Sashe 6
Kulsum Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Dr. Sakeenah ta cika alkawari, tana daukar albashinta ta saya mata ‘yar karamar waya samfurin Siemens, zo ki ga murna wajen Kulsumu. A ranar Goggo da Baffa suka san ta yi wayar kanta, domin kuwa raba dare suka yi suna hira.
Washegari kuma ta kira Nasmah, “Nasmah albishirinki, Aunty Sakeenah ta saya min waya”.
Nasma ta ciji yatsa, “Shi ne ta riga ni? Ya Taufeeq na tahowa wannan satin, na ba shi waya mai kyau ya kawo miki”.
“Allah sarki Aunty Nasma, ke da Aunty Sakeenah ban san wa ya fi kirki ba. Kada ki damu, zan aika wa Babana daya ‘Yalleman, ni kuma in yi amfani da daya, ba ki yi asarar kudinki ba. Na gode ‘yar uwa”.
Cikin ranta ta ke tambayar kanta, tsakanin Hajiya Nasara da ‘ya’yanta wa ya fi son kyautata mata???
*** *** ***
UNIVERSITY OF READING, UK
Yana sanye da bakaken Japanese suit, ya daura farar rigar likitoci a kai, baki ne dogo, tun da can ba shi da kiba kamar yadda ba shi da rama. A duniya akwai kyayawan bakar fata wadanda kyawunsu kan sanya nationality dinsu cikin kokonton daga kabilar da suka fito. Hakika wannan matashi yana cikinsu, domin kai tsaye ba za ka gane daga kasar da ya fito a (Africa) ba in har ba shi ya bude baki ya fada ba.
A babban dakin taron malaman jami’ar 'Reading' wato ‘seminar room’ duk ciki su biyu ne bakar fata.
Dakin Seminar din a cike yake da malaman jami’ar daga tsangayoyi daban-daban na faculty of medicine. Kowanne daga ciki yana wakiltar tsangayarsu ne (delegates). Babban teburi ne mai tsayi da fadi wanda aka zagaye da kujeru, a gaban kowanne delegate dan karfe ne mai dauke da sunan mamallakin kujerar da sunan tsangayar da yake representing hadi da matakin ilminsa. Tattaunawa suke a kan sabuwar tsangayar da za su fitar cikin faculty of medicine na jami’ar ta 'Reading' wanda a baya babu shi a jadawalin koyarwar jami’ar, wato Ophthalmology Department (tsangayar karatu a kan likitancin ido), sun kuma cimma matsaya guda a karshen tattaunawar tasu.
A lokacin da suka rufe tattaunawar kowa ya mike ne don barin dakin taron abun ya faru kamar yadda ya saba faruwa da shi lokaci zuwa lokaci. Yana mikewa kansa ya sara, mummunar sarawa, jiri ya debe shi, gumi ya lullube shi. Daga nan kuma bai san abin da ya sake faruwa ba, sai farkawa ya yi ya samu kansa a gadon asibiti.
A gefensa babban amininsa ne, wanda suka fito kasa daya, wato Abdul’Ahad Maikano zaune a daidai saitin kansa ya kura masa ido. Ruwan da aka makala masa a jijiyar hannunsa ya bi da kallo kamar mai kirga saukar kowanne digo na ruwan zuwa cikin jikinsa. Amma a zahiri ba ruwan yake kallo ba, innocent and naïve fuskarta ce ta ke gilma masa. Wani mummunan scene da ya kasa bace masa, a rana ta karshe da ya tsallake ya barta, bayan ya karbe mata alfarmarta cikin wani yanayi da duk mai imani ba zai yi irinsa ba. Muryar ta ce ke yi masa amsa-kuwwa cikin roko, tana rokonsa da ya tausaya mata, al’amarin da ba shi da maraba da rape ban da igiyar aure da ta lullube shi.
Tun daga ranar kuma, har izuwa inda yau ke motsi, bai zauna lafiya da zuciyar sa ba, bai samu farin cikin da yake hasashen samu in ya guje ta ba. Ya samu cikar kowanne cikin burikan sa, amma ya kasa samun kwanciyar hankali, zuciyar sa kuma ba ta huta ba. Wani irin maganadisu ne ke jan zuciyar tasa zuwa gare ta...., da wani irin extraordinary feeling mai wuyar fassarawa.
Feeling din da har gobe bai san ma'anar sa ba, bai gaya wa wani ba, balle ya samu fassarar sa.
Ya san dai daga ranar zuciyar sa ba ta kara hutawa ba. Ruhin sa bai bar azabtuwa ba da tunanin ta. Girman laifin da ya san ya aikata mata kuma, daga ita har iyayen sa, ya hana shi samun karfin gwiwar komawa gida ya fuskanci iyayen sa. Sannan tunaninta ya ci gaba da yi masa dabaibayi irin wanda ya hana shi jin dadin komai.
Ga dai ilmin da ya fito nema ya samu yadda ya kamata, wanda a take bayan kammalawar sa jami’ar ta dauke shi aiki a Teaching Hospital dinta amma duk da wannan achievements din, ya kasa samun farin cikin da ya kamata ya samu. Ya kuma kasa samun contentment din da ya kamata mai nasarar rayuwa irin sa ya samu.
Girman laifinsa ga iyayensa da kullum yake hangowa, ya hana shi zama lafiya yaji dadin nasarorin nasa; sun yi masa gatan da yake ganin takurawa ne a gare shi, ya bula musu kasa a ido ta hanyar kin komawa garesu, tare da kin waiwayar wadda ta kasance a karkashin alfarmarsa. Ga shi sakamakon hakan yawan tunani da damuwa ya haifar masa da ciwon kai na barin kai guda (migraine) wanda a duk lokacin da ya tasar masa, sai ya fidda shi daga hayyacinsa, kuma sai ya sha drip a asibiti.
“Are you okay Man?”
Abdul’Ahad ya tambaye shi.
Lumshe idanunsa ya yi daga kan ruwan da ya daura su ya kasa daukewa. Abdul’Ahad ya kama hannunsa na hagu wanda babu ruwan a jiki.
“You better be careful da lafiyarka Aboki (sunan da yake kiransa), Dr. Andrew ya ce kana tsanantawa kwakwalwarka tunani ne, shine silar migraine din ka, as a medical doctor ba sai an tsaya gaya maka illolin hakan ga lafiyarka ba. Har gobe ba ka dauke ni yadda na dauke ka ba Aboki, ba sai ka yi haka zan san ba ka yarda da ni ba. Sannan ban kai matsayin da zan zamo amini a gareka ba.
Ka ki gaya min damuwar ka ta shekara da shekaru. Tunda muka zo a haka nake ganin a. Ni ba abin da ba ka sani a kaina da iyayena ba, amma har gobe ban san komai a kanka ba. A kalla in ka gaya min damuwarka ko ban yi maka maganinta ba, zan ba ka shawara, shawara wadda in ka bi ta za ka samu sassaucin damuwarka. Na yi-na yi ka hada ni da mahaifanka ko sau daya ne mu gaisa a waya tsayin shekarun nan Aboki, ka ki yin hakan. Kullum da uzrin da zaka bani. Har yau ba ka yarda da ni ba ne, ko kuwa ba ka ba ni matsayin aboki na gaske ba?”
ABUBAKAR (TURAKI) ya sake lumshe kyawawan idanunsa. Duk inda ake neman aboki na gari, to Abdul’Ahad ne. Ya rungume shi kamar dan uwansa na jini tun zuwansu garin (Reading Barkshire). Ba wai bai amince masa ba ne, kawai bai taba sharing al’amuran rayuwarsa da kowa ba, sannan ya sani shi mai laifi ne ga iyaye abin tinkahon kowanne dan Adam, watakila har wajen Ubangijinsa! Ba ya so Abdul’Ahad ya bar ganin mutuncin sa.
“Okey, tunda hakan ka zaba wa kanka, da yardar Allah ba zan sake tambayarka komai a kan rayuwarka ba. Abin da nake so kawai shi ne, ka kula da lafiyarka, ka kare ta daga cututtukan zamani wadanda ba mu da maganinsu. Aboki, me ce ce rayuwa? Komai da ke cikinta mai wucewa ne, idan har mun dauke shi da sauki”.
Daidai lokacin likita Andrew ya shigo dakin. Ruwan ya cire masa, ya ce suna iya tafiya yanzu, amma yana kara jan hankalin Dr. Aboubacar da babbar murya ya raba kansa da damuwa da tunani.
Abdul’Ahad ke tuka su cikin motar Aboubakar Turaki kirar Acura. Suna tafe a kan titin da zai sada su da gidan Abubakar-Turaki da ke cikin jerin gidajen malaman jami’ar 'Reading'. Turaki ya rasa me ya sa yau zuciyarsa ke neman wanda za ta raba dimbin damuwar nan da ke nukurkusarshi da shi ko da kadan ne? At least ya samu sassaucin damuwar nan in yayi voicing dinta ga wani, someone caring like Abdul Ahad. Yana gefen Abdul’ahad yayin da Abdul’Ahad din ke tuki cikin nutsuwa, bakinsa ya motsa kadan ya fadi abin da bai ta furtawa ba tsayin shekarun da suka yi tare.
“I am married Aboki”.
Ya fada daga can kasan makoshin sa.