Sashe 11
Kara'in Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na gano ki aradun Allah na gano ki Delu wannan ihun ne da ake mana yake ɓata miki rai amma yanzu zan sa a mana tafi" Cewar Jauro yana matsawa saitin fuskar Inna ya miƙa dogon bakinsa mai kamar na jaɓa, wanda yake da adon gemu fari fat, ya kaiwa Inna wani kiss a kunci, yadda ya buɗe bakin ba ƙaramin wuri bakin ya ci ba a wajen yin kiss ɗin dan sosai ba kuma haɗe kuncin ma baki ɗaya d yake ƙaton baki ne da shi, yana mata kiss ɗin wanda sai da aka yi kamar a haɗo da fatar kuncin dan Inna har haƙoransa ta ji sun gatso fatar amma saboda yadda ya shammace ta da kuma tafin da wurin ya ɗauka shi ne abin da ya bala'in birgeta.
..ƘARA'IN INNA DELU
💄💄💄💄
NA
MAMAN AFRAH
FCW💛
Page 1⃣5⃣➡1⃣6⃣
Yana ɗago fuskarsa wajen ya ƙara kacamewa da ihu da tafi, ihu amma irin ma an burge mutane, kowa gemun ango yake bi da kallo dan ya koma kala biyu sama fari na furfura ƙasan kuma na foundation dan kiss ɗin da ya yiwa amarya Delu gabaɗaya ya gogo foundation a ƙasan gemu, hatta bakinsa da ya doɓara wajen yin kiss ɗin kamar akuya ta ci dusa dan foundation ɗin ce da ta haɗu da gumi ya danɓarota. Shi kuwa Jauro da bai san abin da ake yiwa dariya ba tunaninsa duk kiss ɗin da ya yi ne ya burgesu, dan haka sai ya shiga washe baki.
"Aikin banza ashe ma abu ƙanƙane zan yi ku daina ihun ku koma yi mana tafi, da kun ɗauka indiyawa ne kaɗai suka iya hiss (kiss) Da nuna soyayya ga mace to ni ma da nake rugage gashi nan na yi abin da na caje muku ƙwalƙwalwa, ai dama da rashin kira karen bebe ya ɓata kuɓa da rashin tayi ake barin araha" Cewar Jauro a zuciyarsa.
Inna ma ganin abin da ango ya mata ya ɗau hankalin jama'ar wurin dan ta lura mutanen gari ma sai ƙara tuttulowa suke kamar wanda ake faɗa musu su zo dan yanzu gabaɗaya hall ɗin ya cika maƙil. Ganin haka ya sanya Inna ita ma ta nufi fuskar Jauro dan ya mayar masa da martani aikuwa sai da ta doɓara masa bakinta a wuri uku goshi, kan hanci da kuma kunci. Wani uba ihu da tafi ne ya karaɗe wajen wasu ar da tsalle suke, samari da ƴanmata duk sun fito da wayarsu suna ɗaukan hoto wasu video, su kuma nago da amarya sai daɗi ya cika su ganin kowa son ɗaukan hotonsu yake.
Samari kuwa gani suke sun samu comedy dan wasu videon ma a status za su É—ora wasu kuwa a facebuk wasu a wasu kafar sadarwar dan wanda basu gani ba su ga wannan abu mai kama da almara.
Yadda ake ihu abin har ya so basu mamaki sai dai basu san ba fuskar jauro ce ta bada wani irin abin dariya, dan duk inda Inna ra masa kiss wuraren nan guda uku goshi hanci da kunci sai ya yi abin powder fuskar ya fito a wuraren sai duskar ta zama kamar yadda ake yiwa mota idan za a sake mata fenti a saka mata farin abu yi tabbare tabbataren nan, haka fuskar ta yi da foundation sosai ya koma kamar wanda zai je tashe na iya duba-duba sammadara wanda ake da watan azumi. Lantana ma ta haÉ—e da Æ´an tafi da ihu bata lura da yadda fuskar ango ta koma ba, bare kuma Shattu da ke ta aikin watsa ganye kamar wanda aka ce da ganyen ne auren zai É—auru.
Wani daɗi ne yake baibaye Inna da Jauro idan suka ga wulgawar yellown ganyen mainan nan hakan ba ƙaramin faranta musu rai yake ba sannan suna ƙara tabbatar da cewa su amare ne. MC ne ya fara magana bayan an kashe kiɗan da ya karaɗe wajen.
"Amarya da ango muna muku barka da zuwa wannan waje, sannan muna baku haƙuri a kan faɗuwar da kuka yi wacce sanadinta ya haifar da wata salon soyayya da kuka gabatar mai ɗinbin tarihi a rayuwar aurenku da duk wanda ke wajen nan ya ga yadda kuka nunawa duniya irin yadda kuke son junanku" MC ya kai ƙarshen maganar yana cewa
"Dan Allah a tafa musu" A take wajen ya karaÉ—e da tafi da kuma ihu. Sosai zugar nan da aka yiwa amarya da ango ta shiga kunnuwansu shi kuma MC ya yi hakan ne dan ya fasa musu kai amma a zuciyarsa cewa yake
"Allah wadaran naka ya lalace cewar jakin dawa da ya ga an laftawa jakin gida kaya, banda budurwar zuciya mai sa raƙuma ta auri ɗan tsako ya za a yi tsofai-tsofai da ku, amma ku zo ku kama hall dan shagalin bikin ku, ai Allah raba bawa da wahala wai gwauro a teburin mai shayi" Ya faɗa a ransa a fili kuma ya ce
Dan haka yanzu amarya da ango za su ƙarasa wajen zaman su, su zauna dan mu fara gabatar da abin da ya taramu" Ya kai ƙarshen maganar yana ƙarewa wanda ke zaune kallo wanda duk yawanci ƴan ƙauye ne kuma tsofaffi sai matasan mata haka dan duk samari da ƴan matan ƴan cikin gari ne kumabya tabbatar kallon ƙwaƙwaf ne ya kawo su ba wai gayyatarsu aka yi ba.
Hannun dama Jauro ya kai ya riƙo ƙugun Inna tare da riƙe hannunta da ɗaya hannun nasa kamar yadda jiya da dare ya ga wani actor ya yiwa budurwarsa a film ɗin india. A haka suka nufi kujerar tasu, Shattu na aikin watsa musu ganyen maina.
"Wai bauti (Beauty) Ka ɗauke ni mana yadda indiyawa ke yi " Cewar Inna ƙasa-ƙasa.
"A'a Bebi kinsan dai yadda muka sha ƙasa ɗazu kuma lokacin ma da ƙafafunmu muke tafiya shegiyar rigar nan ta taɗe mu bare kuma a ce na ɗaga ki to wallahi yanzu dai muka ƙara shan ƙasa sai kuma yadda hali ya yi" Shi ma Jauro ya bata amsa a hankali, yadda suke maganar raɗa-raɗa sai ya ƙara baiwa mutane dariya su ala dole ango da amarya a haka suka ƙarasa suka zauna.
Kande da Karime da ke laɓe a cikin wani ɗaki suna hango duk abin da ke faruwa, gabaɗaya kishi ya baibaiye musu zuciya Karime mahaifiyar Kande uwar gidan Jauro ita ce ta kalli Kande ta ce
"Maza ɗauki kwanan shan manjan nan tun da sun zauna yanzu ne dai dai aiwatar da abin da a dace tsaffin banza da basa jin kunya" Ta faɗa tana ƙara ƙyallara idonta ɗaya da yake ido ɗaya gareta. Jan hanci Kande ta yi yare da sanya hannu ta share hawayenta ta ce
"Gaskiya Jauro ya iya cin amana ji yadda ya riƙo ta yana zubar mini da mutunci a idon mutanen ƙauye da rugagenmu " Ta kai ƙarshen maganar tana sakin kukan takaici da na kishi.
"Ki haƙuri ai sai inda ƙarfinmu ya ƙare yanzu dai ki je ki yi abin da n saka ki" Cewar mahaifiyarta. Haka ta fito ta nufi wajen da ya karaɗe da kiɗa wasu har sun fita suna cashewa Kande na zuwa bata yi wata-wata ba ta faki idanun mutane da yake kowa idanunsa na kan masu rawa ne amarya da ango kuma ana zaune da cake a gabansu da lemuka amma in ka kalli fuskar Inna yadda take shaining ɗin foundation ga gumin nan yana ta kwaranyowa shi kuma ango da dabbaren fuskar kashe uku a fuskarsa ga wacce ta mayar masa da gemu kala biyu. Ta bayan kujerarsu Kande ta zo ta ɗaga kwanon sha mai cike da manja ta shiga kwaranyawa a kan ango da amarya tun daga kansu har uban jikinsu bata dakata ba sai da ta juye musu shi tas...
Su Jauro an saki baki an maida hankali kan kiɗa ana kallon masu rawa da juyi basu zata ba basu tsammata ba sai suka fara jin zubar wani abu a jikinsu yana gangarowa har fuskarsu. Inna Delu ce ta juya bayanta dan ganin wanda ke musu wannan aika aikan amma sai ta ga wayam babu kowa, juyawa ta yi ga masoyinta abin ƙaunarta Jauro aikuwa ta yi mugun gani domin kuwa manjan ne ya masa sharkaf tamkar an tsoma kaza a ruwan zafi babu abin da ya so baiwa Inna Delu dariya irin yadda manjan ke zubowa ta gemun Jauron, gurbin idanunsa ne kaɗai ake gani a fuskarsa inda ba manja.
"Badaƙalar nan lallai yau zan nuna wa wanda ya mana wannan aiki wacece ni, tabbas dama a san mutum a san sana'arsa in ya bari a san ya daina, domin kuwa inda ba ƙasa nan ake gardamar kokawa" Cewar Inna a zuciyarta a fili kuwa sai ta kalli Jauro da ya washe bakinsa gemun nan nasa har lokacin yana ɗigar manjan amma wai ita yake yiwa dariya kuma duk abin da ake babu wanda ya lura da abin da aka yiwa ango da amarya dan kowa hankalinsa ya karkata ga rawar da ake a wurin.
Deluna kin ganki kuwa, kin ga yadda kika koma kamar jemage ya faÉ—o daga sama" Cewar Jauro cikin sigar wasa.
"Yo ba gwara ni kamar jemage ya faɗo daga sama ba wallahi idan ka ga yadda ka koma kamar an tsamo ɓera daga ruwa" Ta faɗa tana tashi tsaye dan ta ji haushin maganarsa duk da wasa ya faɗa. Tashin amarya tsaye shi ya sanar da mutane halin da ake ciki kowa ɗaɗɗage yake ya hango amarya da ango dan ya tabbatar da ka ce na cen da ake, ita kuwa Delu bata damu da kallon da ake musu ba kawai so take ta ga wanda ya musu wannan ɗanyen aikin.
Iya ganinta bata ga kowa ba shi ma Jauro haka ya tashi yana dubawa amma ba a ga kowa ba Shattu ce ta kamo hanya daga mazauninta dan zuwa wurin aminiyarta amma kafin ta ƙarasa sai ganin Inna ta yi a fusace ta nufi wajen MC rigar nan sai rinjayarta take rana neman faɗuwa.
Inna na zuwa wajen MC ta warce lasifikar hannunsa shi kuwa saka mata ya yi dan kar ta goga masa manja ta taƙaita shi.