← Book details Kulsum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 22

Sashe 13

Kulsum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A rayuwar Taufeeq Muhammad Bello, bai taba haduwa da abin da ya tsaya masa a rai irin Kulsumu ba. Kulsumun da ba ta san yana yi ba, karatunta ta dumfara with much enthusiasm. Karatun kadai ta sa a gaba, shi ne goal dinta, ko ta so ta yi tunanin Turaki tana yakice shi ne da dukkan karfinta.
Hajiya Nasara ta cika alkawarin da ta daukar wa Kulsum, ta aika wa Malam Hadi waya, don haka Kulsum ta zamo ba ta da damuwa, kullum tana tare da iyayenta da kakanninta a waya, in ta dawo gida. Ga Nasmah da Aunty Sakeenah su ma suna kiranta akai-akai.
Sati uku da tafiyar Taufeeq sai ga shi ya dawo ba zato ba tsammani. Hajiya ta ganshi at a smart pace (afujajan), gabadaya ya zama tamkar ba shi ba. Duk ya birkice ba nutsuwa sam a tare da shi. Da Hajiya ta nemi ba’asin dawowarshi ba lokacin da ya kamata ya dawo ba, sai ya ce lafiya kalau. Ba ta kara maida hankalinta ta kanshi ba, sai ta sa Serah ta shirya masa vegetarian meal dinsa, lokacin Kulsum na makaranta.
Taufeeq ya samu Daddy dinsa a falonsa yana shan gahwah, ya shigo falon ya samu wuri gefen Daddyn ya zauna, Alhaji Muhammad Bello ya dubi dan nasa cike da kulawa ya ce, “Ya aka yi ne Taufeeq? Na ganka ba'a yadda na saba ganinka ba, is anything wrong a wajen aikin?”
Taufeeq ya sunkuyar da kansa yana tauna kalaman da zai furta wa mahaifinsa. Daddy bai katse hanzarinsa ba har sai da ya mula don kansa ya yi magana.
“Daddy aure nake so!”
Daddy ya hadiye mamakinsa ta hanyar murmushi, kafin ya ce, “Ka samu matar ne?”
Taufeeq ya kara yin kasa da kai, ya ce, “Daddy, Kulsum nake so, ka roka min Hajiya ta ba ni aurenta. Na yi alkawarin zan barta ta ci gaba da karatu har sai ta ce ya ishe ta, aurena ba zai zama barrier ga neman iliminta ba, insha Allahu.
Ka yi min alfarma Daddy ka roka min Hajiya, in ni na yi mata magana ba za ta amince ba”.
Daddy ya gyada kai, ya ce, “Wai yarinyar nan da ta dauko a Gaya?”
Taufeeq ya ce, “Ita Daddy”.
Alhaji Muhammad Bello ya ce, “Da kyau, na yaba da hankalin yarinyar, ga ta ‘yar uwarka. Ka bar komai a hannuna in dai yarinyar ta amince Hajiyarku za ta fi kowa son al’amarin”.
Amma ko da Daddyn ya furta zancen ga Hajiya Nasara, budar bakinta sai cewa ta yi.
“Ba zai yiwu ba. Na dauko Kulsum don ta yi karatu ne ba don in aura wa dan cikina ita ba. In auren yake so ya nemo wata, amma ban da Kulsum, iyayenta sai su zarge ni da son kai. Don yanzu haka tsohon mijinta ma na ta bilinbituwar nemanta da kome, ni na ce kada a gaya masa inda ta ke, don dai mu samu ta yi karatun nan. Sai kawai yanzu in je in ce musu Dana zai aure ta ko shekarar farko ba ta rufa a karatunta ba?”
Daddy ya dan tsura wa matar tasa ido, kafin cikin sanyin murya ya ce.
“Can we wait for her?”
Murmushi ta yi sabida yadda ya yi maganar cikin lallashi.
Ta ce, “Za ku iya jira har ta kare Nursing School sai ku shiga jerin manema, in Allah ya sa ku ne da rabo sai ku samu, in kuma mijin ta ke da nasara sai kuyi hakuri”.
Murmushi mai sauti Alhaji Muhammad Bello ya yi, kafin ya ce, “Alright. Insha Allah mu ne da rabon. Zan lallashi Taufeeq ko zai fahimce ki, don a yadda na fahimta soyayya mai zafi ce ta kama shi. Ki duba kunya da kawaici irin na Taufeeq, amma ya fito fili ya ce min aure yake so. Ta nan za ki fahimci ba da wasa yake ba. Amma muna neman alfarmar ki barsu su fara fahimtar juna kafin ta gama karatun ko don ya samu nutsuwa”.
A nan ma Hajiya Nasara ta ce ba ta yarda ba, zai kasa wa Kulsum hankali, karatu za ta yi ko soyayya? Ya kyale ta kawai ta yi abin da ke gabanta ya nemo wata ya aura.
Daddy ya ce, “Nasara ki fahimta, Taufeeq ba aure yake so ba, yarinyar wajenki yake so. Ki zama mai tausayi mana? Kuma zan ja masa kunne ba ko yaushe zai dameta ba. Don Allah ki yi mana alfarma”.
Hajiya Nasara ta san yadda Alhaji Muhammad Bello ke son Taufeeq fiye da kowa cikin ‘ya’yansa ba lallashin da ba zai mata ba. Sai ta ce a ranta za ta gwada Taufeeq don ta fahimci ko wane irin so yake yi wa Kulsum. Ta ce da Daddy za ta yi magana da Taufeq din kafin ta amince ya soma kula Kulsum.
Da daddare bayan sun gama cin abincin dare su uku, ita, daddy da Taufeeq, Kulsum na daki ta ki fitowa. Hajiya ta lura tun zuwan Taufeeq ta koma daddawar daka, ko falo ba ta zama. Ita Kulsum a kan-karan-kanta ta rasa me ya sa ta ke jin nauyin Taufeeq? Idanuwansa ne manyan (magnet) din da ke takura zuciyar ta. Yana da wasu irin idanuwa tamkar maganadisu masu jan zuciyar diya mace, tamkar jan wutar lantarki. They makes her feel unease, shi ya sa ta zabi kebe kanta muddin yana wuri.
Hajiya ta dube shi bayan Daddy ya tashi ya koma tsakiyar kujerun kayataccen falon ya murdo tashar CNN ya kure sautin yana sauraron labarai. Ta dago ido ta dubi dan ta Taufeeq, a tsanake ta kalle shi na ‘yan sakanni, kafin ta ce.
“Na ji sakon ka wajen mahaifinka, amma ko ka san Kulsum na da lalura? Dalilin da ya sa na dauko ta ma ke nan bayan karatu, za ka iya aurenta a haka?”
Taufeeq ya daga kyawawan idanunsa ya dubi mahaifiyarsa, a tsanake ya ce, “Wace irin lalura ce Mum?”
Hajiya Nasara ta dube shi, tana son fahimtar yanayinsa, ta ce, “Fitsarin kwance ta ke yi, tunda aka haife ta”.
Taufeeq ya zuqi numfashi ya fesar, (a bit confused) ya ce, “Fitsarin kwance as in tana barci ta yi fitsari cikin barci?”
Hajiya ta ce, “Shi fa”.
Ya yi dan jimm! Kafin ya ce, “Mum, ai ni ita kawai nake so, bana jin hakan zai hana ni aurenta, zan kuma nema mata magani har Allah ya sa mu dace. Idan kuma ba ta warke ba zan zauna da ita a haka, to the very end. Ni dai ki yi min alfarma ki ba ni aurenta”.
Jikin Hajiya Nasara ya yi mugun sanyi, domin ba amsar da ta tsammata daga gare shi ba ce. Danta ko cikin ‘yan gayun samari ajin farko ne. Ko cikin masu tashen ilimi shi Navy Officer ne (sojan ruwa). Bai taba ce mata ga yarinyar da yake so ba a tsayin shekarunsa talatin da uku da haihuwa. Ya tsallake duk ‘yammata a UK ya zo ya ce ‘yar qauyen Gaya yake so, kuma mai lalurar fitsarin kwance. And he is willing to stay with her cikin lalurar tata ba tare da ta warke ba. Don haka ta yarda ciki al’amarinsa gaskiya ce ziryan.
Amma ita wane bayani za ta iya yi wa iyayen Kulsum ba tare da sun zarge ta da son kai ba? Ga maganar tsohon mijinta da ke bibiyar nemanta har gobe, kuma ta sani su Goggo na son zancen sa, don dai sun bi abin da ta ce din ne kawai don sun san ta yi ne don amfanin Kulsumu. Yanzu kuma ta je ta ce musu Dan cikinta zai auri Kulsumu ai ba ta da hujjar kare kanta daga zargin su na kasancewa mai son kai.
Kwarai za ta so Kulsumu ta zamo suruka a gare ta domin a dan zaman da ta yi da ita ta gama yarda da kyawawan halayen ta. Sannan ta shiga ranta yadda ba a zato. Abin farin cikinta ne Taufeeq ya aure ta, to amma ba dai yanzu ba!
Ta yi ajiyar zuciya ta daga kai ta dubi Taufeeq din, ta ce, “Ka yi hakuri mu bi lamarin nan a sannu, babu bukatar gaggawa a cikin sa. Ka bai wa Kulsum lokaci. Aure ko soyayya ba nata ba ne yanzu. Ka bar wa Allah lamarin ka yi addu’a. Allah ya tabbatar da alkhairi a tsakanin ku”.
Taufeeq ya ce, “Na ji abin da ki ka ce Mum, sannan na fahinta, amma don Allah ki bar ni in nemi yardar ta a hankali. Na yi alkawarin ba zan hana ta karatu ba”.
Hajiya Nasara ta ce, “To Taufeeq na amince, sannan Kulsum amana ce a hannun mu, na rabo ta da iyayen ta ba don ba su da yadda za su yi da ita ba, ko don sun gaza a kanta, a’ah, sun ba ni ita ne sabida yarda da suka yi da ni. Don haka sai ka san irin mu’amalar da za ta kasance a tsakaninku. Wadda ba za ta zamo ta Allah wadai ba”.

Taufeeq ya kwanta a kan gadonsa a wannan daren, ya lumshe idanunsa yana tunano maganganun da suka yi da mahaifiyar sa a ranar a kan Kulsum. Maimakon abin da ya ji na lalurar fitsarin kwance ya sagar da gwiwarsa a kan Kulsum, sai ya ji his feelings for her heightened.
Da ma har yanzu akwai masu irin wannan lalurar a duniya? Ina ma shi likita ne? Likitan ma wanda ya yi specializing a kan lalurar Kulsum. To ko dalilin da ya sa Mum din sa ta kai ta wajen Sakeenah ke nan? Allah Sarki Kulsum! Ubangijin halitta ya kyautata halittar ta da halayyar ta ta kowanne bangare, amma sai ya jarrabce ta ta wannan bangaren. Fitsarin kwance nakasa ne ba kadan ba, musamman ga diya mace. To ko wannan ne dalilin da ya sa mijin nata ya guje ta? Shi ji ya yi hakan ya kara sanya masa son ta da tausayin ta.
Chapter 13 · 0% Book details