Sashe 4
Kara'in Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Dan Allah Inna ba dan mu ba" Baba ya faÉ—a kamar zai yi kuka.
"Kai rufe mini baki, ba waɗannn ka ɗakko ba kana ganin kamar su za su saka ni abin da ban yi niyya ba, to duk cikinku babu wanda ya isa ya tauye mini haƙƙi, ni babu wanda na hana ya ƙara aure a cikin ku ko mata huɗu kuke so babu mai hana ku, amma duk wanda ya ce ni zai hana rawar gaban hantsi, to mu zuba shege ka fasa ɗan halak sai yanka, kuma duk wanda ya ƙara yunƙurin hana ni aure sai na saka ya saki matarsa ya zauna a gauro ya ji idan zama haka ba aure da daɗi" Ta faɗa tana miƙa hannu ta ɗauki kankan ɗaya ta kai bakinta har ruwan na gangarowa daga bakin nata ta saka harshe ta suɗe. Tun da ta yi maganaar sakin matansu sai duk suka shiga taitayinsu, babu wansa ya ƙara magana.
"Ke ma kuma in sak naki mijin ya sake ki sai ki dawo mu zauna a tare" Ta faÉ—a tana kallon Maryam da gabanta ya buga jin furucin Inna na saki.
Haka sai su Rabilu suka yiwa Inna sallama suka fice sumi-sumi su da su Abba, Maryam kuma bedroom ɗin Inna ta kwanra tana jiran mijinta ya zo ya ɗauketa su tafi, dan sun yi magana ya ce zai zo bayan magriba saboda ta gaji da abubuwan nan da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa, dan har alla alla take a gama maganar kafin mijin nata ya zo dan bata so ko ɓurɓushin maganar ya tarar a barta da abin kunya. Inna kuwa ko ta kanta bata bi ba dan ta yi alƙawarin babu wanda za ta saurarawa matsawar dai babu wanda zai goyi bayanta.
BAYAN MAGRIBA
Zaune suke a falo su uku Inna tana kan sallaya ta miƙe ƙafafunta tana jan carbi dan tun da ta idar da sallar magariba bata tashi daga wurin ba. Sai Maryam da Amna da suke cin abinci a falon suna hira abinsu, bayan sun kammmala Amna ta kwashe kwanukan ta kai kicin ya cewa Maryam
"Aunty bari in je zan yi karatu"
"To my Amna a yi karatu da yawa, sai yaushe za ki je gidan nawa kuma?"
"Sai dai idan na samu lokaci dan yanzu makarantar boko da islamiya babu hutu amma zan zo"
"To Allah taimaka ya baku sa'a sai kin zo É—in ina zuba ido" Cewar Maryam tana kallon Æ´ar wan nata. Fita Amna ta yi wanda hakan ya yi dai dai da shigowar mijin Aunty Maryam É—in sa sallama cikin É—an sakin fuska Inna ta amsa masa saboda ta san ko ba komai idan zai tafi yana bata kuÉ—i sababbi Inna kuwa akwai son sabon kuÉ—i dan wano lokacin ma sai ta yi ta ajiyarsu kamar wanda za ta rataya a wuya wai bata son kashe sabon kuÉ—i
ƘARA'IN INNA DELU
💄💄💄💄
NA
MAMAN AFRAH
FCW
Page5⃣➡6⃣
Ƙarasowa ya yi ya zauna Inna tana ta washe baki tare da masa marhabin. Bayan ya gaisheta take tambayarsa ɗan gidan Maryam ɗin yake sanar da ita ai daga makaranta gidan mahaifiyrsa ya wuce.
'Yo ke ko ruwa bakya kawo masa ba kika zauna kina wani zumu-zumu da baki kamar shazumamu ya samu sikari" Cewar Inna da ta lura da ɓacin ran da maryam ɗin ke yi tun shigowar mijin nata ita dai ta san dalilinta ma yin hakan. Ruwan ta tafi ta ɗakko masa a plate ta kawo masa tare da masa sanju da zuwa cikin sakin fuska ya amsa yana ɗaukan ruwan ya tilla ya sha ya mayar da ledar kan plate ɗin da yake pure water ne.
"Wannan matar taka ta koyi mugun hali wallahi"
"Mugun hali kuma Inna?"
"Eh mana kai vaka lura sa muzuran da take ba tun shigowarka ai ko idanunta ka kalla za ka ga sun yi luhu-luhu, to kuka ne ta yi ta garƙawa kamar da ranar sa ubanta Malam ya bar duniya"
"Subhanallahi mai ya yi zafi Inna" Ya tambaya da mamaki.
"Maza Maryama ki yi ta hararata amma wallahi harararki ba za fa hana ni faÉ—in abin da ke raina ba" Cewar Inna tana wani gatsina fuska.
Jin haka Maryam ta tashi fa sauri ta shige É—aki dan ta san yun da Inna za ta fara magana babu mai taka mata birki sai ta ida amma dai ta san yau abin kunya ne ta gama ja mata a wajen mijinta
"Inna idan laifi ta miki ai sai ki ja mata kunne...
"Yi shiru ɗan nan bakinka alekum, ai ba zan yi ƙasa a gwiwa ba wajen faɗa maka komai da komai ba in yaso ko addu'a ce sai ka taya ni a kan Allah ya mini mafita ya ganar da yaran nan gaskiya gaskiya ce ƙarya kuma ɓata ce" Ta katse shi tana rattabo bayaninta.
"Yarinyar nan Maryama da Æ´an uwanta ne suke son yin kisan kai...
"Subhanallahi, kisan kai fa Inna amma dai na tattabara ko?"
"Kai dallah ja can, ana maka maganar mutane kana ɓaganar tsuntsaye, to bari na maka gwari-gwari dan na tuna kisan zuciyoyi ya kamata in ce"
"Inna ban fahimta, sai ƙara ɓatar da ni kike, kin ce kisan kai kin ce na zuciya...
"Na gama shiryawa" Cewar Maryam da ta É—akko jakarta ta fito daga É—aki dan duk abin da ake faÉ—a tana jin su.
"To uwa gwadaga babu inda zai je sai na gama faÉ—a masa abin da ke raina wato shi ne kika É—akko wata shegiyar jakarki mai kama da zabirar aski, wai kin gama to sai dai ki jira shi ya gama shi ma"
"Haba Inna "Ta faɗa taa zunɓura baki tare da komawa ɗaki dan ta ga mijin nata ya saki baki cikin rashin fahimtar takamaiman abin da ke faruwa.
'Ɗan nan ina kai ka, kana jina, Maryma da Yayunta su ne suke so su daƙushe zuciyoyi guda biyu haka kawai fa dan na ce zan yi aure, saboda son tauye mimi haƙƙi da kuma neman dalili suke so su dakatar dani wai na tsufa, dan na tarasu na sanar musu tunda na kammala takaba in yi aure, ni ma in huta idan da rabon haihuwa ma ba sai a yiwa mai ɗakin naka ƙanwa ko ƙani ba, to fir suka ƙi yo daɗi ta musu ake lissafani cikin zawarawa bayan ga ƴan matan nan da zawarawa sun rasa mazajen aure amma ni Allah ya bani mijina a hannu amma dan kawai su shiga haƙƙina sai su ce babu maganar aure wai sai dai in zauna in ke sallah da salatin annabi kaar da can ba na yi. Ai gwara dai in mutu a ɗakin aurena, in banda ƙoƙari faɗawa mijin baya tariya, meye a ido banda ruwa, abu lami ba ɗaci ba, banda ma ɗaukan alhaki ɗanka ya hanaka sunnar ma'aiki, to shi ne na ce ko kai za ka mini WALI (Alwali) Cewar Inna tana kafe sirikin nata da ido dan shi tun daga lokacin da ta ambaci aure ya saki baki yake kallonfa dan har ta gama leɓɓansa bash haɗu ba suna nan a buɗe.
"Kai ko kaima mijin ta ce ne, yo ya za a yi in zaunar da kai ina faÉ—a maka magana sai ka saki baki sharam ya layar mai tafiya kana kallona, ko baka fahimci inda maganar ta dosa bane na maka gwari-gwari"
"Eh Inna haka ne dama ai"
"Sammani anya kuwa cikin hayyacinka kake ko dai ka farw shaye-shaye ne, ya xa a yi in taƙarƙare in zabgo maka bayanai rututu amma ka kasa bani gamshashshiyar amsa sai ka ce wai eh Inna haka ne" Ta faɗa tana mere baki tate da maimaita abin da ya faɗa ta hanyar kwaikwayar muryartasa.
"Ko É—aya Inna babu abin fa nake sha"
"A'a yo ni ai ban ga alamar hakan ba, yo wannan ai ba shawara bace ba kuma mafita bace ka bani Allah na tuba wannan magana taka akwai ya babu kakar wajen uba, ina so in ji ka zage kana rattabo bayanai sai kwai ka ɓige da eh Inna haka ne, tashi ku je Allah bamu alheri dan na ga kai da matartaka halinku ɗaya bakwa son ƙaruwata tun da kuwa haka ne sai ko ka ga katin gayyata dan aure babu fashi ko ana ha maza ha mata.
Sammani kamar jira yake ya miƙe tsaye yana gyara zaman babbar rigarsa, dan shi gabaɗaya yadda kansa ya ɗaure da maganar Innar idan da a ce mahaifiyarsa ce ta zo da wannan maganar ai sai dai ya zauna ya yi ta girka kuka saboda bai san mafita ba a ce mace tsofai-tsofai da ke kina maganar ƙara aure daga mutuwar mijinki.
Haka dai ya sanya hannu a aljihu ya É—akko rafar Æ´an É—ari biyu ya ajiye mata a gabanta ya ce
"Gashi Inna kya sayi goro"
"Ikon Allah yo kai kuma Sammani a yi haka, har da kuÉ—in goro kamar yadda aka saba ai da ka barshi a haÉ—u a gaba tunda ga abu nan ya taho kar wahalar ta yi yawa"
"Menene ya taho"
"Yo har ka tambaya ma kai da yanzu na gama baka labarin zan yi aure ai ko dan saboda haɗa gudunmuwa da ka bat na goron a haɗu a gudunmuwar fan wallahi biki zan karɓa babu babbba ba yaro ba ɗa ba siriki...
Kafin ta kai aya Maryam ta daÉ—e da ficewa saboda takaici.
"To Inna ai duk ba zai gagara ba" Cewar Sammani cikin É—an jin nauyi.
"Allahu akbar kabiran to ai shikenan Allah nuna mana dama da na ga ba wani lokaci za a É—auka ba" Shi dai ba sake cewa komai ba ya saka kai ya fice
Da dare Inna ta sanya aka kira mata mamar Amna da Mamar Abubakar, bayan sun zo sun gaisheta cikin girmamawa ta kalle su a shelaƙe ta ce
"Na kirawo ku ne dan in sanar da ku abin da baku sani ba, idan ma ku ne kuke sonnshiga tsakani na da ƴaƴana to ku sani watan komawarku gidajen iyayenku wato ƙauye za ta ɗauke ku"
Cikin rashin fahimta suke bin Inna da kallo wacce ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana musu kallon ɗai - ɗai
"Inna mai ya yi zafi kuma shi ba wuta ba"