← Book details Kulsum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 22

Sashe 5

Kulsum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan fitar Aunty Sakeena ta ja yaran suka nufi dakin da ya zam nata, suka kwaso toys dinsu suna ta wasansu kamar sun dade da saninta. Ba'a fi one hour da fitar Dr. ba suka ce yunwa suke ji, ta ja su suka tafi kitchen, cikin tsanaki da tsananin kula ta kunna cooker din ta dafa musu noodle da dafaffen kwai suka zauna bisa Island din kicin din suna ci tana firfita musu. A haka Babansu ya zo ya same su, kanta a kasa ta gaishe shi ya ce,
“Sakeenah fa ba ta dawo ba?”
Ta ce, “Ai ba ta jima da fita ba ma”.
“O.K”. In ji Engnr. Farouq sannan ya juya ya dau abin da ya dawo da shi ya fita ya sake komawa ofis.
Sai karfe daya Dr. Sakeenah ta dawo, yaran suka rungume ta suna mata oyoyo! Kulsumu ta karbo jakar hannunta zuwa dakinta, ta ce, “In ce ko ba ku yi wa Aunty Kulsumu rigima ba?”
Har suna hada baki wajen cewa, “Ba mu yi ba Mummy, ta dafa mana noodle da egg mai dadi mun ci mun koshi”.
Ta dubi Kulsumu da fara’a ta ce, “Good, na ga alama Kulsum kina da kokari. Na gode sosai”.
Dan murmushi ta yi ta ce, “Lah Aunty me na yi na godiya?”
Ta ce, “Kula da yara mana, bari in yi girki sai mu samu mu zauna. Amma tare za mu shiga kitchen din”.
Tare suka shiga madafin tana ba ta kananan ayyuka tana taya ta, tana yi tana mata bayanin komai. Nan ta fahimci Kulsumu yarinya ce mai saurin daukar abu dakaifin basira, kuma ba ta da kauyanci duk da cewa daga kauyen ta fito. Komai ta gwada mata sau daya ta gane, har tambayoyi ta ke yi mata, wannan duka zan yanka ko ya ya? Ana motsawa ko ba a motsawa? Maggi dunkule guda nawa za a zuba? Da haka har suka gama girkinsu mai rai da motsi.
Sakeenah ta ce ta dauki warmers din ta jera a dinning ta je ta yi sallah, sai ta zo ta dau abincinta ta ci. Ita sai mijinta ya dawo za su ci tare.
Dr. Sakeenah ba ta samu zama da Kulsumu officially ba sai washegarin ranar sabida Kulsumu ta kara sakewa da ita sosai, kuma ta samu hakan, don cikin kwanaki biyun da suka yi tare Kulsumu ta saki jikinta da Sakeenah sosai. Yau da dare wajejen karfe takwas ta shigo dakin nata, ta yi sassaukar kwalliya sai kamshi ta ke da alama mijinta yana gida.
Kodayake ta lura ko ba ya nan Dr. Sakeenah kullum cikin ado da kamshi ta ke, dazu ta ba ta wasu (deo sprays) masu sanyin kamshi har guda uku ta ce ta dinga amfani da su. Ta tadda Kulsumu na gyara kayanta da ke cikin trolley tana jera su a wardrove don Dr. ta gaya mata komawarta Abuja ba rana. Da sallama ta shigo, Kulsumu ta amsa.
Ta ce, “Aiki ake ta yi ne Kulsum?”
Ta yi murmushin ta mai kyau, har dimples din suka lotsa cikin kumatunta sosai, ta ce, “Kayana nake mayarwa wardrove zan fi jin saukin daukansu a can”.
Sakeenah ta zauna a gefen gadon tana bude kofofin hancinta sosai ko za ta ji sauyin atmosphere a dakin, amma ba ta ji ba. Kulsumu tana kula da kanta sosai da muhallin da ta ke zaune, ba ta bari a ji wani sauyin atmosphere ko ya ya a tare da ita mai alaqa da lalurar ta.
Dr. ta ce. “Bar aikin ki zo mu yi magana mai muhimmanci in mun gama sai ki ci gaba”.
Ta ajiye rigar da ta dauko ta dawo gefen Sakeenah ta zauna, ta kuma tattara dukkan hankalinta ta mika mata.
“Tun yaushe ki ke yin fitsarin kwance?”
Ta sunkuyar da kai cikin jin nauyi.
“Abin da zan iya tunawa gaskiya tunda aka haife ni”.
Dr. ta ce, “Kamar ya ya ki ke ji kafin ki yi shi?”
“Mafarki nake na tsugunna a toilet zan yi, daga nan sai kawai in ji ni cikin laima”.
Dr. Sakeenah ta dan kura mata ido, sannan ta nisa ta ce, “Kulsum sunan matsalarki a kimiyyance 'NOCTURNAL ENURESIS’. Ana kuma kiran sa 'bed-wetting' da harshen turanci. Wasu tun haihuwa sai sun girma suke dainawa. Treatment din sa guda biyu ne; pharmacological and non-pharmacological. Na farko da zan dora ki akai 'is non-pharmacological' ni da ke za mu hada gwiwa mu yi shi.
Da farko dai daga karfe shidda na yamma kar ki kara shan ruwa ko wani abu mai ruwa-ruwa. Sannan kafin ki kwanta ki tabbatar kin yi fitsari. Da tsakar dare zan dinga zuwa na tashe ki ki je ki yi fitsari, sai kuma da asubah na sake zuwa na tashe ki ki je ki yi. A hankali system din jikin ki zai saba da hakan, zan saita alarm da zai dinga tashi na ina zuwa tashin ki at interval. In ya ki bari bayan watanni kamar biyu zan yi referring dinki ga 'kidney and bladder specialist/nephrologist' akwai maganin da za su rubuta miki bayan sun yi examining din ki”.
Kulsumu ta gyada kai cikin fahimta, Dr. Sakeenah ta kara da cewa, “Muna fatan ya tafi after this non-pharmacological treatment, ba sai mun kai ga shan maganin ba”.
A sanyaye ta ce, “Insha Allahu Rabbi”.
Dr. ta ce tana mai mikewa tsaye, “In kin gama jera kayan sai ki je ki yi fitsarin ki kwanta, Allah ya tashe mu lafiya”.
Ta amsa da, “Ameen Aunty, nagode”.

*** *** ***
Tun daga wannan ranar suka fara wannan excercise din, Sakeenah ba ta yi kasa a gwiwa ba, kuma ba ta kuskure wa wajen tashinta a kan lokaci sau biyu cikin dare da kuma asubahi ta je ta yi. In ta bushi iska kuma ta zaga gari da ita ta ga garin Lagos ta yi mata sayayyar kayan amfani tare da su Walid. Hajiya na kira akai-akai ta ji development (cigaban) da ake samu haka Goggo, Dr. Sakeenah na yawan kiranta ta hada su a waya, har Baffa ma in yana gida. Kulsumu sai kara mulmulewa ta ke boyayyen kyawunta na bayyana sarari. Garin Lagos ya karbe ta har fiye da Abuja.
Dr. Sakeenah ta samu aiki da Lagos Specialist Hospital, don haka zamanta a gidan sai ya karanta. Duk hidimomin gidan da kula da su Waleed sai ya dawo kan Kulsumu. Ba ta da kiwa ko kadan da jikinta da zuciyarta ta ke taimaka wa Dr. Sakeenah. Wannan ya sa ta shiga ran Sakeenah sosai, ta kuma dage wajen koya mata duk abin da zai amfane ta, kama daga girki, tsafta, turanci da sauransu. Da daddare sukan zauna duk gidan su yi hira kafin lokacin kwanciya barci, amma Kulsumu ba ta sakewa sam in Engnr. Farouq na wajen, Dr. Sakeenah kuma ba ta barinta a daki ita kadai in har suna gida sai ta takura mata ta zauna a cikinsu. Ta kan ce,
“Kulsum in kin tafi zan yi kewarki!”.
Rabon da ta yi fitsari cikin barci har ta manta. Ita kanta a jikinta tana jin ta fara samun lafiya, ko ko ta ce ta samu lafiya daga lalurar fitsarin kwance. Duk da haka basu bar fargabar ko zai dawo ba.
Ilai kuwa, bayan wata biyu da rabi suna murna lafiya ta samu kawai rannan ta kuskure bacci ya dauketa ba tareda ta je ta yi fitsarin ba, ai kuwa ba'a jima ba ta ji ta cikin danshi.
Washegari hankali tashe ta gayawa Dr. Sakeenah, inda ba bata lokaci tace ta shirya su wuce asibiti tare. Asibitin da take aiki ta kaita, da kyar suka samun appointment na ganin 'kidney and bladder specialist' wanda shi kadai ne duk fadin asibitin. Kuma visiting Doctor ne a wata sau daya yake zuwa, sun yi sa'a sanda suka samu appointment saura sati daya ya zo asibitin.
Ranar da suka samu ganin nephrologist din ya dade yana yiwa Kulsumu tambayoyi, ta dinga amsawa da taimakon Dr. Sakeenah. Ya ce da Sakeenah "urinary incontinence (another medical name for bed-wetting) among adults is now rampant. Wato lalurar fitsarin kwance ga manya matsala ce da ake samu sosai yanzu. A karshe ya hada ta da wasu magunguna (tricyclic antidepressants) wato tofranil (imipramine), da kuma DDAVP (desmopressin acetate) bayan series of gwaje-gwaje, wadanda Kulsumu zata dinga sha based on prescription. (A bisa ka'ida).

In ta zauna sai ta yi ta tunanin wahalhalun da kakanninta suka yi shekara da shekaru suna sha wajen nema mata lafiya, yawo tsakanin kauyuka bukkokin masu magani, ashe ciwon ta maganinsa na asibiti ne Allah bai taba ankarar da su ba. Domin tuni jikinta ya saba da system din da Dr. Sakeenah ta dora ta a kai kuma yana karbar medication din da take sha babu kuskurewa. Cikin ikon Allah suna saka ran ingantacciyar lafiya ta samu ga Kulsumu.
Wasa-wasa yau ta kwashi watanni hudu gidan Sakeenah, Hajiya Nasara ta yi-ta yi Sakeenah ta dawo mata da Kulsumu, tunda ta tabbatar mata ta samu lafiya kamar yadda babban likitan ta ya tabbatar mata a ziyarar karshe da suka kai masa amma Sakeenah ta ki, kullum da uzurin da ta ke bai wa Hajiyar. A zahiri kuwa ta saba da Kulsumu ne, ba ta son rabuwa da ita. Ita ma Kulsum ta saba da Sakeenah da yaranta sosai, amma ta fi so ta koma wajen Hajiya ko sabida Nasma, sun saba sosai kullum suna tare a wayar Sakeenah. Rannan da Nasma ta bugo mata waya, Dr. Sakeenah ta kawo mata daki, sai ta ce,
“Ni dai bari in dauki salary dina, waya zan saya miki, ko kwa bar ni in huta ke da Nasma”.

Nasmah ta gaya mata hutunta ya kare cikin satin nan za ta koma makaranta.

“I will be calling you when I get back to Nottingham. I wish you all the best Sis".
(Zan din ga kiran ki idan na koma Nottingham. Ina miki fatan alkhairi).

Wannan ce sallamar su ta karshe da Nasmah, kafin ta bar gida Abuja zuwa U.K.
*****
Chapter 5 · 0% Book details