Sashe 21
Kulsum Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ji komai a jikin ki ba na alamun zazzabi, ina yake miki ciwo?” Da sauri ta ce, “Ido na”. Don dai ta samu ya kyaleta. Ya ce, “Then let us go ki ga ophthalmologist”. Ta katse shi da hanzari, “Ba fa ciwon yau ba ne, tunda na taso da shi na taso”. “Kuma ba ki taba ganin likita a kai ba? this is silly, ki wuce mu je kawai”. Za ta yi musu ya dora yatsansa a kan labbansa, tare da jan hannunta suka bar dakin. A haka suka tadda Nasmah da Mujaheed a falo, wadanda ke zaune suna shan coffee. Su duka biyun suka dago ido suna kallonsu, Nasmah ta ce, “Lafiya?” Ya ce, “Mujaheed ya maida ke gida, zan kai Kulsum ta ga likitan ido”. Ta ce, “Haka ake zuwa ganin likitan afujajan ba shiri ba appointment?” Ni dai gaskiya kada ka hada ni da Aunty Sakeenah". Ya harare ta yace, “European Hospital zan kai ta, sabon asibitin ido ne, na hadin gwiwar European Union (EU), ko yaushe ka je za ka ga likita”. Kulsum wadda duk rawar jikin da yake a kanta ya daina burge ta, kwarjininsa ya zube daga idanunta, ta ce, “Don Allah Ya Taufeeq ka barmu mu tafi gida, ma je asibitin daga baya, idan Aunty Sakeenah ta dawo ta ga ba ma nan za ta yi mana fada”. Ya ce, “To hell with Aunty Sakeenah, kina zaune da ciwon ido shekara da shekaru ba ki taba ganin likita a kai ba ki ce wata Sakeenah? Wuce mu je kada ki bata min rai”. Nasmah ta ce, “Ni dai ka san yadda za ka yi ka fidda ni wajen Aunty, sai kun dawo”. Har ya tada motar suka hau titi Kulsum hawaye ta ke yi, hawayen da ya danganta da ciwon idon nata, ko on fadan da yayi mata. Da kuma rakin ta, haka ta ke da raki kamar kankanuwar yarinya, abin kuka ba ya mata wuya. Kulsum ta daga kai ta dubi tankareren asibitin da Taufeeq ya kawo ta. European Specialist Eye Hospital. Ya samu wuri ya yi parking ya bude mata kofa. Tare da cewa, “Mu je ciki, ko sai na dauke ki ne?” Ba ta ce masa komai ba, don yanzu komai nasa ya daina burgeta, ta sa kafa ta fito. Tana zaune ya je ya yanki kati ya yi komai ya dawo. Aka nuna musu ofishin da za su ga likita. Mutum biyu ne a gabansu, daya na ciki bai fito ba, daya na kan layi daga waje. Suka zauna, Taufeeq ya ce da ita, “Ba sa bata lokaci su, kana zuwa za'a duba ka, sunada kwararrun likitocin ido, duk Nigeria babu kamarsu a fannin ido, don haka ne tsadarsa ba ta dada ni da kasa ba”. Ita dai jinsa kawai ta ke yana kara sire mata. Abun ba kama! Wai Taufeeq mashayin giya. Allah Sarki Hajiya! Ko ya ya za ta ji duk ranar da ta samu wannan bakin labarin? Tana alfahari da ‘ya’yanta, tana bugun kirji da tarbiyyar da ta ba su. Kullum burinta shi ne su zame mata ‘ya’ya na gari. Musamman Taufeeq da yake namiji tilo shi kadai da Allah ya ba su. Daddy na son Taufeeq yadda harshe ba zai iya bayyanawa ba! Ya ya za su ji idan ta zo gabansu ta ce ta fasa auren Taufeeq, saboda giya yake sha, ana saura kwana hudu daurin aurensu? In kuma suka karyata ta fa? Suka ce sharri ta yi wa dan su? Anya za ta iya yi wa Hajiya Nasara wannan sakayyar ta fasa auren Taufeeq kwanaki kadan gabanin aurensu? Duk wani shiri na duniya sun gama shi, har kayan aure su suka yi mata, da wane bakin za ta zo ta ce ta fasa auren Taufeeq a yarda da hujjar ta? To amma haka za ta bari tana ji tana gani a aura mata mashayin giya ya zama uban ‘ya’yanta? Tana wannan tunanin mai matukar soya zuciya mutumin da suka tarar ya fito daga ofishin likita, Taufeeq ya wuce gaba ta bi shi a baya. A jikin kofar ofishin an rubuta (Consultant Ophthalmology), ta bi bayan Taufeeq cikin mutuwar jiki da ta zuciya suka shiga. Sanyin Iya kwandishan ne ya fara bugun jikkunan su. Kulsum ta kai dubanta ga mamallakin ofishin wanda ke zaune cikin kujerar sa mai juyawa dama zuwa hagu, ya baiwa kofar shigowa baya, idon sa na kan file din ta. Sanye cikin grey-black Italian suit. Gabadaya ya juyo da kujerar sa ya fuskance su, amma idon sa na kan file din gaban sa. Ko mutuwa ta yi ta dawo ba za ta kasa gane TURAKI ba, Turakin ta .... Her Ex-Turaki, kowanne irin canjin rayuwa ya samu kuwa, sai dai ya tara suma a kansa wadda a baya ba shi da ita, ta kwanta luf a kansa sai sheki ta ke ta fulanin Gaya. A jikin dan karfen da ke kan teburin sa cikakken sunan sa ne cikin ruwan gold, DR. ABUBAKAR TURAKI ABDULLAHI GAYA..... ta wani irin zuki numfashi ta fesar. A hankali ta soma maida kafafunta baya don barin ofishin. Cikin tsananin taka-tsan-tsan na kada takunta ya bada sauti. Abubuwa da yawa da suka gabata na gilmawa a idanun ta.... Alaqar da ke tsakaninsu, wata irin alaqa ce ba mai kankaruwa daga zuciya ba!!! Saura taku biyu ya rage mata ta fice ya dago kansa gaba-gadi don ganin masu shigowa… Bayyanannen canjin da ta samu cikin shekaru takwas da doriyar watanni bai hana shi gane ta farat daya ba, kamar yadda itama nashi canjin da nauyin shekarun da suka hau kansa, suka bashi suffar cikakken mutum wanda ke cikin ganiyar cin ilmin sa, ya kuma san ciwon kansa a halin yanzu, bai hanata gane shi ba. Ya kafe ta da idanunsa ta cikin farin gilashin da ke manne a idon sa,... idanun nan na Turaki da ke zuwa mata kullum cikin mafarki, ko a ido biyu... A lokacin da ita kuma ta bude kofa ta fice da dan banzan sauri… har tana tuntube, saura kadan ta fadi!