Babu abin da ka yi wanda ba daidai ba, kai matsayin uba kake gareta.

Ban san da wane baki zan gode maka ba,na tabbata ba za ka ta
a bari ta aure wanda zai cutar da ita ba."
Ya juya ga Khausar ka na ya ce,
"Ni ba zan miki dole ba, amma ina baki shawara da ki amshe shi, ina so ki je ki yi shawara da zuciyarki da
walwarki."
Ita dai sauransukawai take yi,amma ba za ta iya rayuwa da wani bayan Abbas
inta ba, mutumin da ya sota tana jin ba wanda zai iya zama da ita yadda ya mata.

Da wannan tunanin nata da take yi taji taron ya tashi bayan sun shafa addu'a.

Sai bayan la'asar su alhaji suka bar gidan bayan sun bar Hajara da Khausar.

Musbahu ji yake ina ma shi ma a ce ya zauna.

Duk yadda likita ya so ya gana da Khausar abin ya faskara,haka ya ha
ura ya ce ya dawo gobe.

A daren ranar Khausar ta ziyarci gidansu
awarta Rabi'a ita da Hajara,ta yi kukan rashin Baban Rabi'a wanda ya zama uba na biyu gareta, mahaifiyarta kuwa ta yi farin cikin ganinta sosai.

In da ta tambayi Rabi'a ta sanar mata tana Abuja wata biyu baya ta zo ta koma.

Ta yi mamaki sosai yadda har Rabi'a ta zo bata nemeta ba, ba kuma ta kirata ko da a wayane ba ,basu bar gidanba har sai da ta
i lambarta da kwatancan inda take a Abujan.

Washe gari suka zuba sammako zuwa gidan
ar'uwarta.

Sosai su ke kuka na rashin ganin junansu .Sun yi kewar juna ba ka
an ba.

Ganin abun ba na
are bane ya saka Hajara shiga tsakaninsu tana mai tsokanarsu,sai ga shi dukkansu sun shiga darawa kamar ba su ne
ke yin kukan ba.

Ba su baro gidan ba sai bayan sallar isha ,shi ma ji su ke kamar kar su rabu.

Bayan sun dawo ne Umma ke shaida musu Likita da Musbahu sun zo ,harma sun nemi ta basu kwatancen inda su ke ta sanar da su ba jimawa
za su yi.

Amma sun ce za su dawo.

Khausar ji ta yi gabantana fa
uwa raass,
walla ta cika mata kurmin idanuwanta, ba ta iya bawa Umman amsa ba ta shige
aki.

Ganin haka ya saka Hajara mara mata baya.

A gefen gado ta iske ta zaune, hannu ta saka tana mai dafa kafa
arta tare da furta.

"Na fahimci cewar har yanzu kina cikin damuwa, sannan uwa uba kina tunanin yadda za ki iya auren Likita saboda soyayyar Abbas cikin zuciyarki,amma ina so ki sa ni komai da yake faruwa daga Lillahi wahdahu ne.

Ina so ki kar
i duk wani tsari da hukuncin da ya yi miki,ki
auka wata ni'imace Allah ya aiko miki da ita shiyasa Likita ya ce yana sonki, dan Allah kada ki bari damar ta wuce."
Ta share ruwan hawayen da ke kwance saman fuskarta tana mai fuskantarta ka na ta ce,
warai ina tunanin yadda zanyi rayuwa tare da wani in ba Abbas ba, amma na amshi duk irin hukuncin da Allah ya wanzar a kaina, na amince zan aure shi."
Wani da
i ya mamaye zuciyar Hajara, ta saki dariya tana rungumota jikinta.

"Yawwa Auntyna ko kefa." Hajara ta ce.

Khausar ta yi murmushi ka na ta ce,
"Ina so kimin wata alfarma
anwata." Ta
arasa tana kamo hannayen Hajara duka biyun cikin nata.

"Ina jinki Auntyna, in sha Allahu in dai ba tafi
arfina ba zan miki kowacce iri ce."
"So nake ki aure Musbahu."
Ta jefa mata maganar a ba za ta.

Cikin sauri ta kalli Khausar tana mai girgiza kanta.

"A'a Aunty dan Allah.........."
"Dan Allah Hajara kimin wannan alfarmar, Musbahu na tsananin sonki sosai fiye da tunaninki, ki yadda da ni." Ta katseta ta hanyar jefa mata maganar.

Shiru ta yi kafin ta ce,
"Shi kenan Aunty ,Allah ya shige mana gaba, amma ya aka yi kika san ya na sona?"
Sai da ta murmusa ka na ta ce,
"Tun kwanciyarki asibiti alamomin sonki suka soma bayyana gareshi na fahimci hakan ganin yadda ya damu dake fiye da yadda na damu dake, na kuma gasgata zancen lokacin da na tuna
an zamanki a gidanmu yadda ya ri
a jele
e a kanki,da na tutsiyeshi sai ya gasgatamin tantamata amman ya ro
eni da kada na sanar miki har sai sanda ya farauto zuciyarki, ni kuma sanin halinki kada a kuma zagaye na biyu ya sa na fasa sirrin na ro
eki da kaina sai a ka yi sa'a kika amshe shi hannu bibbiyu."
Hajara ta yi dariya mai yawa tare da rufe fuskarta tana furta, "Kai Aunty".

Wajen tara da kwatana dare Likita ya iso gidansu Khausar shi ka
ai ,bayan ya yi sallama zauren gidan
Baba na nan shi ya masa iso zuwa
akin dake soron gidan.

Khausar ta shigo bakinta
auke da sallama, suka shiga gaisawa.
*LOKACI NE*
(Gajeran Labari)
Mai_
osai
FCWA
Goma tara(
arshe)
Mintuna hu
u ba wanda ya ce uffan ,ganin shiru ba
arau ba ne ya saka likita furta,
"Da farko ina mai baki ha
uri a bisa kutsen da na miki cikin rayuwarki, ban sa ni ba ko zan sami matsuguni daga cikin sashen zuciyarki ko da ban shiga can ciki ba?

Sannan ina fata ki zama uwar 'ya'yana abar alfaharita.

Idan kin amince zan yi zallar farin cikin da babu algus, idan ba ki amince ba zan yi ha
urin hakan nasan Allah ke shirya kowanne lamari,amma zan yi ba
in ciki mai yawa bisa rashin samun mace tagari da na yi.

Na riga da na sanar da iyayena komai, na kuma bu
aci da su bani damar jin ta bakinki ,ko yanzu kika amince gobe za sukawo ku
in aure gidanku dan saka rana bana san tsaye-tsaye." Ya dire zancen ya na kallon yadda ta yi
asa da kanta tana faman wasa da
an yatsunta goma.
an jima kamar ba za ta ce wani abun ba cikin sanyayyiyar murya ta ce,
"Allah ya tabbatar mana da alherinsa."
Sosai ya ji da
in maganarta ,hakan ya nuna masa kenan ta amince kuma ya gane hakanne ta addu'arta.

Ji yake kamar ya ha
iyata dan murna.

Sosai yake janta da hira amma ta kasa sakewa da shi, cikin farin ciki ya mata sallama ya bar gidan na su.

Musabahu kuwa lokacin da ya sami sa
on Auntyn nasa na jin Hajara ta aminta da shi ya ji kamar ya zuba ruwa a
asa ya dinga lasa, alla-alla yake gari ya waye ya iso gareta ko dan ganin kyakkyawar fuskarta.

Bayan kwana uku da faruwar wa
annan al'amuran a ka saka ranar Khausar da Likita, sai Hajara da Musbahu wata biyu cif, zu ku ga murna wajen ahlin.

Mama ta so a bata Hajara ta yi bikinta a Jama'are kasancewar bikin saura wata guda za ta koma can ita da Kakar Hajara dan ta sami sau
i sosi fiye da zato.

Amma Alhaji Jibril ya hanata hakan, ya kuma tabbatar mata su ma ba zasu koma ba har sai bayan biki shi zai
au nauyin komai,mutanen Jama'are ma za a kai mota duk wanda zai zo za a
akkoshi zuwa bikin.

Ba yadda ta iya haka ta sawa ranta salama.

Bayan kwanaki goma Khausar da Hajara suka shirya tafiya Abuja wajen sahibarta,cikin tafiyar har da Musbahu dan ya na ce sai ya bisu.

Cikin hukuncin Allah ba su sha wahala ba suka samo gidan, kasancewar Musbahu ya san garin ABuja sosai.

Sanda suka yi ido hu
u sai kuka, kukan da suka kasa gane na mene ne.

Sosai Khausar kewa Rabi'a
a kan nesanta kanta da ta yi da ita.

Ba ta san me za ta ce mata ba, dan ita kanta bata da hujjar da
za ta kare kanta, sai kawai ta shiga bata ha
uri.

San da
ta ji auren Auntyn na ta murna kamar me wajenta ba za ta iya fa
uwa ba.

Kwanansu biyu suka baro Abuja, ba su taho ba sai da Rabi'a ta mata al
awarin kasancewa da
ita har abada kuma zuwa biki dole in dai ba rashin lafiya ko mutuwa ba.

Shirye-shiryen biki ake sosai.

Rabi'a ta zo saura sati guda biki, kullum a tafe su ke babu zama.

A na i gobe
aurin aure suka ziyarci unguwar maciyi amana malam kamar yadda suka yi wancan karan, katin
aurin auren suka kai mi shi, sai dai ganin halin da ya ke ciki sun tausaya masa.

Ya na fama da larurar
afa dalilin wani hatsari da ya yi a kan mashin, wanda har ya yi sanadin rasa mazantakarsa.

"Ina fata za ka halarci taron
aurin auren da yafi kowanne ?

Dan kada a zo a baka labari ka san ance gani ya kori ji,gwara ka ganewa idanka Khausar ba ta yara ba ce
ananan
wari irinka." Rabi'a ta ce.
Chapter 14 · 0% Book details