← Book details Kulsum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 22

Sashe 7

Kulsum Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“What?" Maikano ya tambaya kamar bai ji daidai ba.
“Aure ka ce ko me?”
“Aure aboki, I’ve a wife at home (inada mata a gida), ina cikin tasku, domin na yi wa iyayena laifi, na kasa zuwa in ba su hakuri don ban san da kalamin da zan wanke kaina ba.
Na yi musu babban laifi, na kin waiwayar su all these while a kan bana son auren da suka yi min. Tun bayan na taho kuma tunanin yarinyar ya kasa barina, sabida ita ma na yi mata wani babban laifi. I lack the courage na fuskantarsu su duka ukun, in ce su yafe min”.
A wannan lokacin ya kwashe labarin sa kaf ya gayawa Abdul Ahad, garin su, inda ya fito da matsayin mahaifin sa.
Cikin mamaki Abdul’Ahad ya ce, “Kana nufin tun tahowar ka ba ka kara waiwayar gida ba?”
Cikin jin nauyin abin da ya aikata ya ce, “Duk halin da suke ciki na sani. Wani abokina a garin mu yana gaya min, na san lafiyar su kalau. Ina bibiyar lafiyar su. Da farko ina kira, daga baya ne na daina, ba don komai ba sai don kada su takura min in dawo wajen matar da suka aura min. I thought I don’t like her anymore Aboki, saboda tana da lalura... I thought I escaped, auren da bana son, amma tunaninta ya hana ni sakat a duka shekarun nan, something like infatuation… emotional disturbance.... I just..... cannot express…, kawai ji nake zan iya zama da ita da lalurar tata against all odds”.
Abdul’Ahad ya yi wani mischevous murmushi ya ce, “Man, ka dawo hanya kawai, tell me you love your wife right now (kana son matar ka yanzu), shawarar da zan baka itace ka koma gida ka taho da ita, ka kuma nemi afuwar iyayenka bisa kaurace musun da kayi alhalin su da alheri suke nufin ka, in ba haka ba, ba za ka taba zama lafiya ba na gaya maka, kuma ba za ka ga albarka cikin rayuwar ka ba. Babu iyayen da suka san ciwon kansu da zasu so dan su ya tafi Turai ba aure. Da ka kwantar da hankalin ka da ka fahimci manufarsu tuntuni. Ba sun yi ne don su takura maka ba. Shawarar da zan baka ke nan, ka je gida, ka karbi duk wani punishment daga gare su, sannan ka dauko matarka!”.
“Kana ganin za su yafe min Aboki? UmmuKulsum za ta kara kallona da kima bayan duka laifuffukan da na yi mata? Ban taba kallon ta da matsayin mata ba! Aboki har raping dinta na yi don kawai in nuna rashin kaunata gare ta. This is the worst moment da nake tunawa a kanta, kuma abin da ya canza zuciyata zuwa alkhairi bakidaya a kanta.
Ba ta cancanci duk abubuwan nuna rashin kauna da na yi mata ba tunda ba ita ta zo ta ce tana sona ba, iyayena ne suka je suka nemo min aurenta har gaban iyayenta kamar yadda ake neman auren kowacce diya ta mutunci. Ban kyauta ba Aboki, watakila Ubangiji ke hukunta ni da feelings a kan UmmuKulsum, wadanda ke kassara ni a yanzu, suka kuma hana ni jin dadin kowacce nasara da ta same ni”.
Abdul’Ahad ya ce cikin tausayawa, “Don’t ever say you raped her again, tunda igiyar aure ta hada ku. Matarka ce. Sai dai ka ce, ...not in a nice way...! Mace kuma mai rauni ce a halittar ta, ban hakuri, kulawa da nuna soyayya tareda nuna ka amshi laifin ka kadai zai wanke laifinka komai girman sa.
Iyaye kuwa tsakaninmu da su akwai afuwa, yafiya da jin kai, wanda Ubangiji Subhana ya sanya a tsakaninmu da su.
Ka je gida ka kwantar da kai, ka amshi kowanne laifinka. Ka karbi punishement komai tsaurin sa. Sannan ka ba su hakuri, ka dauko matarka kusa da kai ina tabbatar maka hakan kawai za ka yi ka wanke kanka a wajensu, kuma ka samu nutsuwa da zaman lafiyar cigaba da gudanar da al'amuran rayuwar ka”.
Turaki ya yi na’am da shawarar amininsa, cikin satin gabadaya ya maida hankali wajen shirin dawowa kasar haihuwarsa, soyayyar da bai san cewa ita ce ke nukurkusar sa ba tana kara masa azama ga son dawowa gida, da burin ya dora ido a kan KULSUMU.

*** *** ***

GAYA
Batulu na markada abarba cikin blander a kicin din Umma, yayin da Umma ke turara alkubus a kan wuta, ga dukkan alama ita ce da turakar Maimartaba yau. Don girkinshi matansa ne kadai ke yi mishi da hannunsu. Suka jiyo hayaniya daga tsakar gida, wani suna yana tashi daga bakin jama’ar gida, kamar TURAKI!
Umma tayi sak! Daga abinda take yi, ba ta gaskata kunnuwanta ba don haka ta mike ta leka tsakar gidan ta tagar kicin. Ba ta yi nasarar hango wanda jama’ar gidan suka yanyame ba, amma tabbas ta ji suna fadin, "Turaki", komawa ta yi ta zauna ta ci gaba da turara alkubus dinta, amma hankalinta ya rabu biyu. Batulu ta kashe blander ta ce, “Umma kina jin me ake fadi kuwa? Kamar Yaya Turaki na ji suna cewa…”.
Kafin Batulu ra rufe bakin ta Umma kuma ta samu zarafin amsa mata, kamshin turaren Turaki (one man show) ya ziyarci hancin su, daga nan kuma sai sallamarsa, cikin muryar nan tasa mai cike da haiba da ginshiran sarauta, kafin ingarma kuma kyakkyawa Abubakar (Turaki) ya sako kai ta hanyar rage tsawon sa a kofar kitchen din Umman sa.
Sanye yake da kaftan na wata lallausar farar shadda (filtex), hular kansa ruwan kasa ce mai haske, haka fatar agogon hannunsa samfurin RADO itama ruwan kasar ce, a kafarsa budadden takalmin fata ne dan kasar Italy. Kallo daya Umma ta yi masa ta dauke kanta, amma sai da zuciyarta ta buga sosai da sßganinsa.
Ban da uwa-uwa ce da ba za ta yarda Turaki ne ba, domin gabadaya ya canza ya zama wani gogaggen matashi, wheather din kasar England ya amshe shi ba kadan ba. Ya kara kyau da ilhama, ga wani lallausan saje da ya tara a gefen fuskarsa wanda a da ba shi da shi. Batulu ta hangame baki sannan ta sheka da gudu ta rungume shi tana fadin.

“Yaya Turaki kai ne? Ashe za mu sake ganinka?”

Shi ma ya rike ta a jikinsa yana fadin, “Autar Umma kin kara girma, me Umma ke ba ki hakan?”
Dariya ta yi tare da riko hannuwansa duk biyu kamar ta hadiye shi don farin ciki, sai fargawa suka yi babu Umma a kicin din babu alamarta.
Shi da Batulu suka bi bayanta zuwa dakinta, zaune suka same ta a gefen gadonta ta kifa fuska cikin tafukanta tana share hawaye. Jikin Turaki ya kara yin la’asar, fiye da wanda yazo a cikin sa, a kan gwiwoyinsa ya tsugunna a gabanta.
“Umma na san ni Abubakar Turaki mai laifi ne, mai tarin laifuffuka a gare ku, Umma duk laifin da ku ke zargina da shi na karba, kuma na san na yi. Amma don Allah Umma ku ba ni dama in gyara kuskurena. Don Allah Ummah. Ajizanci ne irin na dan adam.
Umma cikin tarin alfarmomin ki na uwa, wadanda ba za su taba karewa a gare mu ba nake rokon ki da ki yafe mini, na tabbata na yi muku laifi wanda in ba ku yafe min ba ba zan taba zama cikin kwanciyar hankali ba. Na kwashe shekaru ban zo na gan ku ba, ban nemeku a waya ba, ban ji lafiyar matar da kuka zaba min ba wanda ba akan haka muka rabu ni da ku ba. Mun rabu ne akan duk shekara zan zo, kuma zan dinga kiran waya.
Ummah a yau gani a gaban ku, durkushe akan gwiwoyi na, na zo in tabbatar muku na karbi zabin da ku ka yi min da hannu bibbiyu. Ki taya ni ba ta hakuri. Ba zan kara maimaita kuskure na ba”.

Umma dai ba ta ce komai ba, amma kalamansa sun shigeta, yana ta magiyar sa, ita kuma tana aikin share hawaye.
Wuni guda ya yi cur yana bin Umma da neman gafarar ta, amma uffan ta ki ce masa komai, Batulu kadai ke kula da al’amarinsa. Ita ma in ta tuna babu Kulsumu a gidan duk sai ta ji wani irin haushin sa ya rufe ta. A haka dai ta yi masa girki mai kyau, ta kuma shigar masa da kayansa sashen sa. Bayan ta sa an share an goge ko'ina.
Yana so ya tambayi Batulu Kulsumu, ya rasa ta ina zai fara. Sabida yadda take sha masa kamshi. Kwarai hankalinsa ya dugunzuma ya tashi da ya fahimci babu ita a sashen nasa, babu komai nata, kai da alama ma an dade ba a yi amfani da sashen nasu ba. Amma ya kasa tambaya. Saboda fargabar abinda za'a gaya masa.

Bai samu ganin Maimartaba ba sai washegari da safe yana kalaci. Mai girki wato Hajiya Saratu ta yi masa iso turakar mahaifinsa.
Maimartaba ya amsa gaisuwar sa kadaran-kadahan, amma daga gaisuwar bai kara ce masa komai ba. Hankalinsa ya kara yin kololuwar tashi. Ya gurfana gaban Maimartaba yana ba shi hakuri tare da jaddada cewa ya amince ya karbi dukkan laifuffukansa. Ya karbi zabin su da hannu bibbiyu.
An dauki lokaci kafin Maimartaba Sarki ya ce da shi.

“Mu kam ai mu za mu ba ka hakuri Turaki, tunda mun takura rayuwarka ba da sanin mu ba. Har dalilin hakan ka zabi ka kaurace mana a wannan lokaci na tsufa da muka fi bukatar kulawarku da komai.
Ka kwantar da hankalinka, kuma ka daina gudun mu in dai a kan yarinya Kulsumu ne, tuni mun maida wa iyayenta ‘yar su, bayan mun sa Alkali ya raba auren bisa doron shari’ah”.
Chapter 7 · 0% Book details