← Book details Kara'in Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 18

Sashe 13

Kara'in Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fusace ya shigo wurin yana shigowa ya yi wurgi da ƙarfen hannunsa rai a matuƙar ɓace. Yana shigowa idanunsa suka sauka a tsakiyar kan furfurar amaryarsa kan nan kawai yake hangowa tana daga durƙushe Shattu da Lantana suna ta faman ta tashi amma kunyar yadda rigarta ke a ɓarke ga babu bireziya dan hannun ɗaya bireziyar ma ya maƙale a jikin ɗankunnenta, ga ihun da wajen ya karaɗe wurin ranta in ya yi dubu ya ɓaci yadda gashin kanta da ta san ko kitson kirki babu a jiki dama hular gashin da aka saka ita ce rufin asirin kan sai kuma saurayin nan ya cire mata dan ya kunyata ta a gaban jama'a.

"Ya Allah kai ka san karatun kurma, ranar ƘARA'IN nan da na ci buri a rayuwata, tun da aka ɗaura auren nan ko barcin kirki bana yi sabo da ɗoki amma a ce yau tun daga farkon shigowarmu muka sha ƙasa ni da ango na anya ba hannu aka saka mini ba, wani ɗan hana ruwa gudu, wato sa'idinawa wanda ana ruwa suna irgawa" Cewar Inna a ranta zuciyarta na ƙuna.

"Jama'a ku kauce, ku jaye ga ango nan da ƙarfin gwiwarsa ya dawo daga filin dagar ya je ya ɗauki fansa ya dawo" Cewar MC a lasifika.

"Ka ji ɗan jaraba, in banda dai neman magana fansar me na ɗauka in banda jikina da ya faɗa mini, kan nan nawa kamar na ɗauki duron kananzir, ai ba dan ba dan ba da na ce wannan ƙara'i ban ji daɗinsa ba" Ya faɗa a ransa lokacin da ya ƙaraso wajen yana aikawa MC wata muguwar harara kamar dai shi ya ce ya bi bayan saurayin.

"Ɗan tsoho ƙyamus-ƙyamus ba ni na ce ka yi auren ƙara'i ba kuma ba ni na saka ka bin saurayin nan ba, ka ga kuwa ba ni na kai zomon ba rataya aka bani" Ya faɗa a ransa yana saki wata ɓoyayyar dariya.

Cikin hanzari Jauro ya nufi inda su Shattun da Inna da Lantanar suke. Su Kande da Karima kuwa sun daɗe da cikawa rigarsu iska dan tun lokacin da ta watsa manjan ta shige ƙasan kujerun da ke wajen shi sa ba a ganta ba, bayan hankalin mutane ya koma wajen Inna da saurayin sai ta fito suka silale suka fice daga wajen, daga nan kuwa garinsu suka koma dan dama Jauro ya ce sai ranar da amarya za ta tare za ta dawo gidan da zama.

Yana zuwa Shattun cikin sanyin murya ta ce

"Yawwa ango, ka ganta nan sai fama muke da ita ta ƙi tashi" Wani haushin Shattu ne ya cikawa Jauro ciki da ta kirashi da suna ango, dan shi a yadda jikinsa yake a damule da manja kai da cillukutu ko abokin ango bai ci a ce an kira shi ba bare ango, gashi ji ya yi kamar ya zabgawa Shattu da Lantana mari da suka bar Delunsa a wajen ai da ko cicciɓarta sun yi sun kaita wani ɗaki.

Hannu kawai ya miƙa ba tare da ya ce uffan ba, Delu da ke durƙushe kanta a ƙasa sai ji ta yi an sure ta an yi sama da ita, sosai ta tsorata dan tunaninta wani ne cikin samarin wurin a sure ta gabaɗaya zai gudu da ita ya mata fyaɗe, dan sosai ta tsorata da lamarin abin da saurayin nan ya mata, sannan bata zaci Jauro zai iya ɗaukanta ba. Tana ɗan ɗago fuska ta sauketa a kan fuskar angon nata da ta sha manja abinta sharkaf, kamar daron da ake siyar da manjan wani tausayin kansu ne ya kama Inna Delu ganin halin da suka tsinci kansu a ciki a yau da ta kasance ranar farinciki.

"Bebi in ce dai ka sumar da shi da ƙarfen nan?" Cewar Inna tana kallonsa. Ai maganar nan da Inna ta faɗa Jauro ji ya yi wani kishi ya ƙara taso masa gashi ba ya so ya faɗa mata gaskiya ta ga ragwantarsa dan haka sai ya ce

"Ai na masa illa, ma dakyar mutane suka ƙwace shi, yana can lange-lange aka tafi da shi asibiti" Ya faɗa yana kallon gefe dan kar ta gano ƙaryar da ya sheƙa mata. Wani daɗi ne ya baibaye Inna jin an ɗau mata fansa hakan ya sanya ta ƙara jin ƙaunar Jauro a ranta.

"Lallai na auri miji na nunawa sa'a" Ta faÉ—a a zuciyarta tana jinjina jaruntarsa.

Tun da ya ɗakko Inna Delu mutane suke ra binsu da kallo samari da ƴan mata kuwa sai ihu suke ganin ango ya yiwa amarya ɗaukan jarirai, hakan ya sa wurin ya ƙara kacamewa da ife-ife shi kuwa bai bi ta kan koa b duk da nauyi yake ji da ya ɗauki Inna kamar wanda ya ɗauki buhun gero, dan dakyar yake ɗaga ƙafafunsa ƙarfin hali ne kawai yake. Ɗakin da aka ajiye musu kayan da za su canja da magriba saboda ƙayatarwa to yanzu kuma tun da komai ya kwaɓe musu dole yanzu su canja kaya tun da kayan sun ɓaci da manja.

Suna shiga ɗakin Jauro ya nufi wata kujera mai zaman mutum ɗaya da ke ajiye yana zuwa jaɓar ya saki Inna a kan kujerar ashe kujerar tsohuwar kujera ce dan haka Inna ji kawai ta yi ta ɓurma ciki, kafin raɗaɗin faɗawar ya gama ratsa t sai ji ta yi mazaunanta sun yi karo da wata ƙusa wani uban ihu ta saki wanda ya saka Jauro da ke sunkuye ya ɗago dan tun da y jaɓar da ita a kan kujerar ya sunkuya saboda ƙagewa da bayansa ya yi na gudun da ya tiƙa da kuma ɗaukan da ya yiwa Inna.

"Wayyo ni Delu yau dai ina ganin sauyawar kalolin rayuwa kamar wacce iyaye suka jeki ka gani, in banda jafa'i da neman rarrabuwar sassan jikin mutane ya za ayi a ajiye wannan ƙazamar kujerar mai jiki duk ƙusoshi " Ta faɗa tana ƙoƙarin kai hannu wajen mazaunan nata tare da sakin wani kuka.

"Haba Delu wai me yasa kike haka ke ba damar a yi abu sai ki ɓare baki ki fara kuka kamar matar marigayi, saboda ke ga mai arahar hawaye"

"Au haka ma zaka ce Jauro, bayan ka jefa ni kan ruɓaɓɓiyar kujerar nan na faɗa a kan ƙosa"

"Wato Jauro gatse-gatse ko sakayawa babu, ko kan ƙaya tsidau na jefa ki ai kya gode mini domin kuwa na yi namijin ƙoƙari da na ɗakko ki a hannu na, tun daga filin can har nan, hannu na da kafaɗata kamar an sara mini da gatari saboda tsabar ƙagewa da suka yi"

"Na faɗa Jauro, kamar wani wanda na yi saɓon Allah dan na faɗi sunanka shin da soyayya ma tana bari masoyi ya ji nauyin masoyi, baka ga yadda turawa ke ɗaukan matansu ba"

"Ashsha Allah baki haƙuri Bebi" Ya faɗa dan kawo ƙarshen maganar.

Banza ta masa tare da taɓe baki, tashi ta yi dakyar daga kan kujerar ta shiga bayi ta wanke fuskar tas ta fito ta cire kayan ta sanya wanda Lantana ta kawo musu, shi ma ya shiga bayin ya gyara jikinsa tare da canja kayan nasa sai gasu sun fito a amarya da angon su. Hannunta ya kama suka fito suna sakarwa juna murmushi gabaɗaya wuri ya ruɗe da fitowarsu haka suka ƙarasa wajen teburinsu.

"Yanzu amarya da ango za su yanka cake" MC ya faÉ—a.

Cikin washe baki suka tashi Jauro sai washe baki yake jin zaa yanka cake dan gabaÉ—aya yawun bakinsa ya tsinke. Haka suka kama hannu a tare suka yanka cake É—in.

"Ango zai fara bawa amarya a baki sai ita ma ta bashi" Cewar MC.

Jauro hannu ya kai ya ɗakko cake ɗin da ya gutsuro da wuƙa, ya nufi bakin Inna da take wani ɗan sunkuyar da kai alamar kunya irin ta amare, dakyar da ta buɗe bakin aikuwa ya saka mata, a take aka ɗauki ihu da tafi.

Inna tunda cake É—in ya isa bakinta ta ji wani irin É—aci da tsami a lokaci guda haÉ—e d warin kananzir, amma haka ta daure ta É—an runtse ido yadda mutane ba zasu lura ba ta haÉ—iye ba tare da ko taunawa ta yi ba ita kaÉ—ai ta san bala'in da ke cikin cake É—in wanda ya ziyarceta amma kuma bata ya aka yi haka ta faru ba.

"Amarya sai gareki ke ma za ki bawa angon naki cikin shauƙi na soyayya" Inna da ta yi nisa wajen tunanin ya aka yi haka ta kasance ta tsinkayi muryar MC yana magana.

Inna cikin rashin kuzari ta yanko cake ɗin ta ɗauka a hannunta, tunda ta fara yankowa yawun Jauro ya cigaba da tsinkewa sai haɗiyewa yake wani yawun na ƙara taruwa, bare da ya ga ta ɗakko a hannunta ai har wani dillo harshe gake, sai dai yadda Inna ta birgeshi ƙato ta yanko ya san dai duk faɗin bakinsa dole wanda ta yanko ya cika masa baki. Inna kuwa tunaninta ɗaya kar fa ta saka masa a baki ya kunyata ta, dan ta san dai akwai gwarama matsawar Jauro ya ji ɗanɗanon cake ɗin gashi tana so ta masa bayanin kar ya kunyata ta amma kuma idanun jama'a a kansu, sannan tana so ta masa raɗa a kunne sai dai ta ga gabaɗaya hankalinsa a kan cake ɗin yake sai wani raba ido yake yana washe baki.

"Haba Delu ƙur'ani kika yi jinkirin saka mini cake ɗin nan a bakina sai dai jama'a su ga yawu yana dalalowa daga bakina saboda gabaɗaya yawuna ya tsinke ƙiris yake jira ya zubo" Ya faɗa a zuciyarsa a fili kuma sai ya shiga ɗan kannewa Inna ido ɗaya yana mata alamar ta sama.
Hannu ta ɗaga a hankali tana so ta saka masa a bakin nasa har dai ya yi ƙarfin halin cewa

"Wannan ɗaukan alhaki da yawa yake Delu mai magana (MC) A dodon magana (Lasifika) Yana cewa in baki na yi saurin baki amma ni kike jirgani" Ya ƙarasa faɗa cikin raɗa-raɗa. Ta ji shi sarai amma sai ta masa banza.

"Bebi ka ce azumi kake" Ta faÉ—a masa ita ma cikin raÉ—a dan ta lura in ta zauna masa bayanin abubuwan da ke cikin cake É—in ba ganewa za ta yi ba.
Chapter 13 · 0% Book details