← Book details Kulsum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 22

Sashe 19

Kulsum Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Amma me? Wadda ta bude kofar a lokacin da ya danna door bell bai yi tsammanin ganinta a garin Lagos ba. Baki ya bude sakaka! Yana kallonta. Murmushi ta yi ta ba shi hanya ya wuce, yana fadin.
“So this is the albishir, sorry Doctor, wannan har goron albishir zan ba ki ai. Kulsum in town, what a surprise!”
Sakeenah ta ce, “Rike goronka tunda ka gwale ni”.
Engnr. Farouq ya shigo falon, ya mike ya ba shi hannu, ita kuma Kulsum ta wuce dakinsu.
Nasma da ke taje dogon gashin kanta ta ce, “Kamar muryar Yaya Taufeeq nake ji a falo?”
Ta amsa mata da, “Shi ne”.
Nasmah ta ce, “To fa shi ke nan yanzu ba sauki, ga shi muna da wajen zuwa, gidan su wata course mate dina za mu je”.
Ya karaso har kofar dakin nasu, ya ce, “Kulsum, abin ma haka ne ko? Za ki zo amma jiya ba ki gaya min ba?”
Tana kawar da kai daga gare shi, ta ce, “Ni ma ban san da tafiyar da wuri ba, don da Aunty Nasmah ita kadai za ta zo”.
Nasmah ta ce, “Ba wani nan, ko sanda ku ke waya jiya ai kin dade da kulle jakar kayanki”.
Ya jinjina kai, ya ce, “Na gode Kulsum, na kwana da sanin ba ki damu da ni ba ai. Ni kadai nake bilinbituwa ta…”.
“Yanzu dai Ya Taufeeq ka dauke mu ka kai mu Lekki gidan su kawata Iftihal, sai ku yi soyayyar a hanya kada ku shiga lokaci na”. In ji Nasmah.
“O.K, ku fito ina jiranku”.
Bakar Abaya ta fiddo za ta dora a kan kayan jikinta, wadanda english wears ne ba masu kama jiki ba, cikin tsarabar da Nasmah ta kawo mata, amma sai Nasmah ta karbe. Wata dakakkiyar shadda dark pink wadda aka yi wa dinki Senegalese ta fiddo mata cikin dinkunan da Sakeenah ta yi mata, tana faman mitar, “Ban san yaushe za ki shigo gari ba Kulsum, kullum ana fiddo ki kina nokewa”.
Kwalliya sosai ta yi mata, sannan suka tadda Taufeeq a mota bayan sun yi wa Dr. Sakeenah sallama.
Suna tafiya zuwa Lekki, Taufeeq na tsokanarta.
“Ka ga amaryar Taufeeq M. Bello ta kashe kala”.
Ta sha kunu sosai sannan a shagwabe ta ce, “Wallahi Aunty Nasmah ce ta takura min na yi kwalliya”.
Ya ce, “Tana so ki burge Yayanta ne, kuma kin burge shin. Duk kin dusashe hasken sauran mata daga idanun sa”.
Ya daga wayarsa ya kashe ta da hoto. Ta yi narai-narai da ido sai hoton ya bada wata irin kala mai kyau.
Tarba ta musamman Iftihal kawar Nasmah ta yi musu. Ba su dade sosai ba sabida Taufeeq da ke damun Nasmah da waya. Sai da ta gwammace ba ta sa shi ya kawo su ba. Ta san arzikin Kulsum ta ci da har ya yarda ya kawo su din.
A hanyarsu ta komawa gida, shopping sosai ya tsaya ya yi wa Kulsum, Nasmah na taya shi zabe.
A kwanaki bakwai da suka yi a Lagos, kullum sai Taufeeq ya zo wajen Kulsum in ya taso daga aiki, a gidan yake cin abincin dare. Kullum kokarinsa Kulsum ta sake da shi, ta yarda za ta ba shi martanin soyayyar da yake yi mata, amma kullum jiya-i-yau, Turaki ya yi wa zuciyar Kulsum babbar illah, duk da ta cire shi a ranta, ba ta da hope a kansa, amma ba ta jin bayan shi za ta iya kara sanya wani Da namiji a zuciyar ta.
Sai dai tana martaba Taufeeq sabida mahaifiyarsa da ‘yan uwansa da ke rikonta bilhakki.
Ta dawo gida ranar lahadi, litinin ta koma makaranta. A can ta baro Nasmah wadda za ta kwana biyu kafin ta dawo.

*** *** ***

BAYAN SHEKARA HUDU
Kamar kiftawar ido, haka shekarun suka zo suka mirgina, abubuwa da yawa sun faru a cikinsu. A shekaru hudun Ummu Kulsum Abdulhadi Yalleman ta fiddo da HND in Nursing. An yi bikin Batulu shekaru biyu a baya, tana garin Kaduna tare da mijinta Abdulkadir ma’aikacin GT Bank, yaranta biyu mace da namiji twins.
Wannan ne lokacin da Hajiya Nasara ta deba wa Taufeeq na jiran Kulsumu, don haka zuwa yanzu kusan kowa nata ya san da zaman Taufeeq, ya je har Gaya da 'Yalleman ya gabatar da kansa. Yanzu burin kakanninta shi ne kawai ta yi aure. Amma Kulsumu kullum tausarsu ta ke yi kan su barta ta yi hidimar kasa, ta fara specialization dinta.
Daddyn su Taufeeq ne ya sa hannu aka barta yin hidimar kasa a Abuja, inda bayan camping suka tura ta National Hospital.
Shekara daya baya suka sha bikin Nasma da masoyinta Mujaheed dan abokin Daddynsu, Mujaheed ma’aikacin Shell Company ne, suna zaune garin Port-Hearcourt.
Kulsum Abdulhadi, cikakkiyar ma’aikaciyar jinya mai shekaru ashirin da hudu, a wannan lokacin komai nata ya kai ya kawo. Ta samu wayewar kai irin wadda zurfin ilimin boko ke sabbabawa mai shi. Wayewa mai tafe da rikon addini. Ta canza gabadaya daga Kulsumun Goggo zuwa Kulsum din Nasara. Ba abin da Goggo Shatu da mijinta za su ce wa Hajiya Nasara sai addu’ar alheri, domin ta zama bayan da ya goya marainiya Kulsum ta tsaya da kafafunta, ta cika burinta na zamowa mai amfani ga al’umma.
Zuwa wannan lokacin ko ta ki ko ta so, ta tsayar da Taufeeq a matsayin mijin da za ta aura, sabida dalilai masu yawa da ba za su kidayu ba. Muhimmi shi ne mahaifiyarsa, sannan ‘yan uwansa mata da suka ba ta kaunar ‘yan uwantaka irin ta 'yan uwa na ciki daya wadda ba ta taba samu a rayuwarta ba. Ta manta ita din marainiya ce. Turaki ya zama wani rufaffen kundi (littafi) wanda ba a bukatar a bude shi. Ya zama past, wani irin past da ba ta ko son tunawa, domin babu wanda ya taba barin tabo a zuciyar ta kamar sa. Ba ta taba hasaso future dinta da shi ba. He is her past and Taufeeq her present.
Chapter 19 · 0% Book details