← Book details Kara'in Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 18

Sashe 6

Kara'in Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyawar da Abubakar zai yi aikuwa Inna taku ɗaya biyu ta yi fisgoshi, ji kake ƙiii ta maido dashi baya ta hanyar riƙo wuyan rigar jikinsa, sai da ta kawo shi gabanta sannan ta damƙe wuyan rigar da hannu ɗaya, ɗaya hannun ta dunƙule ta dage ƙarfinta na tuwo ta duma masa dundu a baya sai da ta masa dundu kifi uku sannan ta ce

"Ko ubanka Sa'adu ya yi kaɗan ya yiwa goron ɗaurin aurena da Jauro wannan dangwararwar yo Allah na tuba ba gwara ka ce Inna kwanta a ƙasa ba idan na kwanta ka fisgi ƙafata riiii har sai ka dangana ni da ƙofar gida, ai sai ya fi mini sauƙi a kan yadda na ji da ka yiwa goro da alewar ɗaurin aurenmu da Jauro riƙon sakainar kashi tare da dangwarar da su kamar an maka dole" Ta faɗa tana sakin rigarsa da ta riƙe wanda wurin gabaɗaya ya cukurkuɗe kamar an fito da rigar daga bakin kura.

Wani takaici ne ya rufe Abubakar ganin abin da kakarsa mahaifiyar ubansa ta masa a cikin mutane, dama ransa a matuƙar ɓace yake na auren da ta yi, dan abin kunya tsofe-tsofe da ita duk ta yi yaba amma wai za ta yi auren ƘARA'I. Wani irin kumburo baki ya yi yana wani huhhura hanci ya juya yana wani fisfisga ya fice daga falon.

"Au ko da na ji, she dai an É—aura wallahi har gabana ya faÉ—i" Cewar Shattu tana buÉ—a ledojin.

"Rabu dashi ɗan kan uwa, an ɗauremu ni da Jauro, mugun hali ne irin na uwarsa, baƙinciki suke da auren sun fi so na zo mutuwa ana cewa matar marigayi ce haka kawai ai gwara a ce ka mutu da mijinka duk da ba a san gawar fari ba" Ta faɗa suna ɗaukar ledojin shiga rabawa mutanen da suke falon, dan dama duk daga ƙauyensu suke Shattu ta gayyato mata su, haka suka shiga rabawa mutane bakin Inna dan dama duk tsofaffi ne bakin Inna har kunne yau dai burinta ya cika, ɗaki ta shiga ta ɗakko wata shadda ƴar ubansu ta saka ta cakara ɗaurin ɗankwali har ta yi gwaggwaro ta koma ta ware ta ɗauki wani kofi a cikin ɗakin ɗan ƙarami da shi ta ɗora a tsakiyar kan nata tare da ɗaura ɗankwalin a kan kofin mudubi ta kalla aikuwa ɗaurin ya mata yadda take so.

"Ai gwara dai yau ɗaya in yi ƘARA'I in yi ɗaurin ɗankwali irin na yaran ƙauyenmu da suke wanda ake cewa a cuci maza"Cewar Inna tana dubawa ta ga ya yi kamar yadda yaran ke yi. Ƙaramar lokar mudubin ɗakin ta janyo ta ɗakko fanfas na yara guda biyu, jimƙe ɗaya ta yi ta ɗaga bireziyarta ta saka fanfas ɗaya a ƙasan nonon nata sai ta maida nonon ya zamana shi ne a akan fanfas ɗin ɗayan ma haka ta masa tun da ta zubawa jikinta da fuskarta ido a mudubi take ta faman doka murmushi, walwala ta kasa barin fuskarta.

"Taɓ lallai na yi maida tsohuwa yarinya ni Delu ai za mu kwashi ƙara'i ta faɗa tana washe bakinta har haƙorin makkarta ya bayyana.

Hanyar fitowa daga ɗakin ta yi domin ta san yanzu Jauro yana dab da zuwa, tana fitowa hakan ya yi dai dai da wata uwar guɗa da Shattu ƙawarta ta carara ba komai ya kawo guɗar ba kuwa sai shigowar Jauro falon shi da abokinsa Mati. Tunda ya shigo yake wuwulga ido ya ga ta inda zai ga Delunsa.

"Shattu ina amaryar take?" Ya faÉ—a yana washe bakinsa.

"Baka gane ni ba" Cewar Inna Delu tana wani farrr da ido ita ala dole amarya.

"De, De,Delu" Ya faɗa idanunsa a waje baki sake yana nuna ta da yatsansa. Kowa ma na falon maida kallonsa ya yi kan Inna Delu ganin ɗaurin ɗankwali mai acuci gashi fanfas ɗin da ta saka ya ɗago da nonon nata sai suka hayo ƙirji hakan ya sanya ta zama kamar yarinyar mace dan sosai fandas ɗin ya yi ɗoɗar a cikin shaddar.
"Wallahi Delu kin fiye mini Kande sau miliyan" Cewar Jauro yana kallonta baki sake.

"Ai baka haɗa bama Jauro" Cewar Mati yana ƙarewa Inna Delu kallo a ransa yana rayawa ina ma a ce shi ne ya yi wannan dacen tsuntsu daga sama gashasshshe, dan ya matuƙar so a ce shi ne musamman ma da ya ji wai a binnin a wannan ƙerarran gidan Jauron zai zauna da Delun dan ɗaurewa ƙarya tsantsa ma har da ɓangaren da zai saka matarsa Kande dan Kanden ta tada badaƙala cewar ba zai tafi binni ya barta a ƙauye ba ita kuma Inna da yake so take yi tana ganin mijinta kullum sai ta saka aka gyarawa Kande wani ɗaki ciki ɗaya daga can gefe yake.Ita kuma Kanden saboda son zaman binni take gani ba za ta yi saki na dafe ba gwara dai ta zo ko a akurkin kaji ne ta zauna.

"Kai jama'a wallahi na tsinci dami a kala" Ya faÉ—a yana shafo farin gashin gemunsa.

"Ai yau sai ka biya mu kwalliyar nan Jauro ango" Cewar Shattu tana washe bakinta wanda ta tauna goro.

Baki ya washe ya ce

"Ai in kin ji biya ma ɗaya kenan, kar ki samu damuwa aminiyar amarya sha kuruminki, kwantar da hankalinki kamar kin kashe ɗan mutum, ko kamar tsumma a randa" Ya faɗa har lokacin idanunsa a kan amaryarsa. Nan aka shiga gaisawa da mutanen ƙauye da suka zo domin ɗaurin aure, da la'asar suka koma garinsu dan Inna ta ce sai nan da sati guda za su zo shagalin biki dan yanzu aure kawai aka ɗaura dan hankalinta da na Jauro ya kwanta.

Da daddare bayan sallar isha'i Inna ta aika aka kirawo mata Abba Sa'adu da Baba Umar a kan tana son magana da su, cikin bin umarninta suka taho a tare sa sallama suka shiga lokacin ta É—aga waya za ta kara a kunne, sai da ta msa sallamar tasu ya musu izinin shiga sannan ta kara wayar a kunne

"Alo Jaurona ango" Ta faɗa tana wani murmushi tare da kashe murya kamar wata ƙaramar budurwa.

Daga ɗaya ɓangaren Jauro ya ce

"Amarya, amarya, amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida" Cewar Jauro yana waya dariya da sautin dariya ya karaɗe kunnuwan Abba da Baba, da yake bolum ɗin wayar a ƙure yake ana iya jiyo maganar tasa.

"Angona kenan bada kan ka a sare ka je gida ka ce ya faɗi, ina ƙaunarka Jaurona"

"Ai kin zama mallakina yanzu Deluwa maƙwallaton zuciyata"

Gabaɗaya Abba da Baba kai kawai suka sunkuyar saboda tsabar kunyar da ta ziyarce su a ce uwarsu mahaifiyarsu ta yi sabon aure yau kuma tana wayar soyayya har da kalamai kamar wata farin shiga, ƙaramar yarinya ko nauyinsu bata ji.

"Ka zo ɓangarena za a yi magana kan shagalin bikinmu" Ta faɗa tana ƙara kashe muryarta har da wani lanƙwasa muryar kamar wani lauje.

"Yanzu kuwa" Ya faÉ—a yana kashe wayar ya taso zai taho.

Ajiye wayar ta yi har lokacin murmushi bai bar yamutsatstsiyar fuskarta wacce tun tuni tsufa ya yiwa kamun kazar kuku. Dakyar ta iya dakayar da murmushin, ta kalli ɗiyan nata ta ce bari Baban naku ya ƙaraso dan na fi so a yi maganar shagulgulan bikin namu a gabansa ko yana da wani tsare-tsaren shi ma"

Baki sake Æ´aÆ´an nata suke kallonta fuskarsu fal mamaki.

"Umaru, Sa'adu wai ko bakwa son albarkar iyaye ne, ya ina maganar abin da zai saka ni farinciki kuna wani kauce kauce kamar wacce ta faɗi saɓon Allah, aure ne fa ba haramun ba sunnar ma'aiki" Ta faɗa tana kama haɓa cike da mamaki dan ita har ga Allah a kan gaskiyarta take.

Da sallama Jauro ya shigo wanda hakan ne ya katse musu maganar, amsa masa ta yi ya ƙaraso zai zauna a kujera mai zaman mutum ɗaya.

"Haba Jaurona matso kusan iyalinka mana ka zauna a nesa da ni" Cewar Inna da ke zaune kan kujera mai zaman mutum biyu, su Umar suna ƙasa daga gabanta, haka ya ƙaraso yana wani washe baki yana wani baza babbar riga kamar wanda ke baza buhu a kasuwar barkono. Kusa da ita ya zauna suka zauna da ita dab da juna da ido ya kafe ta yana mata wani kallon soyayya dan ya kasa ɗauke idanunsa daga kan ɗaurin ɗankwalin acuci mazan da ta yi sosai ta masa kyau.

"Barka da dare" Umar da Sa'adu suka faÉ—a, wanda hakan ne ya dawo da shi daga hayyacinsa daga kallon da yake yiwa uwarsu, amma bai É—auke idanun daga kallonta ba, amsawa ya yi ba tare da ya kallesu ba har lokacin yana kallon Inna Delu.

"Kallon fa" Ta faÉ—a tana rufe fuska da tafukan hannayenta alamun kunya.

"Wallahi bana gajiya da kallonki Deluna, sosai ɗaurin nan ya miki kyau ya ɗauru sosai kamar an ɗaure itace da igiya ɗaurin ya zauna daram ga wani ɗan tozo da ya yi irin na yara, sai kika dawo mini ɗanya sharaf kamar kina budurwa sai yau nake ƙara jin haushi da ba ni na aureki ba, na so a ce ni ne nan na buɗe ki a leda lokacin kina sabuwa dadal, amma Allah bai yi ba sai yau da kike da shekara saba'in" Ya faɗa haƙoransa washe gabaɗaya talatin da biyun a waje.

ƘARA'IN INNA DELU
💄💄💄💄💄

NA

MAMAN AFRAH

FCW 💛
Pag 9⃣➡🔟

Wani daɗi ne ya lulluɓe Inna Delu jin irin yabon da angon nata ke mata, ƙuri ta masa da ido tana kallon fuskar nan tasa mai yalwar furfurar gashin baki da saje. Dai dai nan Shattu wacce ita kaɗai ce bata tafi ba saboda ita ce aminiyar Delu wai sai bayan shagali za ta tafi, shigowa ta yi ganin kallon da Delun ke jifan Jauro da shi sai kuwa ta carara wata uwar guɗa, guɗar da ta carara ce ta sanya Delun sanya hannu ta rufe ido.

"Ikon Allah ga zara ga wata" Ta faɗa lokacin da ta shigo tare da ƙarasowa ta tsaya fuskarta da fara'a
Chapter 6 · 0% Book details