← Book details Kara'in Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 18

Sashe 10

Kara'in Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke! Idan ba za ki yi ba ki kama gabanki u nemi wata" Inna ta faɗa tana harararta, mai kwalliya dai ganin da gaske Inna za ta yiwa sai kawai ta zauna ta shiga fitar da kayan kwalliyarta sai da ta gama tsaf ta kama fuskar Inna ta fente ta tass kamar budurwar amarya, dan har gashin gira aka askewa Inna da za a zana jagira wajen kwalliyar baki kwa sun ɓata lokaci saboda yadda bakin nata yake guluf na tsofaffi haka aka buɗe ledar Inna aka
É—akko wedding gown É—in da suka siyo aka zige zip É—in ta sanyata mai kwalliya ta rangaÉ—a mata É—auri mai fanka sannanta sanya mata komai sai ga Inna ta fito a amaryarta.

Haka dai ta saka takalminta da yamma aka zo za a tafi É—akin da aka kama har da wasu kayan Inna da Jauro suka tafi dan canjawa.

A bayan mota aka sanya su motoci huɗu ne suka tafi cike da mutane, ana zuwa ɗakin taron aka tarar da wasu mutanen a can ga kuma wurin zaman amarya da ango ya sha decoration yinƙurawa ya yi ya fito sanye yake da shaddarsa fara ƙal ta sha aiki sai Inna ma ta fito daga ɗaya ƙofar gabaɗaya sai kallo ya koma kansu...

ƘARA'IN INNA DELU
💄💄💄💄

NA

MAMAN AFRAH

FCW💛

Page 1⃣3⃣➡1⃣4⃣

Da yake ba wani tsaro aka saka a wurin ba duk mutanen gari sun shigo kallo musamman samari, yadda wurin ya tsaru kowa ya ɗauka zai ga amarya budurwa ango saurayi amma suna fitowa aka fara tozali da wata uwar furfura da ta yiwa Jauro ƙawanya a fuska ga wani aski da aka masa na zamani aka aske wani wurin wani wurin aka bar masa gashi sai ya zama kamar irin fataken nan wanda suka daɗe suna yawo basu samu gari a kusa ba. Inna na fitowa daga motar da yake rigar tata doguwa ce ta mata yawa ko ƙafar baka hangowa da takalminta mai tudu gashi kuma yadin satin ne aka yi ɗinkin da shi sai aka ɗora net aka sosai rigar ta mata yawa, tana fitowa kowa ya saki baki yana kallonsu banda ƴan ƙauyensu da dama sun san su waye amarya da angon.

Shattu ce riƙe da wani bokiti da aka zuba ganyen maina irin wanda ya yi yellow ɗin nan tana watsa musu a matsayin furanni dan Inna ta ce babu wani abu da ba za a musu ba sai dai ko idan mantawa suka yi da shi.

Tana watsa musu tana carara guda duk da mc ya ƙure kiɗa baka jin komai amma bata daina guɗar ba, Jauro ne ya riƙe hannunta irin yadda amarya da ango suke yi, matakala ce a wurin suna zuwa sun hau ɗaya biyu suna shirin hawa ta ukun rigar Inna ta taɗe ta aikuwa ta zame ta tafi za ta faɗi, da sauri Jauro ya tareta ashe shi ma rigar ta maƙalo da ƙafarsa aikuwa suka tafi a tare suka tiƙu da ƙasa ji kake tim sun faɗi ai gabaɗaya samarin nan da suka ziyarci wurin ba gayyata suka ɗauki wani uban ihu kamar an ci ball a gidan kallon ƙwallo. Gabaɗaya wurin ya kaure da ihu wasu har fito suke, da yake da suka faɗin Jauro ne a ƙasa ita kuma sai ta faɗa da rubda ciki a kansa, duk sai kunya ta rufe su, Shattu bokitin ganyen mainar da take watsawa a matsayin furanni ta ajiye tana sakin wani salati ta nufe su cikin azama tana faɗin.

"Ya subhanallahi, amarya da ango an sha ƙasa, yo dama ku da za ku shigo cikin mutane ai bakwa fito ba tare da kun sha lahaula ba, ko maganin baki saboda kallo, yadda kuka yi kyan nan ai sai ido ya kama ku kar fa ku manta duk taron nan saboda ku aka yi kuma kowa ƙoƙarinsa ya ganku wasu har ɗaɗɗage suke dan su hangi amarya da ango" Ta faɗa tana ƙarasawa wurinsu ta ce

"Sannu Delu sannu Jauro ai sai ku tashi ku karkaɗe jikinku domin ƙasa ba sirikar kowa bace da za ku ji kunyarta"Cewar Shattu tana miƙa hannu za ta ɗaga Delu dan yanzu ta gangara ƙasa daga kan Jauron, gashi taƙi tashi sai Shattun ta ce

"Ki tashi mana ku ƙarasa kan kujerunku na amare"

"Haba Shattu kin ji ƙirjina kuwa...

"Wane irin na ji ƙirjinki kuwa ke da kika faɗi ai ke za ki ji a jikinki dama" Shattu ta faɗa rai ɓace dan ta fi so Innar ta tashi saboda yadda idanu suka musu caaa

"Haba ina dalili dama ai laifin Lantana ne da bata saka an rage mini tsawon rigar nan ba ta barni ina yawo a ciki zulum-zulum kamar limamin masallacin juma'a zai yi kuÉ—uba...

"Wai Delu ki tashi mana banda ma ɗan adam ke da Allah ya taimake ki kika faɗa a kan Jauro da kan dakalin nan kika faɗa ai da kin ji a jikin ki" Cewar Shattu tana kama tsantsa ganin Delu ta ƙi tashi.

"Ke kike ganin na faɗa kan Jauro, amma ni na san inda na faɗa, yadda na bugu a ƙirjinsa ankan ƙashin haƙarƙarinsa baki ji ba kamar wanda na faɗa kan duwatsun wuta, har sai da na gwammace a kan dakalin na faɗa, yo ƙirjinsa babu tsoka ko ƙwaya sai ƙashi kamar ƙashin kan saniya, yadda kika san baya cin abinci" Cewar Inna tana kai hannu fuskarta ta shiga cire ganyayen mainan da suka lilliƙe mata a fuska wanda Shattu ke watsawa a matsayin furanni, da yake zafi ake fuskar nan ta yi jargaf da gumi fawundation ɗin da aka mata kwalliya da ita duk ta haɗu da gumi ya gangaro har bakinta jagirar ta haɗe da ƴar uwarta fuskar nan ta miki kamar an shafa mata jan ɓurjin bulo, tana cikin cire mainan da yake yanzu a zaune take dakaka shi kuma gogan har yanzu bai tashi ba dan shi kaɗai ya san irin azabar da yake ji, tana cire maina sai wani ƙwaro ya hau fuskar aikuwa ta sanya hannu ta dakeshi daga fuskar ta da sanya hannu ta murtsuke fuskar dan ji ta yi kamar ƙwaron ya cije ta a fuskar duk wanda ya kalli amarya sai ya yi kamar ya shiɗe saboda dariya sosai foundation ɗin ta mata kaca-kaca da fuskar.

"Delu kin ganki kuwa" Shattu ta faɗa tana tuntsurewa da dariya, banza ta yiwa Shattu dan ita bata ma san kwalliyar ta caɓe ba, gabaɗaya ma jin jikinta take kamar an sheƙa mata ruwa saboda gumi ga zafi da kuma nauyin rigar.

"Kamani Delu, ɗago ni, ki taya ni in tashi wallahi allon bayana kamar zai rabe a biyu, wannan wane irin daɓe (ploring) Ne suka yiwa wurin nan wallahi yadda kika san ƙarfe wajen ya daɓu sosai sun samu ma'aikatan gini wanda basu da ha'inci da kuma yashi na kirki marar algus da ƙasa, simintin da suka yi amfani ma da alama irin mai luwai-luwai ɗin nan ne.

Tunda ya fara magana Inna da ke zaune take jifansa da wata ƙatuwar harara, ita takaicinta ma ɗaya yadda ta ji ƙirjinsa babu komai banda tarin ƙasusuwa, wani kishi ne ya turnuƙeta dan tana ji a ranta cewa duk Kande ta lale tsokar wajen shi yasa ta ji saura ƙashi, baƙincikinta ɗaya shi ne babu abin da za ta samu a wajen na amarci.

"Kai wannan mutum akwai ayar tambaya a kan ka wallahi ka ce wai Kande kana ɗan yin sunna da ita saisa -saisa amma gashi duk ta lale tsokar jikinka sai ƙashi wato ma kullum a nan take aaɗora kanta" Cewar Inna a ranta wani kishi na turnuƙeta a gefe ɗaya kuma wata ƙwalla na cika idanunta a fili kuma ta ce

"Zaka tashi da kan ka ka kama hannun nawa irin yadda ake yiwa amaren mu ƙarasa kujerar zaman namu ko kuma zaka tsaya jiran gawon shanu ne har sai na ɗaga ka, to in kuwa haka ne wallahi iska na yawo da mai kayan kara dan ko yatsanka ba zan kama ka tashi ba, banda ragwanta mai makon da zan faɗin daka taro ni ka mini irin ɗaukan da namiji ba indiye ke yiwa ba indiya wato ɗaukan jarirai kar ka bari na kufce daga hannunka yadda za a tafa mana amma shi ne kai ka faɗi ni ɗin ma na faɗi gashi nan maimakon a mana tafi ihu ake mana, zaka bar mini abin gori son a je a baiwa Kande labari take goranta mini" Cewar Inna har lokacin bata daina jifansa da harara ba.

"Haba Delu bakya ganin mutane suna kallomu, a bainan nasi fa muke in banda ma ƙaran kiɗan nan ai da sai kowa ya ji abin da kike cewa...

"Yo su ji mana abin kunya ai ni gaba na bashi ba baya ba, tunda dai suka ga faɗuwarmu mai kuma ya rage, ai komai aka yi da jaki sai ya ci kara in banda ma abin kirki bai gaji kare ba in ya yi ma zaginsa ake, ta yaya za a ce amarya da ango sun sha ƙasa, musamma ma ni amarya, ai amarya ko ta buzuzu ce sunanta amarya a wajen ango" Ta faɗa tana ƙara sharɓuno fuskar zuwa lokacin fuska ta kwaɓe kwaɓ kamar wanda aka yiwa bango flasta da kashi.

Jin maganganun Inna Jauro ya yi ta maza ya miƙe zaune, kamar wanda aka janyoshi ya sake komawa ya kwanta lifet, dakyar dai ya tashi zaune yana yatsina fuska alamar shi kaɗai ya san abin da ya ji.

"Kai Bebi na doku a ƙasan nan yadda kika san ba faɗuwa na yi ba, kamar wanda muke dambe aka samu wanda ya fi ƙarfina ya ɗaga ni sama ya niƙa ni da ƙasa wallahi haka na ji" Ya faɗa, yana ƙoƙarin miƙewa dakyar a dai dai nan ne Lantana da ta koma gida domin ɗakkowa amarya gwaggwaron da za ta yi amfani da shi in za ta canja kaya da magriba ta dawo cikin sauri ta nufi wurin suka kama Inna ita da Shattu suka ɗaga ta tsaye hakan ya yi dai dai da tashin Jauro tsaye aikuwa ya miƙa hannu zai kama hannun Inna ta janye tana ɓata rai.
Chapter 10 · 0% Book details