← Book details Kulsum Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 22

Sashe 17

Kulsum Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

suka yi ido hudu da Taufeeq da ke shigowa, ba shiri ta rufe bakin sai kuma ta kware ta soma tari. Nasma ta juya don ganin abin da ya kwarar da ita, ta ga Taufeeq ne. Ya zuba hannayensa biyu a aljihunsa yadda ya saba ya zuba mata lumsassun idanunsa. Ta sake juyawa ta dubi Kulsum nan da nan ta fahimci akwai wani abu. “Ya Taufeeq, ice-cream zan ba ta fah, ta ganka ta kware”. “To me ye wani za ki ba ta ice-cream, ita jaririya ce?” Ya samu kujerar da ke kallon ta Kulsum ya zauna. Ai da sauri ta tashi ta yi daki, ya ce, “Tafi a hankali kada ki yi tuntube mana”. Nasmah ta ce, “Ai kawai ka goyata ka kai ta dakin”. Ta bi bayan Kulsum da gudu kada ya make ta. A washegari da zai koma Lagos ya samu Hajiya a daki ya gaya mata sun daidaita da Kulsum ta amince masa. Hajiya ta yi mamaki kwarai don ba ta zaci hakan zai zo da sauki ba, ta san Turaki Kulsum ke so, don an fi karfinta ne. Ba ta so ya kasance Kulsumu ta amince da Taufeeq ne albarkacin ta. Sannan ita a wannan lokacin ba ta shirya yi wa Kulsum aure ba. Ta kyale ne sabida Taufeeq bai iya sanya abu a ransa ba, idan ba hadin kan Kulsumun ya samu ba ba zai maida kai ga aikinsa ba. Ta nisa, ta ce, “Taufeeq na yi murna, amma kamar yadda na ce a baya ina so ka ba wa al’amarin nan lokaci. Ka yi hakuri har Kulsum ta kare makaranta, sannan ne za mu ba ta damar fidda miji, yanzu ba ta da nutsuwar da za ta zabi mijin aure, kuma ba auren ta ke son yi ba. Ina rokonka, ka ba ta lokaci”. Taufeeq ya nisa, “O.K Mum, zan bi abin da ki ka ce. Ki taya ni addu’a Allah ya sa in jure jiran, kuma Allah ya sa ina da rabon samun Kulsum a rayuwata”. Abin ki da Da da mahaifi, sosai ta ji zuciyarta ta tabu, ta ce, “Insha Allahu inda alkhairi Allah zai ba ka ita. Kuma ba ga waya ba? Ko ka tafi ko yaushe kana iya kiranta, sai dai bana son abin da zai hana ta maida kai a karatu don Allah”. Dan murmushi ya yi, ya ce, “Mum zan kiyaye, zan tafi gobe ki sa min albarka”. “Albarka kullum cikin sanya muku muke. Allah ya kara wa rayuwa albarka”. Kulsum da Nasma a dakin Nasman, ta tura mata akwati shake da kaya, ta ce duk tsarabar ta ce. Ta bude tana daga English wears din daya bayan daya ‘yan gidan Marks & Spencer, duka babu mai fidda tsiraici za ta iya zama gida da su. Tana daga su daya bayan daya tana yabawa. “Aunty Nasmah, duk ni kadai?” Nasmah ta yi murmushi, ta ce, “Sai a yi ta tsantsarawa Yayana kwalliya”. Rigar da ta daga ta sa ta rufe fuskarta. Nasmah ta yi dariya, ta ce, “Ai kallon ku nake kar, kun dauka ban gane ba ne ko? Sai ki yi hakuri Yayan nawa akwai fada, akwai rigima. Ban sani ba ko ni da Aunty Sakeenah kadai yake yi mawa? Ke kam ai lallaba ki zai yi na sani, tunda shi ne mai nema”. Kulsum ta shuri jakarta ta bar dakin Nasmah na fadin, “Sai fulako sai ka ce tashin Ruga”. Ko da Taufeeq ya koma duk dare sai ya kira ta, komai yake yi sai ya sanar da ita. Tun tana jin kunya har ta saki jikinta da shi. Ita ma takan fada masa me ta ke ciki a kan harkar karatunta. Hatta Aunty Sakeenah da ke Lagos ta san zancen Taufeeq da Kulsum. Kusan ta fi kowa farin ciki da al’amarin don dai ita haka nan ta ke matukar son Kulsum. Hajiya Nasara ta cika alkawarin da ta yi mata, kwanansu uku da yin hutu kawai rannan tana gyaran kayanta a closet dinta ta tsinkayi sallamar Goggo. Goggon da ke zuwa kullum cikin mafarkinta, Goggon da ta ke kewa, kewar da ba za ta misaltu ba. Sakin kayan hannunta ta yi ta buga wani uban tsalle ta rungume Goggo. “Yi min a hankali, tsohon kashi ne”. Goggo ke fadi. Da kyar ta bambaro ta daga jikinta, ta kalle ta ta sake kallonta cikin fulatanci ta ce, “Kulsumu am ondo (Kulsumu na ce wannan)?” Dariya ta yi, ta kama hannunta zuwa bakin gado, Goggo na fadin, “Halan wankan inji na sake fata Nasara ke yi miki?” Dariya sosai Kulsum ke yi, ta rasa inda za ta saka Goggo don murna. Ta zaunar da ita gefen gado, ta bude dan bedside fridge dinta ta dauko gorar fresh milk da ruwan sanyi na gora tana ta rawar jiki, ta ce, “Goggo wanne zan zuba miki?” Hajiya Nasara ta shigo, a bayanta Serah ce da tray din abinci. Ta ce da Goggo, “Ai yau kuma ba kanta tunda ga Goggo ta zo, ina jin ko runtsuwa Kulsum ba za ta yi ba”. Kulsum ta ce, “Kamar kin sani Hajiya, kwanan zaune za mu yi”. Hajiya Nasara ta ce, “To don Allah barta ta huta ta ci abinci, son samu ta watsa ruwa ma, sun sha hanya”. Nasmah ta shigo ta gaida Goggo, Goggo ta ce, “Ita ce auta ko?” Kulsum ta ce, “Goggo kada ki sa Aunty Nasmah ta kara shagwaba akan wadda ta ke yi, idan ta ji kina kiranta auta”. Dariya suka yi, Nasma ta ce, “Ni ce nake shagwaba ko? Zan gamu da ke ne. Goggo ki je ki watsa ruwa ki yi sallah, ki huta ki rabu da ita”. Goggo da Kulsum ba su samu kebewa ba sai da daddare, Kulsum ta dage a dakinta Goggo za ta kwana bayan already Hajiya Nasara ta gyara mata daki. Goggo ta sha labarin zamanta a Lagos gidan Dr. Sakeenah da hanyoyin da Dr. Sakeenah ta bi ta hana ta fitsarin kwance. Da kaita babban asibiti data yi ta ga kwararren likita. Ta ce tun daga lokacin har yau ban kara yi ba. Idan na ji fitsari ko cikin barci ne sai na ji kamar ana alerting dina har cikin kwakwalwata. Amma har yanzu likita bai dauke ni daga shan magani ba. Idan na tuna wahalar da ku ka yi ta sha ke da Baffa, sai in tausaya muku, ashe lalurar tawa ta asibiti ce”. Goggo ta ce, “Godiya ta tabbata ga Sarkin halitta, shi magani ai dama dace ne, ciwo kuma warakarsa lokaci ne. Kulsumu Allah ya kawo miji na gari tunda lafiya ta samu”. Ta rufe fuska da hannayenta tana fadin, “Kai Goggo, ni karatu nake yi. Kuma har yau likita bai ce na warke ba”. Ba ta gaya wa Goggo Taufeeq ya fito yana sonta ba, haka ita ma Goggo ba ta gaya mata dawowar Turaki ba da komenta da ya ke so. Sun yi shawara ita da Hajiya Nasara su bar zancen a tsakanin su kada a raba mata hankali. Ita kuma Kulsumu kunya ce ta hana ta gaya wa Goggo zancen Taufeeq da kuma kasancewar har yau zuciyarta ba ta bai wa soyayyar Taufeeq kwakkwaran matsugunni ba. Ta fi kallonsa a wanda ya fi karfinta, dan gata, amma mutum mai tsananin kirki. Washegari Nasma ta ce za su kai Goggo ta ga gari ta mike kafa. Kowaccensu ta sha kwalliya, amma ko daga nesa ka san Nasmah ta fi Kulsum aji nesa ba kusa ba. Yayin da Kulsum ta fi Nasma kyau mai fizgar hankali. Nutsuwarta na kara wa kyawun nata ado, yana bayyana kwarjininta. Nasmah ce ke tukin motar su shiga nan su fita can cikin garin Abuja, suna ta gaya wa Goggo wurare. Sai goshin magriba suka dawo gida. Kwanan Goggo Shatu bakwai tare da su ta koma Gaya da tsarabar Abuja rankatakaf! Nasmah ta yi shirin zuwa Lagos za ta yi sati biyu, Dr. Sakeenah ta roki Hajiya su taho tare da Kulsum tunda suna cikin hutu. Hajiya Nasara ta ce, hutun ai ba shi da yawa, nan da sati daya za su koma. Sakeenah ta ce, ko sati dayan ne a bar mata aron Kulsum. Sosai ta ke murna da wannan tafiyar. A daren ta shirya kayanta, kuma a daren sun yi waya da Taufeeq amma ba ta gaya masa za ta zo Lagos ba. Washegari jirgin Azman na safe ya daga da su zuwa birnin Ikko.
Chapter 17 · 0% Book details