← Book details Kara'in Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 18

Sashe 5

Kara'in Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kwa santa munfukan banza, wato kuna can ɗakunanku kun ƙule da mazajenku hankalu kwance ni ina nan a matsayin mai muku gadi yo Allah na tuba in ba dai dama su Umaru sun so su ja mini raini ba ya za a yi ina zaune da sirikai gida ɗaya amma a ce ina mazaunin bazawara kuma na ce zan yi aure suke neman hana ni, to tunda haka ne kowane ɗan banza zan sanya ya saki tasa matar su ma su zauna a gwauraye idan zaman haka da daɗi"

Tunda ta fara zuba suka saku baki cike da mamaki suke kallonta, dan sai ma yanzu suka fahimci inda maganar tata ta dosa.

"Inna wallahi bamu san da wannan maganar bama babu wanda ya faɗa mana Allah ne shaidarmu, mu ya za a yi mu hana sunnar ma'aiki abin da Allah ya halatta miki duk wanda zai hana ki ai bai so zaman lafiya ba" Suka haɗa baku wajen faɗa cikin girmamawa dan sun san kaɗan daga aikin nata ta sanya a mayar da su ƙauyen ko a a sake su baki ɗaya.

"Allah sarki Æ´aÆ´an nan ku yafe mini wallahi duk zatona da haÉ—in bakinku"

"Wallahi babu Inna ai ciwon Æ´a mace na Æ´a mace ne kowace mace za ta so ta muti a É—akin mijinta"

"Kai Allah sarki daman an ce mace ita ta san damuwar ƴar uwarta mace, da a ce ku ne na haifa da tuni an ɗaura mini auren ba za ku mini gardama ba amma wannan yarinya Maryama kai kamar kwakwa taƙi fir sai kuka take kamar matar marigayi, amma na san abin da zan yi ku tashi ku tafi Allah muku albarka" Ta faɗa tana share hawayen takaici.

"Amin Inna" Suka haÉ—a baki waje faÉ—a suka mata sallama suka tafi

WASHE GARI

Tunda garin Allah ya waye take ta saƙa da warwara tana son ta samu mafita dan dole auren take so a ɗaura mata. Sai da yamma ta fito lokacin babu kowa a waje ta fito tana ta waige-waige kamar marar gaskiya mai gadin ma yana bayi ta sulale ta bar gidan, titi ta tsallaka abinta tana ta saƙa abin da za ta faɗa idan ta je.

Masallacin juma'ar wanda yake unguwar ta nufa tana zuwa ta samu mutane a ƙofar daga can gefe zazzaune a bishiya suna hira, wurinsu ta nufa ta musu sallama suka amsa mata.

"Dan Allah limamin masallacin nan nake nema" Ta faÉ—a tana kallon matasan da su ma ita suke kallo.

"Gashi can shi ne wanda yake fitowa daga cikin masallacin" ÆŠaya daga cikinsu ya bata amsa. Nufar mutumin ta yi wanda zai kai Abba a shekaru rike yake da carbi a hannunsa sai ganin Inna ya yi ta nufoshi tana zuwa ta ce

"Gafar malam wajenka na zo"

"Ikon Allah to sannu iya ina saurarenki"

"Wallahi mijina ne Allah ya masa cikawa ...

"Allahu akbar kabiran Iya abinci kike buƙata" Ya katse ta,cike da tausayawa duk da bata yi kama da mai jin yunwa ba

"Haba É—an nan wane irin abinci ana maganar babban abinci, aure ne nake so shi ne Æ´aÆ´ana suka hana ni, na ce bari na kawo maka sadakin ka É—aura mini tunda ba haramun bane" Ta faÉ—a tana share hawaye tare da saka hannu a aljihun É—an tofinta ta zaro kuÉ—i.

"Aure iya"

"Yo aure mana É—an nan ku ma da kuke malaman kana tantama da maganar auren bare kuma wanda ba malamai ba"

"Ba haka bane Iya"

"To karɓi nan, ka kirawo matasan can na zaune su zo ku haɗu ku ɗaura mana aure"

"Ina angon"

"Yana can ƙauyenmu, yo ai yana so na ba sai yana nan ba duk abinda na zartar daidai ne"

"Iya ki riƙe kuɗinki mu je gidan ƴaƴan naki sai a musu nasiha su barki ki yi auren"

"To ba a ƙi ta mutum ba"

Haka suka ta shiga gaba yana binta ashe dai ya san gidan ya yi mamakin ganin gidan Alhaji Umar da Alhaji Sa'adu ne ashe mahaifiyarsu ce mai son yin aure tsofe-tsofe da ita.

Haka aka sha É—auki ba daÉ—i da liman da su Abba da Hajiya Inna suna ta kawo hujjoji ita kuma tana ta sharar hawaye ta dage a kan za ta gudu ta shiga yawon duniya idan ba a É—aura mata aure da Jauro ba a haka dai suka amince ba dan sun so ba sai dan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ta dage a kan sai a gidan nan za ta zauna ita da Jauron haka suka amince ba dan ransu ya so ba. Bayan an daidaita da Jauro ya yi matuƙar jin daɗin zaman da za su yi a birnin Kano dan haka ya xe zai siyar da komai nasa dan su dawo nan da zaa ko Kande da ta tada ɓasa hankalin ba zai tafi ya barta ba Inna ta saka an bata inda za ta zauna a cikin gidan.

Dan haka aka tsayar da ranar ɗaurin aure Inna ta saka Shattu ta gayyato mata ƴan ƙauyensu dan su zo su sha bidiri.

Page 7⃣➡8⃣

RANAR ÆŠAURIN AURE

Zaune take a kan kujera mai mazaunin mutum biyu, sanye take da atamfa ja wacce aka yiwa kwalliyar manyan ganye koraye, riga da zani sai ɗankwalin atamfar da ta tufka uban gwaggwaro irin nasu na tsoffi, hannayenta sanye da awarwaraye ƙafar nan ta sha jan ƙunshi dagwal har wajen ƙwaurinta. Kwalli ta rambaɗa da janbaki kai har ma da jagira ta zana abinta jagirar tamkar wanda aka zana da muciya gashi ya haɗu da yamutsatstsiyar fuska. Shattu aminiyarta ce a kusa da ita, ita ma irin kayan Inna Delun ne a jikinta sai washe baki suke kamar wanda ka yiwa albishir da tafiya aikin hajj bana.

Mata ne cike a ɗakin ƴan ƙauyukan su, suna zazzaune a falon suna ta cin abinci wasu tuwon shinkafa da taushe sai rangaɗa hira suke ana yi ana suɗe hannu, da alama ma dai akwai abin da ke faruwa na fari ciki.

"Wai ni Shattu har yanzu auren nan bai ɗauru ba, tun daɗewa aka tafi amma har zuwa yanzu ban ga ana shigowa da goro da alawa ba bare in tabbatar da zamana matar Jauro, karfa a yi mini sakiyar da ba ruwa, dan wallahi kwarankwatsa dubu matuƙar su Sa'adu rufata suka yi ba ɗaurin aure aka tafi ba, to a yau ɗin nan ba sai gobe ba zan ɗagawa kowannensu nono, tsinuwa kwa sai na tabbatar sun gama tsinuwa zan daina ja musu ita, ace na tara jama'a dan taya ni murna amma an shanya mu kamar wasu kaya a igiyar shanya"Inna Delu ta faɗa cikin raɗa dan kar mutane su fuskanci me ke faruwa, jikinta babu ƙwari dan duk ta gama sarewa daga samun cikar burinta.

"Haba Delu me yasa kike da gajen haƙuri ne? Ai duk gaggawar asara ta jira samu ko, sai ki bari ki ga gudun ruwan yaran nan amma ba wai kike ikirarin ɗaiɗaita musu rayuwa ba ta hanyar ambata musu tsinuwa bayan kin tursasa musu su aurar da ke, ai duk lalacewar naka nake ne, kuma naka sai naka daɗin zama sai bare, sannan ma ba da ni ba gaɗa a hurumi, in goyi bayanki da tsinewa ƴaƴan cikin ki yo Allah na tuba kika tsinewa su Umaru ina muka kama kuma" Cewar Shattu cikin ƙarfin hali dan ita ma gabaɗaya ta sare da ɗaurin auren aminiyar tata.

"Haba Shattu bakya tausayina yanzu a ce shekarata 70 amma sai yanzu zan yi auren soyayya, amma ina shirin rasa maƙwallaton zuciyata kuma marurun raina Jauro kina wata magana, na lura yaran nan kishin mataccen ubansu suke" Cewar Inna tana fakar idanun ƴan ɗakin ta share hawayen da ya taru a idanunta

"Ki dauri ki jure Delu, dan rabon kwaÉ—o ba ya hawa sama kuma duk nisan dare ai gari zai waye, in har kuna da rabon aure to za a É—aura in kuma babu to sai...

"Bakin ki ya sari É—anyen kashi Shattu, ai rabon aure ma kamar an yi an gama...

"Aure ya ɗauru, tsakanin Aisha (Delu) Tare da Jabiru (Jauro) A kan sadaki dubu hamsin lakadan ba ajalan ba" Maganar da wani maroƙi da ya shiga faɗa a lasifika

"An ɗaura, an ɗaura na zama matar Jauro Allah na gode ma" Cewar Inna Delu da ta tashi tsaye ta fara taka rawa tana waƙa, ita ma Shattun tsaye ta tashi suka shiga taka rawar a tare gabaɗaya falon ya karaɗe da guɗa kowa ƙoƙarin tofa albarkacin bakinsa yake na guɗar dan duk ɗakin kowa ya san cewa Delu tana mutuwer son Jauro haka shi ma yana ƙaunarta.

Shattu ce ta ɗakko ƴar pos ɗinta ta buɗe ta ɗakko ƴan biyar-biyar sabbi dal ta shiga liƙawa aminiyar tata tana yi tana cewa

"Alƙawari ya cika amarya, alƙawari ya cika amarya, in angonki ya shigo amarya ki yi masa fifita, amarya ki bashi ruwa ya sha, amarya alƙawari ya cika amarya" Tana yi tana mata liƙi ita kuma Imma Delu sai rawa take tana juyi, gabaɗaya matan falo ma tashi suka yi, suka haɗu da Inna ana ta rawa ana ranbaɗa guɗa ko hannu basu wanke ba da suke cin abinci.

Inna! Inna!! Inna!!!" Cewar Abubakar cikin ɗaga murya rai a ɓace yana wani muzurai da cin magani sai wani harare-harare yake yana musu kallon ɗaya saura kwata. Cikin kiɗima Inna da Shattu kai har ma da ƴan ɗakin da ke ife-ife da guɗa suka dakata kowa ya maida hanklinsa kan Abubakar ɗin da ya shigo kamar an koro shi.

"Habubakar kar dai ka ce mini maroƙin nan ƙarya yake ba a ɗaura ba ya karaɗe gida da sanarwa? Idan kuwa har ƙarya yake to wallahi sai na ɗaureshi daga shi har danginsa har sai igiya ta yi saura, a kan ɗaga mini hankali da ya yi" Cewar Inna cikin tashin hankali, burinta kawai Abubakar ɗin ya bata amsa bata ma lura da manyan ledojin hannunsa.

"Oho miki, gashi in ji Abba" Ya faɗa yana dangwarar mata ƙatuwar ledar goro, alewa, da kuma dibono wacce Abba (Sa'adu) Ya bashi ya kawo mata saboda ta ce matsawar ba a sayi goro da alewa da dabino an raba a wurin ɗaurin aure ba sai ran kowa ya ɓaci.
Chapter 5 · 0% Book details