← Book details Kara'in Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 18

Sashe 9

Kara'in Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani kallon mamaki suka bi Inna da shi, ganin kofin da ya faÉ—o daga cikin É—ankwalinta, shi Abba ba ta faÉ—o masa da ya yi ba yake kawai ta yadda aka yi uwarsa tsofai-tsofai ta saka kofin yake dan sun fahimci babu makawa acuci maza ta yi.

"Haɓɓasa aminiyar gaskiya ne ba a bori sa sanyin jiki ai gwara ki gwangwaje ki yi ƙara'in ki" Shattu ta faɗa tana kallon Inna.

"Acuci maza ne, kuma babu wanda na cuta dan mijina na yi kuma ya yaba É—aurin É—ankwalin" Inna ta faÉ—a tana juyawa ta kalli Jauro ta ce

"Ko baka yaba É—aurin ba Bebi"

Wani takaici ne ya turnuƙe zuciyar Jauro dan shi gabaɗaya hankalinsa ya ɗugunzuma ga tafiyar da ta ce za su yi cikin ƙarfin hali ya daure ya ce

"Eh ya miki kyau"

"Yawwa Bauti (Beauty) Jaurona ko a maida kofin cikin É—ankwalin?"

"Barshi kawai ai a haka ma kin yi kyau" Ya faÉ—a yana jin tamkar ya hau Inna da duka dan ya lura shirin tafiyar da take ba wasa a ciki.

"To kun dai ji daga bakin uban naku wanda aka yi É—aurin dominsa" Ta faÉ—a tana gyara É—aurin É—ankwalin ba tare da ta É—auki kofin ba ta , juya abinta Shattu na bin bayanta da akwatin, ganin haka ne Jauro ya yi ta maza ya tashi ya É—auki É—aya akwatin yana jin babu daÉ—i a ransa, suna dab da fita daga falon Baba ya ce

"Ku dakata Inna mun ji za a muku duk abin da kuke so a kan dai ko je gidan rawa" Ya faÉ—a kamar ya saki kuka.

"Eh mun amince" Abba ma ya faÉ—a ba dan ransa ya so ba.

"Kayyasa in ka ji ana ba zan iya ba to bai samu mutum ba" Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta ce

"A'a ku barshi kawai"

"Dan Allah Inna ki yi haƙuri" Abba ya faɗa cikin sanyin murya yana tsaye a gabansu.

"Ke ko Delu ki haƙura mana kuma babu kyau dai fushin uwa a kan ɗanta kuma Allah ma yana son mai haƙuri" ,Jauro ya faɗa yana wani karyar da kai fuskar nan tashi duk hawaye shaɓe-shaɓe

"Haba Delu ki yi haƙuri mana" Shattu ma ta sanya baki.

Dakyar aka shawo kan Inna ta aminci suka dawo da akwatunan nan kowa ya zauna Inna Delu ta ce

"Ni dama ba wai wani abun a zo a gani na ce ku yi ba ƴaƴan nan, yanzu kuɗi nake so ku bani gobe masu ɗan gwaɓi da direba a kai mu kasuwa mu siyo ƴan kayayyakin amarci sannan kuma ranar tariyar a kirawo mai kwalliyar amare (make up) Ta mini kwalliyar in fito rangaɗaɗau a amaryata, sai kuma a ɗauki motoci a kai jama'a can a ɗauki me kiɗa (DJ) A kai shikenan fa daga wannan" Ta faɗa tana kallon Abba da Baba da suka rasa bakin magana.

"To Inna za a miki duk abin da kike buƙata, idan har kika fasa tafiya" Baba da Abba suka haɗa baki wajen faɗa.

"Yawwa ƴaƴan nan ko da na ji ubangiji ya libga muku albarka ku wanye da duniya lafiya" Cewar Inna tana washe baki, Abba ya fito da 100k ya bata haka ma Baba shi ma 100k ya bata na siyayyar da ta ce za ta je haka suka rinƙa jero musu godiya da sanya musu albarka su dai haka suka amsa amma ba dan ransu ya so ba.

Washe gari tun da sanyin safiya Inna ta aika aka kira mata Lantana mai aiki, haka suka sanya ta a gaba wai za ta raka su siyayya, cikin zumuÉ—i Lantana ta yarda, da yamma haka suka É—umguma Inna, Shattu da Lantana a baya Jauro da direba a gaba haka direba ya É—au hanya Lantana ita ce mai faÉ—a kusu inda zai kai su suna cikin tafiya su Inna sai aikin washe baki suke.

"Tsaya, tsaya direba" Cewar Inna da ƙarfi tamkar wanda ta hango wani mugun abu ya tunkaro su da sauri direban ya taka birki ya ɗan gangara gefen titi yana tambaya ko lafiya.

"Haba É—an nan aiulafiya ce ta fito da mu kalli can wancan shagon na tsallake nake so ka kaimu kalli wata mata can ta saka kayan indiyawa ni ma irin nata nake so, Lantana ce ta fashe da dariya ta ce

"Inna wannan fa mutunmutumi ne ba mutum ba kayan siyarwa ne aka saka mata dan masu siye su ga yadda kayan yake yi a jikin mutum"

"Allahu akbar kabiran lallai komai yana binni wallahi, gaskiya Delu idan kika saka kayan nan har sai na kusa suma" Cewar Jauro yana kallon Inna Delu da bakinta ke buÉ—e kamar gonar auduga.

"Ai Bebi yau kaya sai mun siyo har dana banza dan kaima sai ka gaji da zaɓar naka" Cewar Inna tana kallon Jauro.
"Direba yi aikin ka kawai" Cewar Shattu tana Æ´ar dariya. Haka direban ya gangara ya je ya samu wajen parking ya ajiye motar su kuma suka fita su duka suka barshi a motar yana mamakin halin tsofaffin nan.

Ƙaton shago ne wanda ya haɗa komai da komai kayan mata kananan kaya dogayen riguna babu abin babu na maza da mata. Tun da suka shiga kallo ya koma sama.

Hular gashi, rigar amare gown, pakistan, dogayen riguna, rigunan bacci da rigunan bacci wanda basu kai ƙasa ba, bireziya mai ƙoƙo, sarƙa da ɗankunne takalmi mai tudu pos ta amare. Su ne kayan da Inna ta ɗakko Lantana na taya ta zaɓe.

Wandunan jeans, shirts, combos, glases pacing cap , wanduna tiri kwata, su ne kayan da aka zaɓarwa Jauro, sai murna yake zai dawo yaro ɗanye sharaf, shagon aski suka shiga aka yiwa Jauro askin zamani na samari

Daga nan kasuwar ƴan kayan maganun mata suka je suka kwaso kayan mata na amare wai za a ci amarci Jauro kwa sai washe baki yake zai kwashi ganima. Haka suka dawo gida niƙi-niƙi da kaya.

Tun da suka fito suna tsaye ana fiddo kayan sai ga Abubakar kallo É—aya ya musu ya É—auke kai.

"Kai fitsararren yaron nan baka da kunya kana ganin kakanninka amma ka ɗauke kai sai ka ce ka ga wasu bare, to wallahi ka shiga taitayinka, zo ɗauke mana kayan kanshiga da su" Cewar Inna cikin faɗa-faɗa dan ta lura Abubakar ɗin ba ya son cigabanta kwata-kwata yana ta zumɓura baki ya ɗauki ledojin ita ma Lantana ta ɗauki wasu suka shige ɓangaren Inna domin zuwa su ƙara kashe kwarkwatar idanunsu.

Bayan kwana huÉ—u

Yau ta kama alhamis ita ce ranar da za a yi shagalin bikin Inna da Jauro dan haka juma'a kuma za ta tare dan haka yau gabaɗaya wanda suka gayyato daga ƙauye sun hallara tun safe sai hada hadar ake yi masu kiɗan ƙwarya da aka ɗakko su sai aikin kiɗa suke masu rawa na yi su dai masu gidan wato sirikan Inna duk suna ɓangarensu abin duniya ya ishe su saboda abin da surukarsu ke yi hatta Abba da Baba tunda suka fita da safe basu dawo gidan ba sai dai sun bawa Inna komai da za a buƙata hatta hall da dj babu abin da baa ɗakko ba sun ajiye motoci da direbobi dan kawai su faranta mata, Amna ma gidan su ƙawarta ta tafi dan haushi da yake yanzu suna hutun makaranta ne.

Misalin ƙarfe biyu da rabi mai kwalliya ta zo da kayan kwalliyarta haka ta zauna jiran fitowar amarya a ɓangaren Inna a falon sai mutane da kowa je sabgar gabansa.

Inna ce ta fito daga ƙuryar ɗakinta (Bedroom) Hannunta riƙe da leda, mai ɗauke da kayan da za ta yi amfani da su.

"Ƴar nan ina fatan dai kin ƙware wajen yin ƙyalin(kwalliya) Nan na zamani dan ranar nan a TV na ga ana yiwa wata amarya baki ga yadda jagirar ta zanu ba raɗau kamar ka sace amaryar ka zangaya da gudu" Cewar Inna tana kallon yarinyar.

"Kar ki damu Iya in sha Allah idan na gama zaki yaba kwalliyar da zan yiwa jikarki" Mai kwalliya ta faÉ—a tana dariya, dan ita tunaninta amaryar da za ta yiwa kwalliyar jikar Inna ce .

"Wace magana kike kuma wace jikartawa, ai Namna (Amna) Baƙinciki take da auren nan ko zama bata yi a gidan ba bare har a mata kwalliya" Cewar Inna dan ita tunninta mai kwalliyar tana nufin ifan ta yiwa Amna ne.

"Auren dole ne kenan" Cewar mai kwalliya dan ita kwai yadda Inna ke magana ne ya matuƙar birgeta dan tana son hulɗa da tsoffi ko ba komai ka sha dariya abinka.

"Ke wai maganar me kike ana maganar auren ƘARA'I na soyayya kina maganar dole, kula ki gama mini dan kar mu ɓata lokaci na ji an ce kwalliyar akwai ɗaukan lokaci"

"Wai Iya mai za a miki tukunna?"

"Yau ni na ga ikon Allah ɓatan nono a ƙirjin budurwa, ban da kudura ya za a yi a ɗakko ki ki mini kwalliya amma kina mini wani tambyar rainin wayo"

"Ita ce fa amaryar kuma ita aka ɗakkoki domin ki yiwa kwallyar" Cewar Lantana da shigowarta kenan, da sauri mai kwalliya ta tashi tana kallon Inna da mamaki dan ta lura cikin maganar da Lantana ta yi babu wasa ko ƙarya a ciki.

"Ita za a yiwa make up?"

"Ni na ga ƙarfin hali ɓarawo da sallama ke dai ba aikin kuɗi kike ba to ina ruwanki ko bango aka ɗakko ki ki yiwa ai kuɗinki dai kika sani" Cewar Inna tana kallon yarinyar dan ranta har ya ɓaci.

"Haba Iya yanzu tsofai-tsofai da ke zamki ce a yiwa fuskarki kwalliya wannan abu duk a yamutse kamar k...
Chapter 9 · 0% Book details