← Book details Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 22

Sashe 20

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Saboda Yasmin ce kaɗai mace a duniya ko?. Ko kuma saboda an faɗa miki cewar ba ni da wani aiki sai na chat da Yasmin?... Wallahi Mima idan ba ki daina shiga min hanci ba zan fatoki. Kuma a ranar da zan fato ki idan kika duba fuskarki a madubi ba lalle ki gane kanki ba!”

Sai ta sosa kai tana zare ido.

“Shugaban masifaffu!”

Ta faɗi a ƙasan maƙoshi. Mu'az ya kalleta.

“Kin yi magana ne?”

Sai ta yi saurin girgiza kanta.

“Ni kaza?... A'a, komai ban ce ba!”

Ya wurga mata harara yana faɗin.

“Ƙaramar mara kunya!”

Mima ta ɗauki wayarta ta nufi stairs tana faɗin.

“Allah ya nuna min ranar da ni ma zan zama babbar mara kunyar nan, matsayina ya ƙaru a idon ya Mu'az!”

Kasancewar a hankali ta yi maganar ya sa bai jita ba.

“Mummy!”

Ya kira Mummy. Mummy ta dube shi tana amsawa.

“Ɗazu na je gidan Anti Farida. Kuma tace tana gaisheki”

Mummy ta ja tsaki tana mayar da dubanta kan tv. Can kuma tace.

“To ina ruwana?”

Mu'az ya yi murmushi me sauti.

“Mummy! Mummy! Mummy!...”

“Kai ni kar ka ƙarar min da suna!”

Mummy ta katse shi.

“Wai ni Mummy me Anti Farida ta miki ne?”

Mummy ta galla masa harara.

“Babu abin da ta min... Babana Mu'az”

Tana ƙarashewa ita ma ta miƙe ta bar falon. Ya rage daga shi sai Na'im. Shi ma miƙewa ya yi ya kama hanyar fita.

“Ya Mu'az wai yaushe za ka siyo min sweatern?”

Na'im ya tambaya. Lokaci guda ya saki murmushi. Sannan ya juyo.

“Kada ka damu oga tulele. Zan siyo maka gobe. Akwai chocolate a wurinka?”

Ya tambaya yana murmushi. Saboda har ya fara hasaso haɗuwarsa da Halima a gobe.

“Akwai. Amma sai kinder delice. Kuma ai kai baka shan kinder”

“Ba ni zan sha ba, kyautarta zan bawa wata Baby. Ka kawo min guda goma idan akwai m&m's cookies ka ɗauko min guda biyar”

Na'im ya miƙe yana faɗin.

“Babyn waye?”

Mu'az ya kalle shi.

“Wata kyakkyawar baby girl ce... Me saurin kuka da fitina”

Na'im ya yi dariya kawai. Sannan ya nufi sama. Ɗakinsa ya shiga ya buɗe wardrobe. Ya ɓebo chocolate da cookies ɗinsa, sannan ya saka a cikin wata bag me kyau. Ya sauƙo ƙasa ya iske Mu'az a inda ya barshi. Ya miƙa masa jakar da ya saka chocolate ɗin.

“Yauwwa oga tulele. Ka kyauta. Insha'allah gobe zan kawo maka sweaternka. Sannan zan sake siyo maka wasu chocolate ɗin”

Mu'az ya faɗa yana karɓar jakar. Na'im ya yi dariya.

“A'a. Ba sai ka siyo min wasu ba, ina da wasu kalar da Daddy ya sai min last week”

“To Baby ta gode. Yayan baby ma ya gode”

Ya faɗa yana juyawa. Fuskarsa ɗauke da murmushi.

“Baby!”

Ya furta sunan yana nufar part ɗinsa. Kuma har ya shige bai bar murmushin ba.

FARUK POV.

Zaune suke a falo shi da Hilal da ya yi bacci tun wuraren ƙarfe 8. Kwance Hilal ɗin yake a kan cikinsa. Yayin da shi kuma yake zaune a kan kujera, yana jiran dawowar Mariya gidan.

Shi ya rasa wannan wata kalar rayuwa suke shi da Mariya. Matar aurensa ta sunna ce za ta sa ƙafa ta bar gidan aurenta ba tare da ta nemi izinin mijinta ba?. Ba kuma hakan ne ya sa shi mamaki ba. Saboda ta saba fita ba tare da ta tambaye shi ba. Mamakinsa shi ne barin ƙaramin yaro da ta yi a gida shi kaɗai.

Idan bai ɓata a ƙirgen watan haihuwar Hilal ba, dudu yanzu ba zai wuce wata goma sha ɗaya ba. Amma har ta kan iya tafiya ta bar shi a gida shi kaɗai. Ko da gidan Hajiya za ta je bai kamata ta tafi ta bar shi a gidan shi kaɗai ba.

Kuma halin da ya zo ya same shi a ciki ne ya ƙara baƙanta masa rai. Ya zo ya same shi cikin yunwa. Ga kuma diapers ɗin dake jikinsa ta cika da bayan gari da kuma fitsari. Da alama tun safe da aka saka masa ba'a sauya masa ba.

Tsaki ya ja yana kaiwa dubansa kan agogon dake bango. Ganin goma ta haura ya sa ya sake jan wani tsakin. Sannan ya sa hannunsa a kan ɗansa yana shafawa a hankali.

Lokaci guda ya ji Hilal ya zabura, sannan ya kuma canyara kuka yana ƙara zabura. Saurin kaiwa hannu ya yi ya gyara masa kwanciya a tsakiyar hannunsa. Yana karantowa ayatul kursi, tare da tofa masa.

A hankali a hankali kuma sai kukan nasa ya ragu, har ya yi shiru, ya dawo yana jan zuciya, kuma duk wannan abin da ya faru idonsa a kulle yake gam. Sai ya ɓata fuska yana turowa leɓensa na ƙasa. Yanayin fuskar tasa ya bawa Faruk dariya. Dan haka ya yi murmushi. Ya shafa kansa, sannan ya sumbaci goshinsa. Ya rungume ɗansa yana faɗin.

“Allah ya raya min kai babana!”

Shiru ya yi ya ɗaga kai ya kalli ƙofar falo da aka buɗe. Mariya ta shigo tana kallonsa. Kuma ba tare da tace masa komai ba ta wuce shi ta nufi stairs. Kamar daga sama ta tsinkayo muryarsa, da amon da bata taɓa sanin cewa yana da shi ba.

“Daga ina kike?”

Sai ta tsaya cak. Sannan ta juyo. Sai ta gan shi a tsaye, Hilal ɗin da ta shigo ta same shi rungume da shi kuma ya kwantar da shi a kan sofa.

“Tambayarki nake Mariya!”

Ya sake magana yana tsareta da ido. Sai ta dawo cikin falon, ta tsaya a gabansa ba tare da ta masa ko tari ba.

“Ina kika je ba tare da izinina ba? Kuma kika fita kika bar min ɗana a cikin gida shi kaɗai kamar maye!?”

Sai ta yi murmushin da ta saba.

“In da ka aike ni na je!”

Lokaci guda wannan murmushin da take, da kuma yanda ta masa maganar a sigar dake nuna bata damu da ɓacin ransa ba suka fara hasalla zuciyarsa. Ya ji ya kawo wuya. Duk da shi bai cika saurin fushi da saurin kai hannu ba irin na Mu'az ba. Amma yau dai kam yana jin Mariya ta kai shi bango.

“Na farko kin aikata min laifin fita daga gidana ba tare da izinina ba. Na biyu kin fita kin bar min ɗa a gida shi...”

Bai kai aya ba Mariya ta katse shi.

“Wai ni a kanka aka fara haihuwa? Magana ɗaya biyu sai ka sako ta ɗanka a ciki? Ai ni ma ɗana ne, ba shegensa na yo a waje ba!...”

Ba ta rufe bakinta ba ta ji sauƙar mari a kuncinta na dama. Lalle yau ta ƙure Faruk har wuya, tun da yake bai taɓa ɗaga hannunsa a kan wata mace ba, ballantana matarsa ta auren sunnu, matar tasa ma Mariya, wadda yake jin sonta har cikin ransa.

Amma abin da ta aikata yau ya sa ba zai iya yafe mata ba kamar sauran kura-kurenta na baya. Ita ce da laifi, amma ji yanda take ɗaga masa murya kamar ita ce mijin, shi kuma matar.

“Ba ki isa ba Wallahi... Mary ba ki yi wannan tasirin a zuciyata ba da zai sa ki aikata min laifi, sannan ki zo kina ɗaga min murya na ƙyaleki...”

Mariya da mamaki ya sa ta sandare ta ci gaba da kallon fuskarsa da ta sauya mata lokaci guda. Ko dai ba Faruk ɗinta ba ne?. An yama kuwa wannan mijinta ne?... Har ya gama faɗansa ya ɗauki Hilal ya bar mata falon ba ta iya yin ko da tari ba.

Cike da jin haushin da bai gama washewa a ransa ba Faruk ya kwantar da Hilal a kan gado. Ya lulluɓe shi yana jin wani abu na baƙin ciki na tokare masa maƙoshi. Gaba ɗaya ma ya rasa yanda zai yi ya huta.

MAIMUNA POV.

Yau da matsanancin ciwon baya ta tashi. Amma duk da haka sai da ta yi duk ayyukan da suka zame mata wajibi a gidan. Tana yi tana kuka, saboda yau ciwon da take ji ya fi na kullum. Ta yi doyar safe. Ta je ta siyar, sanan ta fara haɗa kunun dare. Tana tsaka da tatar hatsin da ta karɓo a wurin niƙa Auwwa ta kirata.

“Ke Maimuna!”

Da ƙyar ta iya ɗaga yalayen idonta irin na masu sickler ta kalli Auwwan. Sannan ta amsa.

“Na'am”

“Zo!”

Da ƙyar ta iya miƙewa tsaye. Tana dafe da bayanta da yake matsanancin ciwo. Ta nufi inda Auwwa ke tsaye. Auwwa ta miƙa mata dubu uku, ta kai hannu ta karɓa.

“Kasuwa za ki zo ki tafi ki siyo min doya. Na ga sauran guda ɗaya!”

A take Maimuna ta ji ruwan dake zuba a idonta ya ƙara gudu. Dan haka ta ɗaga kai ta kalli Auwwa. Yanzu idan ba'a rage mata aikin dake kanta ba ai ba a ƙara mata ba. A yanayin jinyarta kwata-kwata ba'a son su shiga damuwa ko tashin hankali, dan hakan kan iya taɓa zuciyarsu kai tsaye. Amma a gidansu sam ba'a damu da hakan ba. Ɓacin rai kullum sai Auwwa ta kasa mata a fai-fai ta ɗauka.

“Ko ba za ki je ba ne?”

Ganin Auwwan na shirin ɗaukan madoki ya sa ta yi saurin girgiza kai.

“A'a zan je”

Ta rufe leɓenta ƙwalla na ƙara sauƙo mata. Ba tare da tace komai ba ta ja siraran ƙafafunta da ba su cika ƙwari da lafiya ba ta ɗauki hijabinta. Ta saka. Sannan ta fita waje tana kallon yanda rana ta baza duniya.

Da ace tana da gata da a mashin za ta je kasuwar. Amma a halin da take ciki na magen maƙota ma ta fita muhimmanci ba za ta samu wannan gatan ba. Ba komai take hasasowa ba face nisan dake tsakanin gidansu da kasuwa.

A abin hawa ma tafiyar ba kaɗan ba ce, ballantana kuma a ƙafa. Ga kuma yanda rana ta ƙwalle a sama, kamar ba lokacin hunturu ba, duk da sanyin ya fara ja baya. Ga ciwon baya ga na ƙafa, ga kuma na jiki da na zuci.
Chapter 20 · 0% Book details