← Book details Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 22

Sashe 13

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Yanzu wani mataki aka ɗauka a kansu... Da ace asirin ƙungiya ya tonu tadalilina gwanda a kawar da mijina da kuma ɗan uwana. Idan har asirin ƙungiya ya tonu ina zan saka kaina Wahash?!”

Wahash ya girgiza kansa, sannan ya juyo suka fuskanci juna.

“Mijinki da ɗan uwanki ba su ya kamata mu kashe a yanzu ba. Shi wannan ɗan sandan me sunan Muktar shi ne babban haɗarinmu a yanzu. Dan haka shi ne wanda za mu fara kawarwa a duniya”

Ba tare da ta nemi sanin waye ɗan sandan ba tace.

”Ina fatan yin hakan ya kawo ƙarshen wannan tsinannen binciken da aka fara. Da dukkan goyon bayana na amince da hakan Wahash!”

Wahash ya gyaɗa kansa. Sannan ya lumshe idonsa, cikin ƙasa da sakanni ya ɓace a falon. Mariya ta ja dogon tsaki tana jin haushin Mu'az da Faruk a lokaci guda. Ta lura da kamar suna so su daƙile mata son kasancewarta ta hannun daman Wahash. Amma ba komai, idan har suka ci gaba da ƙoƙarin tono ramin za ta sa a binne su ciki.

_Share fi sabillilah❤️_

*Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.*
*CANDY CE🦋.*

--------------------
_Kada a manta da biyan kuɗin littafi. Dan free pages sun kusa ƙarewa. To subscribe pay ₦300 to._

5487270431
Salma Isah
Monie point.

And send the evidence of payment via.

08130172702

#Candy
°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*ƘADDARA CE!*

*©SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY🦋*

_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_

*07*

*Unguwar Dutsen Alhaji, Bwari, Abuja.*

*Da misalin 08:20 na dare.*

HALIMA POV.

Mai mashin ɗin da ya ɗaukota tun daga Ummul Banat boutique, wato wurin da take aiki ya tsaya a ƙofar gidan kawunta. Ƙanin mahaifinta, wanda take kira da Kawu Sani. Sauƙa ta yi daga kan mashin ɗin. Sannan ta ɗauko kuɗin mai mashin ɗin ta ba shi.

Ta juyo ta kalli ƙaramin gidan da ya fi ko wani gida nuna halin rashi a layin. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga gidan. A tsakiyar gidan ta taka birki. Ta shiga kallon jama'ar gidan dake kaikawo. Duk yawan mutanen gidan, an rasa wanda zai amsa mata sallama sai Mama Sadiya. Wato matar Kawu Sani ta farko.

Ba tare da tace ko ta yi komai ba ta wuce ɗakin 'yan matan gidan. Su huɗu ta samu zazzaune a ɗakin suna sabgarsu. Sallama kawai ta yi ta shiga cikin ɗakin. Kai tsaye ta wuce wurin da take aje kayanta, wato kusa da katifarta ta kwana. Jakarta ta sauƙe. Sannan ta zauna a bakin katifar tata tana jin yunwar dake cikinta na ƙara girmama.

“Halima!”

Zaliha 'yar Mama Sadiya ta farko ta kira sunanta. Hakan ya sa ta juyo ta kalleta.

“Me yake damunki?”

Ta shagwaɓe fuska kamar yadda ta saba. Sannan ta nuna mata gefen fuskarta.

“Dubi ki ga abin da wani mugun soja ya min yau a boutique. Wai dan kawai mun yi karo fa shi ruwan da yake hannuna ya zube a jikinsa. Shi ne ya sharara min mari! Wallahi yanzu haka ma wurin ciwo yake min. Ji nake kamar ya karya min ƙashin fuska !”

Ta ƙarashe ƙwallar shagwaɓa na zubo mata. Ta turo baki gaba. Tana jin kamar ta fashe da kuka. Da ace lokacin iyayenta na raye ne da yanzu wannan abin da ya mata ya sa ta kwanta jinya. Saboda a wancan lokacin ita 'yar gata ce. Shagwaɓiɓiyyar iyarta da babanta, saboda har suka koma ga mahaliccinsu ita kaɗai ce 'yarsu.

Mahaifinta Alhaji Auwal Kaska ɗan kasuwa ne me arziƙi dai-dai gwargwado. Matarsa ɗaya, haka kuma 'yarsa ɗaya. Kasancewar tun bayan da aka haifi Halima ba su sake samun wani ɗan ba sai suka shagwaɓata. Gata babu kalar wanda ba su yi mata ba. Shi ya sa ta taso a shagwaɓe.

Domin ko me ta nema za ta samu. Ba ta san babu ba. Shi ya sa a sanda Allah ya yi wa iyayenta rasuwa a lokaci guda ta shiga halin ha'u'la'i. Ba'a samu kanta ba sai bayan kwana arba'in da rasuwarsu. Kuma daga lokacin ne ƙalubalen rayuwarta ya fara. Saboda kaf cikin dangin mahaifiyarta babu wanda ya yi ƙoƙarin ɗaukanta dan ya riƙeta. Kowa yana gudun wahala. A cikin dangin mahaifin nata ma da ƙyar aka samu Kawu sani yace zai riƙeta.

Saboda a lokacin an raba gado, dan daga ita sai shi ne kaɗai suka ci gadon mahaifinta. A sanda ta dawo wurinsa ya lallaɓata da daɗin baki ya ƙwace duk wani abu da aka mallaka mata ya cinye. Sai da kuɗaɗe da kadarorinta na hannunsa suka ƙare sannan ta fara fuskantar taskun rayuwa a gidansa. Dan gaba ɗaya Kawu Sani rikiɗewa ya yi ya sauya mata. A farkon zuwanta gidan ba ta cin abinci ɗaya da sauran iyalansa.

Saboda ita ba ta saba da cin abinci mara kyau da daɗi ba, shi kuma taƙonsa ya sa gidansa babu kyakkyawan abinci. Amma bayan kuɗaɗen sun ƙare sai ita ma ta dawo tana cin abinci ɗaya da na yaran gidan. Sai kuma tsangwamar da matar Kawu Sani ta farko wato Mama Zulai ke mata. Aikin wahala babu wanda ba ta sakata, kowa na gidan ya rainta. Shi ya sa gaba ɗaya ta tsani rayuwar gidan. Idan ta tuna da yankan ƙaunar da mutuwar iyayenta ta mata.

A rayuwar Kawu Sani, idan kana da kuɗi kai ne mutum. Shi ya sa gaba ɗaya 'ya'yansa mata suke fita domin nemo masa kuɗi. Wasu ma ta hanyar da bata dace ba suke samowa kuɗin. Amma shi bai damu ba, in har za'a kawo masa kuɗi to su bi kowace hanya ma. To Halima bata shiga tara ba sai da Kawu Sani ya bijiro mata da zancen dole ta fara fita neman kuɗi kamar sauran 'ya'yansa. A lokacin ta sha kuka sosai, duk da da ma can ita kuka ba ya mata wahala.

Sai dai ta riga tasa a ranta cewa ba za ta taɓa yin abin da su Jidda babbar 'yar Mama Zulai ke yi ba, na bin maza domin samun kuɗi. Shi ya sa ta naimi taimakon Zaliha kan ta tayata naiman aiki. Shi ne har ta samu aiki a Ummul Banat boutique. To da wannan aikin ne take samun kuɗin da take bawa kawu Sani, dan ta samu ta zauna a gidansa. Amma duk da haka ba ta da kwanciyar hankali, saboda masifar Mama Zulai ba ta barinta ta huta.

“Ayya. Sannu, kuma wurin ya yi ja sosai, bari in shafa miki man zafi!”

Faɗin Zaliha cikin tausayawa. Halima ta gyaɗa kai tana jin tausayin kanta, saboda yanzu haka ma kanta ciwo yake. Zaliha ta miƙe ta nufi jakarta ta kaya, ta ɗauko man zafin. Sannan ta dawo ta zauna kusa da Halima, ta shafa mata a gefen fuskar tata da ya kumbura.

“Kin yi sallah?”

Zaliha ta tambaya. Halima ta gyaɗa mata kai a shagwaɓe.

“To Mama ta kusa gama girki, idan ta gama sai na zubo mana mu ci”

Ta kuma gyaɗa kai, sanna ta kwanta tana jin kanta na ƙara mata ciwo. Idonta ta lumshe, fuskar wannan mugun sojan ta shigo cikin tunaninta, dan haka ta yi saurin buɗe idonta gabanta na faɗuwa. Dan haka kawai take ganinsa kamar wani dodo. Ƙwafa ta yi, sannan ta cije leɓenta na kasa. Ta juya kwanciyarta tana ja masa Allah ya isa.

“Insha Allah ba za ka samu sukuni ba tun da ka ɗaga hannunka ka mareni. Mugu me jar fuska kawai... Banza ƙatoto!”

Ta faɗi a zahiri, zuciyata na zafi da abin da ya mata. Kamar daga sama ta ji Mama Zulai na ƙwala mata kira.

“Ke Halima!. Halima!”

Idonta ta rintse. Ko wani ɗan ƙaniyar ne ya faɗawa wannan masiffafiyar matar ta dawo?. Miƙewa ta yi zane, tana faɗawa zuciyarta cewa yanzu za'a haɗata da wani aikin. Ba'a barta ta huta da gajiyar da ta kwaso a wurin aiki ba, an zo za'a ƙara mata da wani aikin.

Tana tura baki gaba tana shagwaɓe fuska ta ɗaga labulen ɗakin da suke ciki, tana amsa kiran 'yan farautar da Mama Zulai ke mata. Tsaye ta hangeta a bakin rumfar da ake girki a gidan. Ta haɗe girar sama da ta ƙasa, tana mata wani kallon tara saura kwata.

“Ub*n me kika shiga yi a ɗakin?. Bayan kin san cewa yau girki na ne?”

‘Aikin ƙaniya na shiga yi a ɗakin. Masifaffiya kawai! Ni na saki yin girkin dole?, Da za ki zo ki takurawa rayuwar marainiyar Allah?. Muguwa Azzaluma’

Ta yi maganar duka a zuciyarta. A fili kuma sai wani tsuke baki take tana rau-rau da ido. Tana wani karkata kai, wai duk dan a ji tausayinta. Amma ta san ba za'a ji tausayi nata ba. Tana yi ne kawai dan ya zame mata jiki.

“Ki fito ki zo ki ƙarasa tuƙa tuwon nan... Kuma in kin gama ki rabawa yara... Mtsuww!”

Mama Zulai ta ƙarashe da tsaki. Sannan ta juya zuwa ɗakinta. Jiki a saɓule Halima ta fito daga ɗakin. Tana tafe hawaye na mata zuba. Tana shirin zama a gaban murhun dake ɗauke da tukunya lamba goma. Mama Sadiya ta fito daga ɗakinta tana faɗin.

“A'a me sunana. Ta shi ki je ki kwanta ki huta. Ni zan tuƙa tuwon!”

Halima ta girgiza kai. Sannan ta zauna a kan kujera tana faɗin.

“Ba komai Mama. Zan yi”

“Da dai kin kawo na tuƙa”

“Ai ba yawa, yanzu zan tuƙa”

Da haka ta ɗauki doguwar muciyar tuƙin tuwon da ta kusa kaiwa tsawonta. Sannan ta saka a cikin buɗaɗɗiyar tukunyar. Ta fara ɗiban garin dawar dake gefe tana zubawa a cikin tukunyar. Sai da ta gama tuƙe tuwon, sannan ta shiga rabawa yaran gidan a tray. Ba ita ta koma ɗaki ba sai da ta tabbatar da ta rabawa kowa nasa. Sannan ta koma ɗaki ta kwanta. Tana hawayen da suka zame mata jiki tun shekaru uku baya.

“Halima tashi mu ci tuwo”

Faɗin Zaliha tana aje musu tray ɗin tuwon da ta saka masa miyar kukar da Mama Zulai ta yi. Halima ta miƙe zaune, tana sharar ƙwalla. Ita fa a rayuwa ba ta san cewa mutane na cin dawa ba sai a gidan Kawu Sani. A rayuwarta ta baya ta ɗauka cewa doki kawai ake bawa dawa.
Chapter 13 · 0% Book details