Sashe 8
Kara'in Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Aradun Allah saisa-saisa nake yi Shattu" Ya faÉ—a yana share hawaye dan shi har ga Allah gani yake kamar ma ya É—akko ruwan dafa kansa ne Delun za ta ce ta fasa, shikenan zai rasa zaman birni ya ga samu zai ga rashi, sannan zai mutu da son ta a ransa.
"Rabu da shi Shattu yo ko ɗan taure ne yake awoyin nan ai a sara masa ba wajen kaifin ba, haƙiƙa ka ci amana ta Jauro, kake daɗewa haka kana sunna kenan baka da lokacin tunani na ma, ni ina can a gidan Malam ko yaushe ina tunaninka, ko Malam ɗin ne ya kawo kansa wataran hana shi kaina nake dan sai in ke ganin kamar amanarka zan ci ashe kai kana can kana kashe arnan soyayya, kana kwashe awoyi da mace yo Allah na tuba ai duk ka gama lale komai da komai babu sauran abin da zan samu, ko wani sauran abin da zan mora, har nake zumuɗin cin amarci...
Tana cikin faÉ—a tana kuka, bata ankara ba sai hango wulgawar Abba da Baba ta yi sun fice dan ko ganin tashin su bata yi ba ficewarsu kawai ta gani.
Umaru, Sa'adu" Ta faÉ—a tana ware murya dan su dawo. Amma ko alamarsu bata gani ba.
"Shattu bisu ki kirawo mini su, ki ce wallahi idan basu dawo ba zan yi abar" Ta faÉ—a tana kallon aminiyar tata da gabaÉ—aya ita ma ranta a jagule yake da maganar Jauro.
"Ki bar maganar yin abar ke baki da aiki sai anbaton za ki yi abar, to meye ribarki in kika tsinewa Æ´aÆ´anki?" Cewar Shattu tana kallonta.
"Ke ce miki aka yi Delun mahaukata ce ni, ai ba wai yin tsinuwar zan yi ba ina faÉ—a ne dan in samu cikar burina kin san tsinuwar ce kaÉ—ai zan ambata a mini abin da nake so a zauna lafiya" Cewar Inna cikin raÉ—a dan kar su Abban ko suna kusa su jiyo ta.
"Yawwa ko da na ji" Bari in bi bayansu" Shattu ta faɗa tana ficewa da sauri dan kar kowannen su ya shige ɓangarensa.
Tana fita Jauro ya matsa kusa da Inna ya kamo hannunta ta ƙwace, ganin za ta ɓata masa lokaci ya haɗa duka hannun biyu ya riƙe ya shiga aikin lallashi tana ta zunɓura baki ta ce
"Haka kurum ka je kana cin amanar soyayya ta"
"Haba Delu fara kyakkyawa wallahi kina raina, kuma da kike maganar ba na tunaninki, wani lokacin ko ina kan masai(Toilet) Ina kashi sai in ji tunaninki ya hana ni sakat, ke ko sallah nake ma tunaninki nake"
"Ka ce ɓata sallarka kake"
"A'a ba haka bane ai ina cewa a'uzubillahi minashshaiɗanir rajimmm, in kori shaiɗan ɗin kawai dai ina so ki san irin yadda kika yi kane-kane a raina, ke ni fa akwai lokacin da Harɗon rugarmu ya aika a kirawo ni wai dabobina sun shiga gonarsa, tun da na doshi fadar tasa kawai sai na ga ya koma mini ke sak, kawai ke na gani a kan kujerar mulkin dan haka tun da na kalleshi sai nake sakin murmushin ƙaunayya aikuwa ya harzuƙa, ina zama yake faɗa kamar ya cinyeni ɗanye, ni kuwa tun da na sunkuyar da kai tunaninki kawai nake, dan haka faɗan da yake mini ma amon muryarki nake ji kina mimi kalaman soyayya dan haka ko da ya saurara da faɗan ya ce da kai fa nake Jauro ka ƙyaleni ai ina ɗago kaina ban san lokacin da na ce ina jinki Deluna"
Gabaɗaya Inna ta tuntsure da wata irin dariya sai ƙyaƙyatawa take ita ala dole Jauro yana tuna ta duk daɗi ya cika ta.
ƘARA'IN INNA DELU
💄💄💄💄
NA
MAMAN AFRAH
FCW💛
Page 1⃣1⃣➡1⃣2⃣
Abba ne ya yi gyaran murya ya fara magana kamar haka, dan ya ga abin na su Inna ya wuce gona da iri nema suke su É—akko musu magana su É—akko musu ruwan dafa kansu.
"Hana Inna wannan abu fa ba mai yiwuwa bane, saboda abin da zai iyu shi ake faÉ—a ta yaya ma haka zai faru a ce wai mu kama É—akin taron shagali ai sai duniya ta zage...
"Idan fa ban yi da gaske ba, ba zan taɓa samun abin da nake so ba gwara dai in tauna tsakuwa ko aya ta ji tsoro" Cewar Inna Delu a zuciyarta a fili kuma sai ta ce
"Yanzu Sa'adu ni kake faɗi in faɗa dani, ni kake cewa ba mai yiwuwa bane, haka zan tare a ɗakin sabon uban naka babu wani shagali kamar wacce ta yi auren ƙiyayya, yo in ba auren ƙiyayya ba a ina aka taɓa biki lami shataf babu wani ɗanɗano, ai ko auren ubanka Malam duk da ba son sa nake ba sai da aka ɗakko masu gurmi" Ta katse masa maganar tana kaiwa ƙarshen maganar tare da fashewa da wani kuka mai sauti kamar an kunna jiniya, tana fara kukan Jauro ya yi saurin ruƙo hannunta yake bata baki amma ko saurara wa da kukan bata yi ba ganin haka shi ma sai ya ɓare baki ya saki nasa kukan yana ƙwalawa da ƙarfi har wani jan birki yake sai kuma ya ci gaba.
Shattu ma bata yi ƙasa a gwiwa ba ta ƙarasa wajensu tana basu baki
"Haba amarya da ango ya da kuka kuma a ranar farincikin ku, ranar da kuka yi shekaru sama da hamsin kuna mafarkin samunta"
"Barmu mu yi kayanmu Shattu ɗan yanzu ni ka haifeshi baka haifi halinshi ba, in banda zamani mai sa wani ya ƙi uwarsa ya so wasu, zamani mai sanya ɗa ya baƙantawa uwarsa rai ya farantawa uwar matarsa rai, ta yaya za a ce kamar ni in haifi yaran na su girma su mallaki hanklin kansu amma su ƙi mini abun da zai sa ni farinciki" Cewar Inna tana goge hawayen takaici. Ganin haka sai Jauro ya miƙa goshinsa ya haɗa da goshin Inna a haka suke kukan kamar wasu tsuntsaye.
"Muke kukan a haka Bebi in gwara duk runtsi duk wuya mu zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya" Ya faɗa yana ƙara sautin kukansa.
Shattu ma ganin haka sai kawai ta mara musu baya dan ita ma tana ganin ba a barta a baya ba wani irin kukan tsoffi ta saki irin mai sanya ciwon kai lokaci guda. Sun cika É—akin da koke -koke kamar gidan mutuwa, baka jin komai sai sautin kukansu babu mai lallashin wani.
Idan Inna ta bada sautin
"Yiiiiii"
Sai Jauro ya bada sautin
Yeeeee"
Ita kuma Shattu nata sauti
"Yeyiye-yiye" Kamar wata agwagwa haka suke kukan suna jan hanci.
Abba da Baba kawai kansu suka sunkuyar hannuwansu dafe da kansu.
"Ya Allah ka bamu ikon cin jarabawar nan" Cewar Abba a zuciyarsa.
"Kai ji nake dama bana ƙasar nan Inna ta yi aure da wataƙila ba zan ji takaici kamar haka ba" Cewar Baba a zuciyarsa yana jin wani damshi a fuskarsa hannu ya kai ya shafo ashe dai hawaye ne suke gangaro masa.
"Bari dai in tashi mu san inda dare ya mana yaran nan in basu ga da gaske nake ba babu abin da za su yarda su mana" Inna ta faÉ—a a ranta tana mai tashi ta nufi É—akin har lokacin tana kuka mai sauti, su ma su Shattu basu bari ba an ma rasa sautin kukan wa za a saurara kamar wasu yara.
Ƙaran akwatunan da Inna ta ɗakko guda biyu su ne suka dakatar da kowa aka shiga kallonta har masu kukan ma ɗiff suka yi dan dama kukan sheƙiyanci ne. A kanta ta ɗora akwatin ɗaya yadda kika san irin inyamuran nan na Lagos masu ɗora daro a ka haka ta koma, tana janye da ɗaya akwatin a hannunta
"Kai wannan mata da shegen abu take kin ga ni ban samu shagalin biki ba za ta jaza mini komawa ruga bayan na yi sallama da zaman can" Cewar Jauro da bai san ma lokacin da kukan munafurcin da yake yi ya tsaya ba, banda faÉ—uwa babu abin da gabansa ke yi.
"Kin mini dai dai gwara ki tarki tafiya ko sa saduda su sakko" Cewar Shattu a ranta.
Cikin hanzari Jauro ya tashi ya karɓi akwatin kan Inna ya sauke ta ƙasa sannan ya koma ya zauna yana share hawaye, amma a baɗini hawayen baƙincikin barin binni ne dan ya ga Delu da gaske take tun da har ta ɗakko akwati.
"Ku taso mu tafi mu bar musu gidansu" Cewar Inna tana saurin dafe kanta jin É—aurin É—ankwalin na neman faÉ—uwa.
Wani zillo gaban Jauro ya yi jin maganar da ta ratsa kunensa a kiɗime ya ɗago yana kallon amaryar tasa ji yake kamar ya ce su haƙura da shagalin su tare a haka amma kuma ya ga babu fuska a wajen Inna.
"Ni dama a shirye nake aminiyata dan dai nan da garinmu ko a ƙafarmu ma isa daga yanzu zuwa sulusun dare kan gari ya waye" Cewar Shattu da ta ɗauki akwati ɗaya.
"Bebi taso ka É—auki É—ayar"
"Ga samu ga rashi wayyo ni Jauro duk na É—aga dabbobina da shanaye da gonaki na siyar yanzu idan na koma gorin jama,a ma ya ishe ni" Cewar Jauro a zuciyarsa yana tuna washe garin ranar da Inna ta dawo binni aka É—akko shi har za a É—aura aure aka fasa shi ne da ya koma ya siyar da duka kadarorinsa.
"Ina zamu???" Cewar Jauro har lokacin yana zaune a kujera dan ko maganar tafiyar ma baya ƙaunar ji.
"Ka taso mana, baka gani yanzu dare ne kuma akwai gidan casu a garin nan akwai kwalob (Club) Akwai gidan karuwa kai sai inda muka zaɓa sai mu je mu yi casunmu in yaso daga can sai mu koma rugarku mu yi rayuwar aurenmu a can tun da nan an gagara kama mana gida a sirri ai sai mu je inda ƴan iskan duniya suke in yaso tunda su suna gudun maganar, a ce sun kamawa uwarsu ɗakin taro an yi shagali ai a ce an ga uwarsu a gidan rawa " Cewar Inna tana saurin ƙara dafe kanta jin kofin da ta yi acuci zai gangaro aikuwa dai an yi rashin sa'a dan ya faɗo ji kake ƙwal, ya faɗowa Abba a tsakiyar kansa da babu hula.