← Book details Kulsum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 22

Sashe 8

Kulsum Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Wani gumi ne ya keto wa Turaki tun daga tsakar kansa har zuwa yatsar kafarsa. Ya san Maimartaba ba ya zolaya, kuma ba ya fadin abin da bai aikata ba. Idan mafarki yake yana rokon Allah ya farkar da shi, Maimartaba ya janye abin da ya gaya masa yanzun nan.
Maimartaba ya ci gaba da cewa, “Muna fatan yanzu za ka daina gudun mu, tunda mun bi ra’ayinka, mun yi maka yadda ka ke so? Wato zama babu aure?”
Hawaye suka zubo daga idon Turaki, ya rasa da bakin da zai yi wa mahaifinsa bayanin cewa; gabadaya shekarun da ya yi, ya yi su ne cikin son Kulsumu, da nadamar abin da ya yi musu. Sannan ganin girman laifin sa ne ya hana shi dawowa har sai da Abdul’Ahad ya karfafe shi. Ba fitsarin kwance ba, ko kashin kwance ta ke yi a yanzu kam ya daura dammarar zama da ita cikin so da kauna. Sannan as a medical doctor zai nema mata magani iyakar iyawarsa, idan ma ba ta samu lafiya ba ya alkawarta wa ransa ci gaba da zama da ita da lalurar da Allah ya dora mata. Har bincike na musamman ya yi a kan lalurar ‘Eneuresis’ kasancewar ba fanninsa ba ne, ya kuma samu kwarin gwiwar cewa, da ya dawo zai kai ta inda za ta samu magani.
A wannan halin Umma ta shigo ta same su. Dukkan su babu wanda zuciyarsa ba ta motsa ba ganin Turaki yana kuka. Daga yarintar sa zuwa yanzu za su iya kididdige sau nawa ya yi kuka a rayuwarsa. Amma ba su yi saurin nuna karayar su ga laifin da ya yi musu ba tukunna, domin ya jawo sun cutar da yarinyar mutane, sannan ya nuna wa duniya ba su isa da shi ba. Wannan shi ne babban abin da ke kara fushinsu a kan dan nasu.
***
Washegarin ranar Kiru ya tafi wajen Yayarsa Hadiza. Hadiza ta karbe shi kadaran-kadahan don ita ma ya bata mata rai ba dan kadan ba. Allah ya gani tana son Kulsumu! A zaman shekaru hudu da suka yi da yarinyar ba za su taba cewa ga aibunta ba. Ta shiga ran su sosai sabida kyawawan halayenta. Amma yadda Turaki ya kwantar da kai yana ba ta hakuri tare da rokonta ta shige masa gaba ya shawo kan iyayensu su dawo masa da matarsa su kuma yafe masa laifin sa, dole ta tausaya masa. An ce naka sai naka, don duk cikin kannenta Turaki ne favourite dinta, tana sonshi sosai a matsayin sa na namiji daya tal a cikinsu. Dole ta hakura ta karbi uzurinsa ta ce ya tafi gobe za ta zo gidan insha Allahu za su shawo kansu, amma tana mai kara gaya masa bai kyauta musu ba, kuma ya yi babban kuskure. Kulsumu duk da kasancewar ta tashin kauye, mace ce cikin dubu ba zai samu kamar ta da sauki ba. Turaki ba ya ja, akan ko me aka ce ya yi, ya karbi laifinsa, shi mai baiwa kowa hakuri ne da dukkan iyawarsa.
Washegari Hadiza ta zo Gaya, Umma ta yi mamakin ganinta ko waya ba ta yi ta ce za ta zo ba.
Bayan sun gaisa ta ce, “Umma wajenku na zo ke da Maimartaba, kuma a tare nake son ganinku”.
Ko kusa Umma ba ta kawo zancen Turaki ba ne, don ba ta san jiya ya je Kiru ba, ta ce, Maimartaba yana da baki, in sun tafi sai mu je. Allah ya sa dai lafiya”.
Hadiza ta ce, “Lafiya kalau, sai alheri Umma”.
Bayan tafiyar bakin Maimartaba suka je suka same shi a falon da yake ganawa da iyalinsa. Ya dubi Hadiza ya yi murmushi, ya ce,
“Fulanin Kiru ku ne tafe?”
Hadiza ta zube ta gaida mahaifinta yana tambayarta ‘yan jikokinsa, ta ce, duk a gida ta baro su, ita kadai ta zo. Sannan ba ta bata lokaci ba ta dora da abin da ya kawo ta, wato nema wa Turaki afuwa daga gare su, ta ce ba komai ya hana shi dawowa ba illa iyaka yana hango girman laifin da ya yi muku ne, yana jin nauyi har sai da abokinsa ya ba shi shawararar ya ture hakan ya fuskance ku, ya karbi laifinsa komai girman sa.
Don Allah Umma ku yi hakuri ku maida masa matarsa tunda shi da kanshi yanzu ya zo ya ce yana son ta, na kuma fahimci wallahi da gaske yake, kuma wannan shi ne karo na farko da ya taba saba wa umarnin ku. Sannan karo na farko da Turaki ya taba bude baki duk kawaicin sa ya ce yana son mace. Ni na tabbatar su Goggon Kulsumu ba za su ki dawo da ita dakinta ba tunda dama ba su suka nemi a mayar musu da ita ba, daga gare mu ne”.
Maimartaba ya ce da Hadiza shi ai tun jiya ya yafe wa Turaki, amma ba zai zama karamin mutum a idon talakawansa ba, ba zai yi masa bikon Kulsumu ba, ya je da kansa in iyayenta sun gamsu da nadamar sa su sake bashi aurenta, kada kunyarsa ta sa su yi abin da ba sa ra’ayi. Umma ma ta ce tana bayan ra’ayin Maimartaba.
Hadiza ta samu Turaki a sashensa ta yi masa bayanin yadda suka yi da iyayen su. Ko ba komai hankalinsa ya kwanta tunda sun yarda sun yafe masa, ya sa a ransa wannan karon shi da kansa zai dawo da Kulsumu rayuwarsa. Zai yi amfani da hikimarsa ta Da namiji wajen sabunta rayuwar su, zai nemi soyayyar Kulsumu, ba tare da taimakon kowa ba!!!.
Washegari Hadiza ta koma Kiru gidan mijinta.
Chapter 8 · 0% Book details