← Book details Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 22

Sashe 4

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saboda tsabar yanda makashin ya bata wahala wurin kasheta ya sa su kansu ba su tabbatar da cewa gawarta ba ce sai da iyayenta suka zo suka tabbatar da cewa ita ce. Kuma tun bayan rasuwarta da Mu'az Faruk ba su huta a kan binciken wanda ya kasheta ba.

“Ka yi haƙuri Kaigama. Da yardar Allah za'a kama mai laifin”

Faɗin Mu'az a ƙoƙarinsa na kwantarwa da Faruk hankali. Ganin yanda suka fito daga headquartern duka a dame. Cike da damuwa Faruk ya dube shi yana faɗin.

“Har yanzu na kasa mantawa da hoton gawarta da na gani a idona MJ. Kuma hoton tashin hankalin da ahalinta suka shiga lokacin mutuwar ya kasa fita daga kaina. Ba na jin hankalina zai kwanta idan har ban kamo me laifin nan ba MJ!”

Mu'az ya dafa kafaɗarsa.

“Insha'Allah za mu kamo shi!”

“Allah ya yarda”

MAIMUNA POV.

Kamar yanda ta saba farkawa sassafe haka ta farka a asubar yau ma. Abu na farko da ta fara yi shi ne alwalal sallahr asuba. Ta dawo ɗakinta ta tada sallahr. Kuma bayan ta idar ta fita tsakar gidan ta fara aikinta na safiya kamar yanda ta saba.

Duk da yanda sanyin safiyar yake sauƙa a kanta bata haƙura da aikin ba. To da ta isa ma ta haƙura da aikin?. Ita a wa?, Kare da gudun layya?. Sai da ta yi shara. Sannan ta wanke kwanukan da aka ɓata a daren jiya. Kafin ta zauna ta fara firar doyar da za ta dafa ta kuma soya domin kai wa makarantun safe dake kusa da su. A lokacin Auwwa ta fito daga ɗakinta tana hamma.

Kanta ta ɗaga ta kalli Auwwan. Sannan ta gaisheta a ɗarare. A ranta take ƙiyasta lokacin da Auwwan ta tashi. Dan ta san lokacin dai ƙarfe bakwai za ta yi. Kuma ita ba ta isa ta tasheta a bacci ba. Saboda kyakkyawan warning ne daga Auwwan, kan kada ta kuskura ta tasheta idan tana bacci.

A kan idonta Auwwan ta ɗauki buta ta yi alwala. Sannan ta shiga ɗaki domin yin sallah. Sai da a kammala fere doyar sannan Gambo yayanta ya shigo gidan. Kallonsa ta yi tana gaishe shi. Ko kallon arziƙi bata samu daga gare shi ba. Ballantana har ta yi zaton zai amsa gaisuwar tata.

A tasowarta a gidan bata jin akwai rana ɗaya da suka taɓa yin magana da ɗan uwan nata ta minti biyar ta arziƙi. Ko kalo bata ishe shi ba ballantana har su samu damar yin hira. Kuma da ma shi ba zama yake a gidan ba. Kullum yana waje wurin abokansa masu hayar napep.

“Ke Maimuna!”

Auwwa ta ƙwala mata kira daga cikin ɗakinta bayan Gambo ya shiga ɗakin.

“Na'am”

“Ki yi maza ki ɗora ɗumamen tuwo yanzu. Gambo yace yunwa yake ji”

“Auwwa na ɗora tukunyar doya fa”

Tsautsayin shan zagi ya sa bakinta ya suɓuta wurin faɗar hakan. Ai ko an danƙaro mata zagin. Dan sai da Auwwa ta zaɓo wani zagi tun na zamanin maguzawa ta makawa uwarta dake cikin ƙasa.

“...Gidana ko gidanki?. Da har zan ce ki yi abu ki kawo son ranki”

“Allah ya baki haƙuri”

Maimuna ta faɗi. Tana nadamar maganarta ta farko. Jiki na rawa ta sauƙe ƙatuwar tukunyar doyar da ta ɗora. Sannan ta ɗora ta ɗumame.

“Kuma ki cire bayan tuwon da ya bushe”

Ta ji Auwwa ta sake faɗi daga cikin ɗakin.

“To”

Ta amsa wani sashi na zuciyarta na farin ciki. Dan ta riga da ta san yau babu rabonta a ɗumamen nan. Kuma tun da Auwwa tace ta ɓare bayan tuwon tana nufin ta zubar bata so. To ita kuma da wannan damar take amfani wurin rage yunwar da take damun cikinta. Dan idan ta ɓare bayan wankewa take, sai ta ɗan saka yaji ta ci.

Yau ɗin ma haka aka yi. Tana ɓarewa bayan tuwon shinkafar da ya bushe ta saka musu tuwon a cikin miyar dake kan wuta. Yayin da ta zube bayan tuwon da ya bushe a roba, ta wanke shi, tafaki ido ta zuba yaji a ciki. Ta koma gefe ta cinye.

Sannan ta wanke robar ta aje. Ta dawo ta sauƙe tukunyar ɗumamen. Ta sanar da Auwwa cewa ɗumamen ya kammala. Kafin ta mayar da tukunyar doyar kan wuta. Tana zaune a wurin. Auwwa ta fito ta zuba ɗumamen a kwanika biyu, ɗaya nata ɗaya kuma na Gambo.

Maimuna bata ta shi daga gindin murhun nan ba sai da ta gama dafa doyar, sannan ta soyeta da fulawa tas. Ta faɗawa Auwwa cewa ta gama. Auwwan ta zo ta zauna ta lissafa kuɗin doyar. Sannan ta saka mata a cikin bokiti fallasa.

“Ta dubu uku da ɗari biyar ce. Saura kuma yau ma ki bada bashin”

Faɗin Auwwa tana hararta. Maimuna ta gyaɗa kai tana nufar randa.

“Ub*n me za ki yi kuma?”

Ta juyo a tsorace tana faɗin.

“Na ga hantsi ya fara ɗagawa ne. Shi ne zan zuba ruwa a bokita na aje a rana. Kafin na dawo daga talla na san ya yi ɗumi sai na ɗan yi wanka da shi!”

Auwwa ta maka mata harara haɗi da jan tsaki. Sannan ta miƙe ta ja tulelen jikinta ta shiga ɗaki. Maimuna ta zuba ruwa a bokita. Ta aje a rana. Sannan ta shiga ɗakinta ta saka hijabina ta fito tana ɓoye kuɗin babur ɗin da Mummy ta bata.

Ta ɗauki bokitin doya da fulawar ta fita. Kasancewar yau ƙafar tata bata ciwo ya sa ta isa makarantar Famfo goma da ta fi kusa da su da wuri. Dan a yankin unguwar tasu kusan makarantu shida ne. Kuma duk ciki babu wadda bata kaiwa tallahr doya da fulawa da safe.

Tana isa makarantar ta wuce sashin da 'yan tallah ke taruwa a babbar makarantar ta 'yan mata. Kasancewar government school ce ya sa masu kawowa tallar kayan suke taruwa da yawa. A kusa da wadda ta fi sani cikin 'yan tallar me suba Rahina ta aje bokitinta.

“Yau kin zo da wuri Maimuna. Dan sauraminti goma a fito tara”

Faɗin Rahina. Mamuna ta yi murmushi.

“Dan Allah Rahina so nake ki jire min kayana zan je asibiti a dubani!”

Rahina ta dubeta. Kasancewar ta san cewa su masu scikler ba'a raba su da jinya, ballantana kuma yanzu da ake cikin lokacin sanyi da cutar ta fi yawan tashi yasa tace.

“Ƙafar ce ko bayanki ne yake ciwo?”

“A'a. Ai yau da na tashi ban ji ciwon ƙafar ba. Auwwa ce ta ƙona ni jiya da dadare!”

Ta ƙarashe tana nuna mata singalin hannunta na hagu da ya yi alamar ƙuna. Dan fatar wurin har ta tashi Cike da jin tausayinta Rahina ta kawar da kanta gefe tana kare fuska.

“Subhannallahi. Wallahi Maimuna Auwwa muguwa ce”

Maimuna ta sunkuyar da kanta tana gyara ledar dake kan murfin bokitinta. Sannan ta ɗaga kai ta kalli Rahina dake kallonta.

“Bari na je”

“Amma kar ki daɗe”

Maimuna ta gyaɗa kai tana miƙewa. Kuma kai tsaye ta nufi bakin titi. Domin hawa napep, wadda za ta kaita Haɗejia general hospital. Duk da asibitin bata da nisa da unguwar Fantai.

Da yake ta san sashin da Mummyn su Maryam take sai bata sha wahalar nemanta ba. Kai tsaye ta je ta sameta a inda suke zama. Kuma Mummy ita ta kaita aka ɗaye fatar ƙunan da ta tashi. Sannan aka saka mata magunguna.

Kuma a pharmacy ɗin asibitin Mummy ta sai mata magungunan da aka rubuta mata, har ma da wanda ba'a rubuta ba. Wato magungunanta na cutar sickler. Kasancewar ta sanar mata cewar nata sun ƙare.

Basu rabu da Mummy ba sai da ta sai mata dafaffen ƙwai. Dan ko ba'a faɗa ba ta san cewa Maimuna na buƙatar kayan ƙarin jini. To kuma sai ƘADDARA ta sa ta taso a gidan da abincin da za ta sa a cikinta ma gagararta yake. Ballantana ta samu wanda zai ƙara mata jini. Haka Maimuna ta yi ta mata godiya har suka rabu ta dawo makarantar Famfo goma.

_Share fi sabillilah❤️_

_______________

_Ya kamata a fara biya tun daga yanzu fa!_

_If you want to subscribe pay ₦300 to._

5487270431
Salma Isah
Monie point

*Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.*
*CANDY CE🦋.*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*ƘADDARA CE!*

*©SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY🦋*

_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_

*03*

*No.42, Inuwa Wada crescent, Utako, Abuja.*

*12:55 na dare.*

MARIYA POV.

A dai-dai irin wannan lokacin da ya kasance duk wani abin hallita yake bacci domin samun hutu ita idonta biyu. Duk wani hankali da tunaninta ta tattara shi a kan agogon bangon dake manne a bangon ɗakinta. Burinta bai wuce ta ga ƙarfe sha biyu ta cika dai-dai ba. Ba dan komai ba sai dan ta tafi babban meeting ɗin ƙungiyarsu da za'a gabatar a yau da ƙarfe sha biyu na dare.

Cike da ƙaguwa ta juya ta kalli Hilal dake kwance a kan bed ɗinta yana bacci. Ta ja tsaki tana ƙara maida idonta kan agogon. Ganin mintuna biyu ne suke rage sha biyun ta cika ya sa ta miƙe tsaye. Ta sunkuya ƙarƙashin gadonta ta janyo wani akwati dake aje a wurin.

Zama ta yi a ƙasa, sannan ta buɗe akwatin, komai dake cikin akwatin ja ne. Kuma abubuwan dake cikin akwatin ba su wuce huɗu ba. Daga wata jar doguwar riga, sai 'yar ƙaramar ƙwarya da aka yiwa fentin ja. Sanna kuma a cikin ƙwaryar akwai wani jan ruwa me kauri.

Daga gani daskararren jini ne. Sai reza dake ɗauke da busasshen jini a jiki, da kuma wasu zobunan ƙarfe har da sarƙoƙi. Hannu ta kai ta ɗauki rigar. Sannan ta miƙe tsaye, ta cire tufafin jikinta ta saka rigar. Har ƙasan ƙafafunta rigar ta sauƙa, kuma hannun rigar dogo ne sosai.

Hannu ta kai ta cire ribbon ɗin da ta ɗaure gashin kanta da ba kitso. Ta barbaza shi a bayanta. Ta ɗauki zobina masu ɗauke da kan wata dabba mara fasali ta saka a yatsunta duka goma. Sannan ta saka sarƙoƙin dake cikin kayan. Ta ɗauki kwaryar dake ɗauke da daskararren jini ta riƙe a hannunta. Sannan ta juyawa gabar baya tana jiran cikar ƙarfe 12.
Chapter 4 · 0% Book details