← Book details Kara'in Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 18

Sashe 2

Kara'in Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai Umaru sa idanunka cikin nawa da kyau aure na ya fi ƙarfin wai, dan wallahi ko budurwa dal a leda ba za ta cewa aure na wai ba, dan aurena dai dai yake da nata na saurayi da budurwa wataƙila ma nawa ya fi armashi da moruwa ko dan saboda tsohuwar zumar soyayyar da nake yiwa wanda zan aura ɗin, soyayya ce mai ruwa-ruwa wacce ta daɗe tana iyo a cikin gogin raina, duk ta bi ta sanya mini rauni a zuciya kunsan so da raunana zuciyar mai yinsa duk girman mutum sai ya so ya mayar masa da zuciyarsa ɗanya sharaf kamar ta jaririn da ya sunkuto daga mahaifar uwarsa yanzu...

"Inna!!!" Cewar Sa'adu da ya miƙe tsaye kamar an tsikareshi yadda furucin Innar ke masa dirar mikiya a kunnuwansa shi kansa bai sa ya tashi ba sai ganinsa ya yi a tsaye cankarkar.

"Sa'aduuuu" Ita ma ta faɗa tana miƙewa tsaye har zaninta na kuncewa ta kama ta ɗaureshi gamgam.

"Inna maganar auren nan ki daina yi dan Allah ko daɗin ji ma babu yanzu dan Allah a ce daga gama takaba da sati biyu sai ki ce wai aure za ki yi, mahaifinmu ko shekara bai yi ba a ƙasa amma dan Allah Inna da girmanki a ce wai kina maganar ƙara aure.

"HHHH na dawo in ji ɗan yawon duniya yo Umaru cewa za ka yi marigayin ubanku kuke tayawa kishi bayan yana can rufe a cikin ƙasa,Allah na tuba a nunawa na ringingine farin wata, yo kalle ni da kyau ka gani dangargar nake ji na kamar saurayi sabon balaga, amma kowa dama da kiwon da ya karɓeshi maƙocin mai akuya ya sayi kura, ni babu ni babu Malam Lawwali mahaifinku, mutuwa ce ya mutu tsakaninmu kuwa takaba ce ko a musulunci idan na gama takaba ko da kwana ɗaya ne zan iya yin aure, babu inda addini ya haramta kuma addini ba ruwansa da tsufana, ko akwai wanda zai faɗa mini inda aka haramta auren tsohuwa???" Ta jefa musu tambayar tana tsatstsare su da ido. Babu wanda ya tanka dan sun rasa bakin magana.

"Kun gani, baku da amsa to tunda ba faɗin Allah bane ba na ma'aikinsa ba babu wanda zai taka mini birki duk cikin ku, in banda ma sabo da yi gawa da gatsine ina za a haɗa wanda ke doron duniya da kuma wanda ke can ƙasa a ƙumshe ya gama zagwanyewa...

"Inna fata nagari lamiri"

"To na ji ubana Umaru in kuma duka zaka saka to aiki Maryama ta samo maka kirfo(Bulala ko madoki)"

"Ni ba haka bane amma gaskiya ki janye maganar aure dan duk wanda ma ya ji maganar nan mu za a zaga a ce mu ne Æ´aÆ´anki muna gani...

"Yo a faɗa mana zagi kuma a zageku tun da dai zagi baya fitowa a jiki,duk da an ce ba a ƙin ta mutane wai an ce wa ɓarawo ya gudu, amma ni dai na san duk wanda ma ya zage ku ya ɗauki alhakinku dan ni ce mai aure, sai ka ce wanda na ce zan fara karuwanci, to aure dai kuma babu wanda ya isa ya taka mini birki duk duniya sai dai in ni Delu bana numfashi" Ta faɗa tana bugar ƙirjinta.

"Haba Inna wai shin mai kike so mu miki? Mai kika nema kika rasa da zaki mana wannan abin dan Allah " Maryam ta faÉ—a tana sakin kuka.

"Maryama goge hawayenki kar ki yi asarar zubar da su, dan indai dan in saduda ne in ji tausayinki to ba zan ji ba tun da ni ma baku ji tausayina na luguden da zuciyata take yi ba, kullum bugawa take tana kiran Jauro, Jauro, wallahi auren ƙara'i dai tsakani na da jauro babu fashi har sai na ji an ce alfatiya, sannan hankalina zai kwanta duk wanda kuma ya ce zai hana ga wurin nan dan ta yaro kyau take bata ƙarko!"

"INNA zan biya miki umara idan kika fasa auren nan" Sa'adu ya faɗa da ƙarfin gwiwarsa dan sai yanzu ma ya tuna lagom mahaifiyar tasu, dan tana mutuwar son zuwa makka duk da ta je ta koma.

"Yanzu dai na je hajj ita ce farilla, umara kuwa zuwana ya fi a ƙirga to ko ban taɓa zuwa umara ba gwara in auri Jauro wataƙila ya mini tukuici da amarcin darenmu na farko ya biya mini umarar " Ta faɗa tana ɗan darawa

Da sauri Sa'adu ya zauna daɓas jiki ba ƙwari dan yana ganin mahaifiyar tasu ta yi nisa ba lallai ta ji kira ba!

🤚😃🤚😃🤚😃🤚
ƘARA'IN INNA DELU
💄💄💄💄

NA

MAMAN AFRAH

ƘARA'IN INNA DELU
💄💄💄💄

NA

MAMAN AFRAH

FCW💛

Page3⃣➡4⃣

"Inna kamar yadda kike da haƙƙi a kan mu, na mu miki abin da kike so mu ma fa muna da haƙƙi a kan ki, dan haka daga cikin haƙƙoƙinmu da ke kan ki, kar ki zubar mana da mutuncinmu tare da ja mana zagi a gari" Cewar Baba Umar yana ɓata rai tare da kauda kai gefe.

"Au Allah, Umaru to tsakanin haƙƙin uwa da haƙƙin ɗa wanne ya fi ƙarfi, ba cewa aka yi a yiwa uwa biyayya har sai da Allah ya faɗa sau uku kafin ma a ce a bi uba kuma sau ɗaya Allah ya faɗa, to ka ga ba a haɗa ni da ubanka Malam ba ma a wajen yi mana biyayya bare kuma a haɗa ni da kai, kuma idan maganar zagi ce an daɗe ba a zage ku ba amma ku sani aure wallahi tallahi babu fashi sai an ɗaura shi, sai dai ɗan baƙinciki ya mutu arqur'ani kwa" Ta faɗa tana tafa hannu a cinya tare da komawa mazauninta ta zauna tana hararar Maryam da ke ta sharar ƙwallah.

"Ke matsa daga kusa dani uwar ƴan arahar hawaye, dan uwaki za ta ƙara aurar sabon miji ki samu wani uban ki huta da maraici shi ne kika zauna kina kuka kamar dai an ce na mutu, ko kuma an ce ke za a yiwa kishiyar" Inna ta faɗa tana taɓe baki.Maryam kuwa kamar Inna ta zuga ta sai kawai ta ƙara volume ɗin kukanta.

"Affafadaran to wallahi sai ko in kin koma gidanki mijinki ya yi aikin lallashi, ko in kin je ya ga idanunki luhu-luhu ya tambayeki dalilin kukan, kin ga sai ki ji daɗin ce masa Inna ce ta samu bazawari son kowa ƙin wanda bai samu ba za ta galla aure shi ne kike kuka kin ga sai ya ce baƙinciki kike mini" Ta faɗa tana miƙa hannu ta ɗauki ledar goranta a kan kujerar ta since ta ɗauki ɗaya ta mayar ta ƙulle ta ɓalgata ta shiga taunawa hankali kwance.

"Inna!"

"Umaru"

"Inna ki janye maganar auren nan" Ya faɗa cikin ɓacin rai da murya mai kamar yana bata umarni.

"Iko sai rabbani Umaru ni kake aikowa saƙon harara, kamar wata kishiyar uwarka, to na gode, amma ba bansan harara ba sai dio ya faɗu, kuma in ce dai ka fitar da ni daga matsayin uwarka, shi yasa kake wannan muzuran har kana bani uwarni kamar kai ne uwar ni ce ɗan, to wallahi ko ubanka Lawwali, zai dawo daga lahira bai isa in fasa auren nan ba bare kai cacakurukuci cikon banci, banda ma rashin tunani ni da aka mini auren dole da ubanku na haƙura na zauna da shi shekara da shekaru da ƙiyayyarsa a zuciyata kuma yanzu dan ya margaya(mutu) Sai a hanani rawar gaban hantsi"

"Inna ba na son maganar auren nan gaskiya matsawar dai mu ne ƴaƴanki to dole ki haƙura" Baba ya faɗa yana kallonta, shi dai Abba tun da ya zauna bai kuma magana ba.

"Umaru, biyani nono na da na shayar da kai, aradun Allah gwara na sheƙa masa ruwa na yi kindirmo(Nono) tun da ni kake so na maka biyayya ba wai kai bane za ka mini biyayya ba"

"Ni ba haka nake nufi ba"

"Yo in ba haka kake nufi ba menene ba dai ni bace kake rainawa har muke faɗi in faɗa, to ni kuwa ni ce ƙofar shigarka aljanna, ka ga wannan ƙafartawa mai faso da kaushi kana ganinta kamar kofaton doki wallahi ita zan ɗaga ka shiga aljanna" Ta faɗa tana ɗage ƙafarta ta nuna masa.

Gabaɗaya sun kasa gane ta inda za su ɓullowa Innar kowa sai ya zuba mata ido tana ta taunar goro abinta, zuwa can, Abba Sa'adu ya zamo daga kan kujera ya nufi wajen Inna da rarrafe, shi ma Baba Umar sakkowa ya yi ya nufi wanjenta gwiwarsa a ƙasa yana rarrafe, Maryam ma ganin haka sai ta sakko daga kujera ta durƙusa a kan gwiwoyinta. Su duka kuka suka saka mata kamar ƙananan yara, Inna kuwa baki sake take kallonsu dan ko a jikinta kukan da suke ita dai aurenta na ƙara'i babu abin da zai sanya ta fasa.

Ai Inna ma sai gani suka yi bidik ta sakko ƙasan ta durƙusa kamar yadda suka yi gabaɗaya sai kowa ya tsayar da kukan da yake suka shiga kallonta. Fashewa ta yi da wani irin kuka mai jiniya wanda ya fi nasu su duka ukun, tun da ta ɓare bakinta bata rufe ba kuka kawai take zabgawa kamar wanda aka bata umarni. Yin nan take babu ƙaƙƙautawa sun rasa ma bakin magana.

"Inna menene" Maryam ta yi ƙarfin halin jefa mata tambayar cikin shaƙeƙƙiyar muryarra da bata fita sosai saboda kukan da ta yi. Maimakon Inna ta bata amsa sai kawai ta ƙara gudu da kuma ƙaran kukan nata.Tun suna lallashinta har suka yi shiru gabaɗaya tausayinta ya kama su dan su duk tunaninsu ko iyayenta ta tuna take kukan, falon ya yi tsit baka jin komai sai kukanta zuwa can.

"Dan Allah Inna ki daina kukan nan baki ji ba yadda duk kika karya mana zuciya, su kaka babu abin da suke buƙata sama da addu'a" Cewar Baba yana kallon Inna da tausayawa.
"Ba batun mutuwa bane ɗan nan, duk da an ce ana bikin duniya ake na ƙiyama amma yau dai iya duniyar ne"

"Ikon Allah, ba su kaka kika tuna ba dama" Abba ya jefa mata tambayar.

"Allah sarki Inna Baba Malam ta tuna ai dama ko ba komai akwai sabo sa...
Chapter 2 · 0% Book details