← Book details Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 22

Sashe 9

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Na fahimta. Amma kuma ya aka yi matarka ta yi girki yau. Ita da bata da lafiya. Ko dan manta da wanan batun, ai lafiya ta Allah ce, haka ma jinya, zai iya ɗorawa kowa ya kuma sauƙe masa s sanda ya so, haka ne ba?”

Ya tambaya yana ɗage masa gira. A tsorace Eze ya gyaɗa kansa.

“Eh haka ne. To amma me ya sa baka sanar ba. Ai ya kamata ace ka sanar da mu. Yanda matarka ta iya girki irin wannan ai ya kamata ace na je na dubata!”

Eze ya kuma haɗiye miyau. Sannan yace.

“Sir! Sir”

“Ya isa. Na san haka kawai ka ƙi zuwa duty. Kuma wannan abincin bai isa ya hanani sakawa a maka hukunci ba. Dan haka ka je wurin lieutenant Bala, ka ce na ce a maka bulala hamsin!”

A take Eze ya fara rawar tsoro, hawaye suka zibo masa.

“Sir dan Allah ka yi haƙuri. Na tuba Sir, ba zan sake ba!”

“Hamsin ta yi yawa. Tun da ka haɗani da Allah ka je a maka talatin. Idan ka kuskura ka sake magana kuma zan sa a ninka maka ita, daga talatin zuwa wasu masu kamarta sau uku. Na san ka iya lissafi!”

Eze ya ja bakinsa ya yi shiru. Ya sara masa a tsorace, sannan ya juya ya fita daga sashen office ɗin nasa. Mu'az na tsaye a ƙofar office ɗinsa yana cin abinci Faruk ya shigo.

“Yanzu ba za ka iya haƙuri ka ci a zaune ba MJ?”

Mu'az ya kalle shi yana cusa loma a bakinsa. Kafin ya miƙa masa containern.

“Za ka ci ne?. Amma fa kayan haram ne, cin hancinsa aka kawo min!”

Faruk ya yi murmushi yana girgiza kai.

“A ci daɗi lafiya. Ni ba na ci”

Ya faɗi yana shirin wucewa, amma sai Mu'az ya dakatar da shi.

“Daddy yace yau yana son ganinku a gida kai da Mariya!”

Cak Faruk ya tsaya. Sannan ya juyo ya kalle shi.

“Fatan dai ba wani abin ne ya faru ba?”

Mu'az ya girgiza kansa alamun bai sani ba.

“To Allah ya kaimu an jima ɗin. Zamu zo”

“Sai kun zo”

Mu'az ya faɗi yana shiga office ɗinsa. A kan table ya aje containern da ya cinye abin ciki tas. Sannan ya shiga banɗaki ya wanke hannunsa da bakinsa. A sanda ya dawo cikin office ɗin ya ja ya tsaya yana kallon Yasmin da bai ji shigowarta ba. Yasmin na ganinsa ta miƙe tsaye.

“We need to talk MJ!”

“Bani da wannan lokacin Yamin. Na sha faɗa miki cewar kada ki sake zuwa office ɗina. Bana tattauna abubuwan da suka shafi rayuwata a office, ki bari idan na koma gida sai ki zo mu yi magana!”

Ya kai ƙarshe yana zaunawa a kan kujera. Takaici ya sa Yasmin cewa.

“A nan nake so mu yi maganar, saboda bana jin za mu sake haɗuwa bayan yau!”

“Mutuwa za ki yi ke nan?. Yasmin bai kamata ki kashe kanki a kan wanda bai damu da ke ba!”

Yasmin ta kai hannu ta goge ƙwallar da ta zubo mata.

“Ko kaɗan ban taɓa tunanin kashe kaina ba, domin kuwa da ace zan yi hakan da na yi tuntuni. Nan da next week zan tafi Cairo, zan je na ƙarasa makarantar da soyyayarka ta hanani ƙarasaww!”

Mu'az ya yi dariya.

“Da kuwa kin taimaki kanki”

Yasmin ta kuma goge ƙwalla.

“Mu'az ya kamata ka ji tsoron Allah. Ko da kaɗan ne ya kamata ka nuna kulawa ga wanda yake sonka...”

Ya nuna kansa yana faɗin.

“Ni? Ni kuma me na yi bawan Allah?”

“A'a, ba ka yi komai ba, ni ce wadda ta yi kuskuren fara sonka, har ina zaton cewa wata rana kai ma za ka fara sona. Ashe na aikata babban kuskure. Mu'az ina maka addu'ar Allah ya ɗora maka son da zai wahalar da kai. Allah ya sakawa zuciyarka son da zai sa ka yi ƙoƙarin kashe kanka. Allah ya sa maka son wadda za ta hana rayuwarka sukuni, Allah ya saka maka son da zai gana maka kwatankwacin azabar da ka bani. Allah ya ɗora maka son da zai sa ka ga fari ka ce baƙi ne. Wata ƙila a lokacin za ka fahimci irin abin da nake ji. Bana maka addu'ar fara son wadda ba ta sonka, dan nasan yanda raɗaɗin son ma so wani yake. Na barka lafiya!”

Ta ƙarashe tana ɗaukan jakarta da ta aje a kan table sanda ta shigo office ɗin. Kuma har ta fice Mu'az bai ce mata ƙala ba. Dan shi yana farin cikin ficewa daga rayuwarsa da za ta yi. Kuma ko kaɗan bai sa a ransa cewa addu'o'inta za su bishi ba. Tun da ya san shi bai zalunceta ba.

_Share fi sabillilah❤️_

*Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.*
*CANDY CE🦋.*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*ƘADDARA CE!*

*©SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY🦋*

_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_

*05*

MAIMUNA POV.

Yau ba kamar kullum da ta saba siyar da kunu duka ba. An samu ragowar wanda ba'a siya ba. Kuma ga shi har ƙarfe goma kunun bai ƙare ba. Dan haka ta kamo hanyar gida tana hasaso yanda za su kwashe da Auwwa.

“Maimuna!”

Ta ji an kira daga bayanta. Hakan ya sa ta juya dan ganin me kiran kafin ta kai ga amsawa. Ganin Abba ne, ɗaya daga cikin abokan Gambo ya sa ta amsa.

“Na'am”

Ta tsaya tana kallonsa. Har ya ƙaraso inda take. Duk da ba haske sosai a inda suke tana iya ganin fara'ar da yake ta yi.

“Har an dawo daga tallar ne?”

Ta gyaɗa kai tana son sanin dalilin da ya sa yake mata magana. Bayan da ba ya mata magana.

“Kin siyar da kunun duka?”

Ta girgiza kai.

“To yanzu ya za ki yi da wannan muguwar matar?. Na ga idan ba ki siyar ba dukanki take”

Sai ta yi shiru tana ƙare masa kallo.

“Ko ba za ta dakeki ba?”

Ta kuma girgiza kanta. Sai ya sa hannu a aljihun wandon jikinsa, ya zaro kuɗin da ya kai dubu biyu, ya miƙa mata.

“Ga shi idan kin je ki bata. Na san wannan zai hana ta dakeki!”

Maimuna ta kalli kuɗin, sannan ta kalli fuskarsa.

“Idan har ka bani wannan kuɗin ne dan Allah. Allah ya baka kadan niyya, kuma na gode. Idan kuma ka bani ne da wata manufa mummuna. Allah ya mayar maka da kayarka kanka. Kuma ina so ka san cewa duka ba ya kisa!”

Tana gama faɗin hakan ta ja siraran ƙafafunta ta yi gaba. Abin da Abba ya yi bai bata mamaki ba. Saboda Allah ne kaɗai ya san adadin samarin da suka so lalata rayuwarta. Samari da dama sun sha cewa suna sonta, amma ita ta san ba soyyayar gaskiya ba ce.

Ƙawayenta na makaranta sun faɗa mata cewar a halin rayuwar yanzu babu namijin da zai iya aureta, saboda tana da sickler. Duk wanda zai zo yace yana sonta raina mata hankali kawai zai yi. Kuma ita ma ta yarda da wannan batun nasu, shi ya sa bata sa a ka ba, in ji ɓarawon tagiya.

Bata takurawa kanta cewar sai ta yi aure ba. Tun da ta kammala secondary school bata sake sakawa kanta wani buri ba. Saboda ita ma secondary school ɗin da ƙyar da fama Auwwa ta barta ta ƙarasa. Shi ya sa ta ture ko wani irin buri da ta san tana da shi. Ta fawallawa sarkin sammai da ƙassai duka lamuranta. Kuma ta san zai kawo mata ƙarshen wahalar nan da take sha.

“Salamu alaikum”

Ta yi sallama daga soron gidan. Jin muryoyi uku sun amsa sallamar ya sa ta fahimci cewa ba Auwwa ba ce kaɗai a gidan. Ilai kuwa, kusan su huɗu ta samu a tsakar gida. Kuma ta san su waye, ƙannen Auwwan ne daga cikin gari.

“Anti Kubura ina wuninku!”

Ta gaishe su tana tsuggunawa. Ciki-ciki suka amsa. Kuma ita bata damu ba, dan idan da sabo ta saba. Tana shirin miƙewa Auwwa ta dakatar a ita da faɗin.

“In ji dai kunu bai ƙare ba?”

Ta sauƙe ajiyar zuciyar kwanciyar hankali. Dan ta san tun da su Kubura suka zo su za'a bawa sauran kunun. Da ace ba su zo ba kuwa yau da ta yabawa aya zaƙinta a hannun Auwwa. Da sauri ta gyaɗa kai tana aje bokitin.

“Akwai saura”

“Shiga kitchen ki ɗauko kofuna ki zubawa su Kubura!”

“To”

Maimuna ta amsa da sauri. Sannan ta miƙe ta shiga ɗan ƙaramin kitchen ɗin gidan. Ta ɗauko kofuna huɗu. Ta zube kunun da ya yi saura a bokitinta, ta miƙawa ƙannen Auwwa.

Daga nan ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala. Sannan ta shiga ɗakinta ta yi sallah. Ta fito ta zauna tana jin yunwa, a gefe guda kuma tana jin tsoron tambayar Auwwa abinci.

“Ub*n miye za ki zo ki zauna ki samu a gaba kina jin zancen da muke?”

Auwwa ta faɗi cike da hantara. Maimuna ta sinne kai tana faɗin.

“Yun... Yunwa nake ji!”

“Saboda ub*nki ne yake kawowa abincin da zan girka ai dole ki ce min kina jin yunwa. To na yi na bawa 'yan uwana sun cinye... Sai a tashi a kaini gaba”

Ta sunkuyar da kanta, ƙwalla na taruwa mata a cikin ido. Kafin ta miƙe ta fita daga gidan. Da ta rasa inda za ta je sai ta nufi unguwar Chadi a cikin wannan daren. Dan ba ta son ta cika kaiwa Mummyn su Maryam matsalolinta. Jiki da jini, wata rana za ta iya gajiyawa da ita. Dan haka gwanda ta je wurin dolenta, wato gidan kakarta.

Da yake tsakanin unguwar Fantai da Chadi ba nisa sai bata sha wahala wurin isa ba. Tun daga soro ta fara shagwaɓe fuska, dan ta san ta zo inda za'a share mata hawaye. Sallamar ma a shagwaɓe ta yi, ta shiga cikin gidan tana wani bubbuga ƙafa a ƙasa.

“Wani irin iskanci ne kuma wannan Maimuna?”

Hajja dake zaune a cikin ɗakinta ta tambaya. Maimuna ta ƙarasa cikin ɗakin tana turo baki gaba.

“Hajja”

Ta kira tana zama kusa da kakarta. Hajja ta dubi jikar tata cike da tausayawa.

“Na'am mai sunana”

“Hajja yunwa nake ji. Rabona da abinci tun safe”

Ta faɗi a shagwaɓe tana shafa cikinta. Hajja ta girgiza kanta.

“Jeki ki ɗiba abincin a cikin cooler. Yana nan a rumfa”
Chapter 9 · 0% Book details