← Book details Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 22

Sashe 5

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A dai-dai lokacin da hannun agogon ɗakin ya kaɗa a kan ƙarfe sha biyu dai-da. Mariya ta rintse idonta da ƙarfi. Sannan pendant ɗin ɗaya daga cikin sarƙoƙin dake wuyanta ya kawo jan haske. A hankali cikin salihar muryarta ta furta.

“Mhish!”

A lokacin da fatar leɓenta ta sama ta haɗu da 'yar uwarta ta ƙasa wurin kaiwa karshen kalmar taɓace bat a cikin ɗakin.

*RED SHAITAAN'S SAVERNTS PALACE.*

Babban ɗakin taro ne. Wanda ya ƙunshi jerin kujeru sama da ɗari. Kuma duka kujerun suna kallon juna ne daga ko wani bango na ɗakin. Kamar dai jerin kujerun majallisar sarakunan gargajiya.

Ko wace kujera a wurin ja ce, kuma kowacce tana ɗauke da sunan me ita. Daga can kan stage ɗin dake a tsakiyar ɗakin taron daga can ƙarshe kuma kujeru ne guda uku. Wadda ke tsakiya tafi kowacce kujera girma. Yayin da biyun da suke a gefe da gefenta kuma irinsu ɗaya. Amma kuma su ma sun fi sauran kujerun dake ɗakin girma.

Daga tsakiyar ɗakin kuma wani katon rami ne dake ɗauke da itatuwan dake ci da wuta. Ga kuma wasu kayan tsaface tsaface da baka ce ga sunayensu ba. A hankali suffar Mariya sanye cikin jan kaya ta bayyana a tsakiyar ɗakin taron. Kuma sai da ta ji ƙafafunta sun sauƙa ƙasa, sannan ta buɗe idonta a hankali. Ƙafarta ta cira ta fara tafiya a hankali. Har ta isa kujerar dake ɗauke da sunanta a cikin ƙungiyar. Wato RAZOR!.

Sai da ta zauna sannan ta aje ƙwaryar dake hannunta a kan wani teburi. A hankali a hankali mutane suka ci gaba da bayyana a cikin ɗakin. Kafin kace me har sun cika ɗakin. Duk yawan waɗannan kujerun sai da suka cika su taf.

Mutane ne da ban-da ban, daga sassan duniya, wasu baƙaƙen fata ne, wasu kuma fararen fata ne. Kuma ko wa a cikinsu na sanye da jan kaya. Yayin da wasu daga cikin bayin shaiɗan na wurin ke aikin haɗa wutar dake ci a ɗakin taron.

Bayan shuɗewar wani lokaci wata ƙofa dake kusa da babbar kujerar dake ɗakin taron ta buɗe. Sannan wani tsoho da ya tara farin gemu ya shigo sanye cikin jan kaya. Bayyanarsa a cikin ɗakin taron ya sa sauran bayin shaiɗan ɗin suka miƙe domin nuna girmamawarsu ga Shugaba!.

Tsohon ya tsaya a jikin kujerarsa da tafi ta kowa kyau da girma a ɗakin taron, wadda ke nuna cewa ya fi kowa matsayi a wurin. Ya ɗaga hannayensa duka biyu sama, sannan ya haɗesu wuri guda alamun bauta da jinjina.

“Jinjina zuwa ga bayin shaiɗan!”

Duka ɗakin ya ɗauka da muryoyin mutanen cikinsa, masu banbancin jinsi, al'ada da yare.

“Jinjina zuwa ga shugaban bayin shaiɗan!”

Tsohon ya yi murmushi, sannan ya musu alama da su zauna. Kowa ya zauna, sannan shina ya zauna. Sai da ya juya ya kalli ɗaya daga cikin kujerun da suka saka tasa a tsakiya. Wadda wani ba'indiye ke zaune a kai, alamun dai shi ne na hannun hagunsa.

Kafin ya juya ya kalli ɓangaren kujerar dake damansa, wadda babu kowa a kai. Sannan ya juya ya kalli sauran bayin shaiɗan ɗin da suka yi shiru suna jiran jin abin da ya sa aka tara su a wurin.

“Kamar yanda muka saba gudanar da taron tattaunawa a ko wani mako. Yau ma haka ne. Sai dai ina so na sanar da ku cewar lokacin sadaukarwa ya kusa. Dan haka sai ku shirya domin sadaukar da ɗaya daga cikin waɗan da kuke so ga shugabanku shaiɗan. Sannan kuma ku sani cewa duk wanda ya kuskura ya tsallake sharuɗanmu to zai mutu, kamar dai yanda Kunda ya mutu. Duk wanda muka nuna cewa shaiɗan na so a cikin ahalinku, dole a sadaukar da jininsa. Ƙin amincewa da hakan na nufin barin mutum duniya. Dan za ku mutu ku je ku faɗa wuta tare da shaiɗan!”

(Wa'iyazubillah.!)

“Mun ji mun amince shugaban bayin shaiɗan!”

Suka amsa da babbar murya. Ciki har da RAZOR.

“Sai kuma batu a kan wanda zai maye kujerar Kunda!...”

Sai ya dakata yana kallon Razor da ta maida hankali kansa.

“Razor!”

Razor ta zabura ta miƙe tsaye, daga ciki ban da tsallen murna babu abin da zuciyarta ke yi. Dan da alama mafakin da ta ci burin cimmawa ne ya zamto gaske. Mafarkin da ya samu muhalli a cikin rayuwarta tun bayan mutuwar Kunda na hannun daman shugaban bayin shaiɗan. Wato maye kujerar Kunda ɗin. Shugaban bayin shaiɗan me suna Wahash ya kalli sauran bayin shaiɗan, sannan ya nuna Razor da hannunsa yana faɗin.

“Razor ita ce wadda za ta maye wurin Kunda!”

Cike da farin cikin wannan batu na Wahash Razor ta zube ƙasa, ta yi wa wutar shaiɗan sujjada tana masa godiya. Kafin ta miƙe tana yi wa Wahash godiya.

“Amma kafin faruwar hakan, dole ki sadaukar mana da ɗanki Haruna Faruk Kaigama. Hilal nake nufi!”

Wahash ya faɗi abin da suke buƙata a maimakon wannan kujera. Ba tare da tsoro, shakku, ko ɗar ba Razor ta amince cike da farin ciki.

Ta sadaukar da abubuwa da dama kafin ta kawo yanzu. Na farko sai da ta fita daga musulunci, dan sam a yanzu bata sallah ballantana azumi a watan ramadan, ko wata ibada da ta kasance wajib a kan ko wani musulmi na mai imani. Sannan ta sadaukar da mahaifarta bayan ta haifi Hilal. Ta kuma ƙauracewa haɗa shimfiɗa da mijinta tsawon shekara guda duka a kan wannan ƙungiya.

Abubuwan da ta sadaukar ba za su ƙirgu ba. Dan haka ko da mahaifinta Alhaji Jibrin Gimba Gashuwa GG suka buƙata za ta sadaukar da shi, ballantana Hilal ƙaramin alhaki. Da wannan batun taron nasu ya waste. Amma kafin Razor ta tafi sai da suka yi tattaunawar sirri ita da Wahash.

“Razor!”

Ta kalle shi cikin girmamawa.

“Mun gano cewa mijinki da yayanki suna bincike a kan mutuwar Munira abokiyar aikinsu da kika kashe. Sakamakon ganinki da ta yi a lokacin da muka aikeku ku kashe Kunda a BB Paradise hotel!”

Nan take yanayin bugun da ƙirjinta yake ya sauya salo. Daga na farin ciki zuwa na tashin hankali. Daga Mu'az har Faruk babu wanda ta yi wa ƙaramin sani. Ta san halinsu kamar yunwar cikinta. Idan har suka gano gaskiyarta ba za su yi la'akari da alaƙarta da su ba za su hukuntata. Ganin kamar ta tsorata ya sa Wahash faɗin.

“Babu buƙatar ki ɗaga hankalinki. Domin mun yi wa tufkar hanci, ta hanyar goge duk wani CCTV footage na ranar da kuka haɗu da Munira a hotel ɗin!”

Idonta ta lusmhe tana jin bugun zuciyarta na dai-daita. Sannan ta buɗe idon nata.

“Wahash yaushe zan sadaukar da Hilal ɗin?!”

Ta tambayi abin da ya fiye mata muhummanci. Dan ita a yanzu babu abin da take buƙata da ya wuce maye kujerar Kunda. Kuma ita ta ƙagu ta sadaukar da Hilal ta huta. Tun da da ma shi da ubansa duka ba sa gabanta. Wahash ya goya hannayensa a bayansa yana murmushi.

“Me kike ci na baka na zuba Razor?. Ai daga zarar lokacin ya yi za mu sanar da ke. Yanzu dai abu ɗaya nake buƙata daga gareki. Shi ne gashin kansa, domin ba za mu sadaukar da jininsa ga shugabanmu shaiɗan ba ba tare da mun tsaface shi ba. Dan haka sai kin jira nan da wasu wattani!”

Duk da ba haka ta so ba ta ji daɗi. Da wannan batu ta yi wa Wahash sallama, sannan ta dawo gidanta, cikin ɗakinta. Kuma tana dira a ɗakin Hilal ya zabura ya farka, lokaci guda ya canyara kuka. Amma ko ajikinta an mintsini kakkausa. Dan bathroom ma ta shiga.

Ta je ta yi wanka ta dawo ta sauya kaya ta kwanta a kan gadon tana kallon Hilal ɗin dake kuka har zuwa lokacin. Kallonsa da ta yi ya motsa wani abu a cikin zuciyarta. Musamman ma da ta tuna cewa nan da wasu watanni za ta sadaukar da shi ga abin bautarta a yanzu, wato shaiɗan.

(Ya ilahi!)

Tausayinsa ta ji ya fara shiga zuciyarta, dan haka ta kai hannu za ta taɓa kansa. Amma sai wannan baƙin hayaƙin da ya saba rufe mata ido a duk sanda za ta tuna wani abu na soyyaya tsakaninta da Faruk ko ɗansa ya rufe idonta.

Lokaci guda hannunta na dama da ta ɗaga za ta ɗora a kan Hilal ya ƙame a saitin kan nasa. Ƙwayar idonta ta juye zuwa ja. Sannan lokaci guda fushi ya maye fuskarta. Sai ta yi saurin janye hannunta daga kansa.

Sannan ta juya masa baya tana huci kamar wadda aka ɓatawa rai. Lokaci guda idonta ya soma zubar da hawayen jini. Ta rintse idonta gam tana karanto wata addua'a tasu ta bayin shaiɗan. Har ta samu ta yi bacci.

FARUK POV.

Da misalin ƙarfe goma na dare ya fito daga banɗaki. Bayan ya watsa ruwa a jikinsa kasancewar bai jima da dawowa daga wurin aiki ba. Sanye yake da yellow plain T-shirt da baƙin sweat trouser, ƙafafunsa duka na sanye cikin baƙin sliders ɗinsa.

A hankali ya kai hannu ta taɓa sumar kansa da take a jiƙe, wadda kuma bata cika tsayi ba kasancewarsa soja ya sa ba ya tara gashi ko da ya so hakan. Shi yasa yake askin high fade tare da buzz cut.

Yana shirin kashe hasken dake ɗakinsa, idonsa ya sauƙa a kan wani hoto dake cikin kyakkyawan frame. Wanda ya ƙunshi Mu'az da Munira da kuma shi kansa. Zama ya yi a gefen gadonsa. Ta inda hoton ke aje a kan side drawer.

Ya kai hannu ya ɗauki hoton yana kallo. Gaba ɗaya su ukun na sanye cikin korayen kaya ne na sojoji, kuma sai kayan dake jikin nasu ya tuno masa da lokacin da aka ɗauki hoton. Wato ranar da suka yi passing out.

Domin NDA Kaduna (National Defense Academy Kaduna) suka fara haɗuwa da Munira a wurin training. Ƙwazonta da kuma nuna jarumtarta duk da kasancewarta mace 'yar arewa yasa suka ƙulla abota da ita. Alaƙarsu da Mu'az kuma ta fara ne tun daga secondary school. Har suka kai ga tertiary school suna tare, kuma burin kowwane a cikinsu tun a wancan lokacin shi ne zama soja.
Chapter 5 · 0% Book details