← Book details Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 22

Sashe 17

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kuka da ma ai ke gwanarsa ce... Tun da yanzu ma ga shi nan kina yi”

Ya faɗi yana kallonta. Sai ta kalle shi ita ma. Sannan ta ɗauke kai tana ƙara tura baki gaba.

“Yanzu kin haƙura?”

Ya tambaya. Shi kansa tambayar na ba shi mamaki. Ita ma sai ta kuma kallonsa, sannan ta miƙe tsaye, hannunta riƙe da gorar ruwan da ya bata.

“Na haƙura amma ban haƙura ba!”

Ya ɗan ƙara girman idonsa cikin mamaki. Wai ta haƙura amma bata haƙura ba.

“Me ya sa kika haƙura kuma at the same time ba ki haƙura ba?”

Ta masa wani irin kallo da ya hautsina bugun zuciyarsa nan take. Sannan ta juya kanta tana kallon wani gefen... Sai tura baki take, kamar wadda aka wa dole kan sai ta yafe masa.

“Na haƙura dai”

Ta faɗa tana kallon gorar dake hannunta. Mu'az bai san sanda murmushi ya suɓuce daga kan leɓensa ba. Saboda shi haka kawai wannan abin da take yake burge shi. Yana jin ana cewa shagwaɓa, bai taɓa ganin mace me shagwaɓa ba sai yau...

A hankali ya sunkuya ya sa hannunsa a cikin motarsa ta saitin inda ta fito. Ya ɗauki chocolate. Sannan ya miƙe ya miƙa mata.

“Kina so?”

Sai ta masa irin wannan kallon na ɗazu. Sannan ya kalli chocolat ɗin.

“Ai ban sanka ba. Na sani ma ko kai ɗan yankan kai ne?”

Murmushi ya sake yi yana ɗaga kansa sama kaɗan. Sannan ya sauƙe yana faɗin.

“Ba ki ga ni soja ba ne?”

Ta kalli wandon kakin sojojin dake jikinsa. Dan daga shi sai wata baƙar T-shirt da ya sa. Ta kalli fuskarsa, wadda yanayinta kaɗai, da kuma askin kansa zai sa ta gane cewa shi sojan ne, amma sai ta girgiza kai.

“Ai akwai sojojin gona”

“Ni ba ɗaya daga cikinsu ba ne”

“Me cece shaidarka?”

Ta tambaya tana kafe shi da ido. Ya kuma yin murmushi yana girgiza kansa, sanna ya sa hannunsa ya kamo nata da bata riƙe gorar ruwan da shi ba. Ya saka mata chocolat ɗin a ciki, kuma ba tare da ya saki hannun nata ba ya kalleta yana faɗin.

“Ki daina jayyaya Leemat. Ba na son gardama na san kin yarda da ni, tun da har kika yarda kika sha ruwan da na baki. Dan haka ki karɓi wannan ma. Kyauta ce daga MJ zuwa Leemat! Sunana Mu'az... Wata ƙila hakan zai amfaneki wata rana”

Tun da ya riƙo hannunta Halima ke kellon fuskarsa. Saboda ita ta kasa gane wannan wani kalar mutum ne. Haka kawai sai ya yi ta riƙe mata hannu ba da son ranta ba?. Saboda ƙarfin hali biyan ba shi da ɗan kishiya?.

Kuma ita amfanin ne sunansa zai mata. Ai tun jiya take fatan kada Allah ya sa ta sake haɗuwa da shi, yanzun ma tsautsayi ne. Kuma tana fatan kada Allah ya sake nuna mata shi har ta koma gare shi. Hannunta dake kan nasa ta janye tana goge ƙwallar idonta. Sannan ba tare da tace masa komai ba ta juya ta nufi hanyar shiga cikin boutique ɗin.

Sai da ta shige ciki sannan Mu'az ya yi dariya. Haka kawai halinta na saurin kuka da langwami da kuma shagwaɓa suka saka shi cikin nishaɗi. Motarsa ya shiga ya tayar ya bar boutique ɗin. Kuma har ya isa barrack bai daina dariyar abin da Halima ta yi masa ba.

Cike da farin ciki Halima ta buɗe ledar chocolate ɗin da MJ ya bata. Saboda tun tana ƙarama Allah ya ɗora mata ƙaunar chocolate. Kuma iyayenta na sai mata chocolate ɗin sosai. Yanzu kuma da ruwa ya ƙarewa ɗan kada ta manta rabonta da shan chocolate ɗin.

Bite na fako da ta yi sai da ya sa ta ji ta kamar a wata duniya. Saboda ta yi matuƙar kewar chocolate fiye da yanda za'a iya kwatantawa. Lokaci guda ta yi murmushi. Saboda ta tuna da yanda mahaifinta yake yawan kawo mata chocolate.

“Allah ya ji ƙanka Daddy”

Ta faɗa a fili. Tana tuna duk wani kyakkyawan abu da ya gabata a rayuwata.

“Ke Halima! Zaman me kike a nan da ba za ki zo ki kama aiki ba?”

Ta juyo muryar Boss ɗinsu a bayanta. Da sauri ta sauƙa daga kan kujerar da take. Tana zare ido kamar wadda ta yi wa sarki ƙarya.

“Ki zo ki fara aikinki. Ga wasu can sun zo siyan kaya suna neman wanda zai taya su zaɓa!”

Ta gyaɗa kai da sauri tana nufar hanyar wurin da Boss ɗin ya nuna mata.

_________________

_Daɗina da gobe saurin zuwa😂_

_Salmanians!_

_Da alama Sir MJ dodon abinci ya haɗu da gamonsa_

_Share fi sabillilah❤️_

*Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.*
*CANDY CE🦋.*

--------------------
_Kada a manta da biyan kuɗin littafi. Coz free pages sun kusa ƙarewa. To subscribe pay ₦300 to._

5487270431
Salma Isah
Monie point.

And send the evidence of payment via.

08130172702

#Candy
#SalmaAhmadIsah
°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*ƘADDARA CE!*

*©SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY🦋*

_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_

*09*

MUKTAR POV.

Kamar yanda suka yi alƙawarin komawa bincike layin BB hotel sun koma ɗin. Amma a wanan karon da shirinsu suka tafi, ta yanda ko da za'a kawo musu hari za su iya kare kansu. Amma kuma rasa makama ya sa shi da Ali yin cirko-cirko a cikin layin da Munira ta bi sanda motar nan ta biyota. Saboda tun da suka shigo ba su ga wani me tallah ko me abin siyarwa ba. Hatta da masu wucewa sai dai ka gansu jifa-jifa.

Shi ya sa ya faɗawa kansa cewar dole ne ma a sace mutum a wannan layin, saboda babu zirga-zirga a layin. Sai dai idan har Allah ya hukunta faruwar abu a lokaci, to ba makawa sai ya faru. Dan har sun riga sun cire rai da samun wani abu. Sai Allah ya jefo da dalilin tonuwar asirin da suka daɗe da son ya tonu. Saboda a sanda suke da niyyar juyawa su koma inda suka fito. Muktar ya yi arba da wata mabaraciya ta shigo layin. Hakan ya sa ya yi wa Ali magana kan ya tsaya.

Tsayawar suka yi. Kuma a kan idonsu matar ta tsaya a jikin wata bishiya. Ta shimfiɗa buhu, ta zauna a kai, sana ta aje wani kwano a gabanta ta fara barar da ta saba yi kullum a layin. Muktar bai san sanda murmushi ya suɓuce masa ba.

“Ali mu je”

Yace kawai. Sannan ya nufi wurin matar. Ali ya bi bayansa kamar kullum, zuwa jikin bishiyar da matar ke zaune a ƙarkashinta. Har ƙasa suka durƙusa suka gaisheta. Sannan Muktar ya fara tambayarta.

“Iya. Mu jami'an 'yan sanda ne. Kuma muna bincike a kan ɓatan wata matashiya. A cikin binciken mu mun yi karo da wani bayani da yace an ga sanda ita wadda aka sace ɗin ta shigo layin nan. Dan haka muke so mu tambayeki ko kin ga sanda ta shigo!”

Iya me bara ta jinjina kai. Sannan tace.

“To yaro, faɗa min rana da kuma lokacin da aka ga ta biyo ta nan ɗin. Idan zai iyu ma ku faɗa min har da kalar tufafin jikinta. Saboda idan har nan layin ta iyo to tabbas zan ganta. Dan ni nan da kuka ganni kullum nan nake zama ina bara, sai dai idan da magariba ko da sassafe ta shigo layin. To shi ne dai ba zan sani ba!”

“To Iya. Yanzu za'a iya kaiwa kimanin wata ɗaya da kwanaki da faruwar abin. Kuma ranar asabat ne da yamma. Sannan tana sanye da jallabiya kalar ruwan goro. Haka fara ce, me ɗan siririn jiki!”

Muktar na kaiwa aya Iya me Bara na buɗe bakinta.

“Ƙwarai kuwa yara. Na ga sanda ta wuce ta nan. Kuma ka ga can...”

Ta ɗan yi fasali tana nuna musu ƙofar wani gida, Muktar da Ali suka juya suka kalli gidan, sannan suka sake kallonta a tare, sanda ta ci gaba da faɗin.

“... A ƙofar gidan can wata baƙar mota ta tsaya. Wasu mutum biyu mace da na miji da baƙaƙen kaya suka fito daga ciki, sannan suka ɗauketa suka jefa cikin motar!... Ni kuma ganin hakan ya sa na tsorata, shi ya sa na yi gum da bakina ban taɓa faɗawa kowa ba”

“To iya shin kin iya ganin fuskokin waɗan da suka ɗauketa?”

Muktar ya tambaya da sauri. Iya me bara ta girgiza kanta.

“A'a. Ban gani ba. Amma ranar da aka saceta akwai wani matashi ɗan can gidan da shi ma ya ga sanda suka saceta, kuma har hoto me motsi ya ɗauke su a wayarsa. Da yace zai faɗawa 'yan sanda, amma sai mahaifinsa ya hana shi!”

Muktar da Ali suka dubi juna. Sannan suka jinjina kai a tare.

“Iya me nene sunan matashin?”

“Audil”

Iya ta amsa. Yanda ta kira sunan Audil ɗin instead of Abdul ya sa su yin dariya. Kafin Muktar ya ɗebo kuɗi ya bata. Har suka bar wurin tana saka musu albarka. A ƙofar gidan da ta nuna musu suka tsaya. Ali ya yi sallama. Sannan suka tsaya jiran fitowar masu gidan.

Da farko mahaifin Abdul ɗin ne ya fito. Sai da suka masa bayanin abin da ke tafe da su, sannan ya kira Abdul ɗin. Ya saka su a gaba yana son ganin abin da zai faru. Dan ko sama da ƙasa za su haɗe ba zai bari su tafi da ɗansa headquarter ba. Idan videon suke son kallo shi bai hana ya nuna musu ba. Za ma su iya turawa a nasu wayoyin, amma su tafi da ɗansa shi ne abin da ba zai lamunta ba.

“Abdul. Idan har ka san kana da videon nan a wayarka. Ka daure ka nuna mana. Saboda idan har ba ka nuna mana ba rayuwar sauran al'ummar gari tana cikin haɗari!”

Abdul da ya sunkuyar da kansa ya ɗago ya kali babansa. Wanda ya harɗe hannaye a ƙirji yana kallon kowa cikinsu. Sannan ya kalle su.

“Idan da akwai a wayarka ka nuna musu. Ni ban hana ba, amma fa daga nan babu inda za ka ƙara ɗaga ƙafarka. Ba zan bari ka tafi ko ina ba Wallahi!”

Faɗin baban Abdul. Kuma kalamansa suka sa Abdul ya sa hannu a aljihun wandon jikinsa. Ya ɗauko wayarsa ya cire password. Sannan ya nemo videon a inda ya ɓoye. Ya kunna, ya miƙawa Muktar.
Chapter 17 · 0% Book details