← Book details Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 22

Sashe 7

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saboda yawan jin kiɗa ɓabi'ar sojoji ce. Bai haura mintina biyar da shigowa ɗakin ba aka kira wayarsa. Hakan ya sa ya rage sautin kiɗan. Ya ɗaga wayar yana wani haɗe rai, kamar wanda aka cewa ya sha magani ba ruwa. Kuma hakan ya samo asali ne daga ganin sunan me kiran.

Yasmin. Wata yarinya ɗaya tilo da ta nace a duniya kan shi take so. Kuma cikin wani ikon Allah sai aka yi rashin sa'a shi babu sonta a tsarin rayuwarsa. Dan yace shi bata masa ba, saboda ta cika naci da yawa.

“Yanzu abin da kake min ka kyauta Mu'az?”

Muryarta me sanyi ta fito daga cikin wayar. Ya lumshe idonsa yana murza goshinsa.

“Me na yi kuma?. Ko da yake, ai ba'a rasa nono a ruga. Da ma ni kullum me laifi ne!”

Daga ɗayan ɓangaren, Yasmin ta girgiza kanta.

“Ko kaɗan Mu'az ba haka ba ne. Ni dai kawai abu ɗaya nake so daga gareka. Kuma shi ne na kasa samunsa har yanzu. Kulawa ita ce abin da nake buƙata Mu'az. Ya kamata ka riƙa nuna cewa ina da muhimmanci a cikin rayuwarka!”

“Me ya sa zan miki ƙarya?”

Cikin rashin fahimta Yasmin tace.

“Ƙarya kuma? What do you mean?”

“Yes, ƙarya. Did you want me to be saying that i love you?. Bayan kuma a zahiri ba haka ba ne”

Ƙwalla ta zubo daga idon Yasmin.

“Mu'az!”

Ta kira cikin sanyin murya.

“Na'am”

Ya amsa.

“Ina so na tambayeka abu ɗaya”

“Faɗi, ina ji”

“Mu'az kana sona, ko a'a?”

Kai tsaye yace.

“Bana sonki Yasmin. Ban taɓa sonki ba, kuma bana tunanin fara sonki ko da a nan gaba”

Cike da baƙin ciki Yasmin ta kashe wayarta. Yana jin ta sauƙa a layi ya cilla wayar kan gado. Sannan ya ƙure Volume ɗin waƙar da yake ji hankalinsa kwance kamar tsumma a randa. Kamar ba shi ne ya gama tarwatsa zuciyar wata yanzu ba.

_Share fi sabillilah❤️_

------------------------

_I have told you that KADDARA CE! Isn't free!_
_If you want to subscribe pay ₦300 to._

5487270431
Salma Isah
Monie point

And send the evidence of payment via 08130172792.

*Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.*
*CANDY CE🦋.*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*ƘADDARA CE!*

*©SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY🦋*

_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_

*04*

*Unguwar Fantai, Haɗejia local government, Jigawa state.*

MAIMUNA POV.

Su uku ne jere a bakin titi. Kuma ko wacce a cikinsu kayan siyarwarta ne a gabanta. Ɗaya tana suyar awara, ɗaya tana soya wainar fulawa, sai kuma ita da bokitin kununta ke aje a gabanta.

Tun daga nesa ta hangi kawunta, ƙanin mahaifinta wato Kawu Barau. Duk da duhun magariba da ya fara sauƙa bai sa ta kasa gane shi ba. Baki ta washe ta miƙe tsaye tun kafin ya iso inda suke. Kuma shi ma har ya iso inda suke murmushi yake.

“Kawu ina wuni!”

“Lafiya ƙalau me sunan Hajja”

Kawu Barau ya amsa yana kallon tilon 'yar ɗan uwansa. A lokacin ya lura da hannunta na dama dake ɗauke da tabon ƙuna. Lokaci guda fara'ar kan fuskarsa ta yi balaguro.

“Me sunan Hajja ya aka yi kika ƙone?”

Maimuna ta kalli hannunta, sannan ta kalli kawu tana faɗin.

“Auwwa ce ta ƙonani rannan. Amma ai ya fara warkewa, saboda Mummynsu Maryam ta kaini asibiti, kuma har magunguna ta sai min”

Cike da tausayawa Kawu ya girgiza kansa yana faɗin.

“Wa cece kuma Mummyn su Maryam?”

“Wannan ƙawar tawa, jikar tsohon Kaigama”

“To to. Na gane, 'yar gidan Bara'atu ko?. 'Yar Alhaji Haruna Kaigama me rasuwa, ƙanwar Alhaji Bello Kaigama na yanzu!”

Maimuna ta gyaɗa masa kai.

“Amma ko ta kyauta. Allah ya biyata da gidan aljanna... Amma baki faɗawa Hajja ba?”

Ta yi saurin gyaɗa masa kai. Dan bata faɗawa kakar tata ba. Saboda a tsakanin kwanakin ba ta je gidanta ba. Kuma ko ta je ma ballale ta faɗa ba idan har ba tambaya Hajjan ta yi ba.

“To Allah ya kyauta. Ya saka miki da abin da Auwwa take miki. Ki ci gaba da haƙuri kin ji ko me sunan Hajja?. Allah na sane da ke, kuma zai kawo miki ƙarshen wannan wahalar taki. Ki ci gaba da addu'a. Kan Allah ya baki ikon cinye wannan jarabawar da yake miki”

Faɗin Kawu Barau yana lissafo 'yan kuɗaɗen da suka sa aljihunsa yin nauyi a safiyar yau. Cike da damuwa Maimuna ta gyaɗa masa kai.

“To Kawu. Inshallah zan yi”

“Karɓi wannan ba yawa. Na san magungunanki sun ƙare, dan wallahi suna raina, shi ya sa na kasa sukuni har sai da na samo kuɗin siyansu, dan na san a yanzu lokacin sanyi kin fi buƙatarsu”

Maimuna ta yi murmushi tana girgiza masa kai.

“Ai duka Mummy ta siya min har da folic acid da palludrine”

Cike da mamaki Kawu ya kalli kuɗin hannunsa, sannan ya ƙara miƙa mata.

“Duk da haka dai ki karɓa, ba zaki rasa amfanin da za su miki ba. Ko sabulu kika siya kika wanke kayanki ai kin rage”

Maimuna ta karɓi kuɗin hanu biyu, tana kallon kawunta da yalayen idanuwanta.

“Na gode Kawu. Allah ya ƙara buɗi”

Kawu ya yi murmushi. Sannan ya mata sallama ya ɗale kekensa ya nufi gida. Kasancewar tun bayan rasuwar matarsa bai sake yin wani auren ba ya sa yake zaune tare da mahaifiyarsu. A soro ya jingine kekensa, sannan ya yi sallama ya shigo cikin gidan. Inda ya iske mahaifiyarsu Hajja, zaune a tsakar gida, da alamun alwala ta yi, dan ga buta nan aje a gabanta.

“Barau an dawo?”

“Eh Hajja. Na dawo”

Hajja ta miƙe tana faɗin.

“To sannu da hanya”

“Yauwwa Hajja”

Daga haka ta shiga rumfar dake gidan, ta ɗauki hijabinta dake aje a kan sallaya. Ta saka ta tayar da sallah. Yayin da Kawu ya kama ruwa, sannan ya yi alwala ya fita masallaci.

Sanda ya dawo Hajja na zaune a nan rumfar tsakar gidan tana jan carbi. Zama ya yi a kan kujera 'yar tsugguno yana jiran ta kammala. Kuma sai da ta kammala ɗin ya faɗi abin da ke bakinsa.

“Hajja magana nake so mu yi a kan Me sunanki!”

Hajja ta aje carbin hannunta tana tattara hankalinta gare shi, jin batun magana a kan tilon jikarta.

“Me ya samu Maimunatun?”

Cikin damuwa Kawu ya tsara mata abin da Auwwa ta yi wa Maimuna, sannan ya ƙara da.

“... Ni Wallahi dan de kin ƙi ta tawa ne, tun yarinyar nan tana ƙarama na so ta dawo wurinki da zama, amma kika ce can shi ne dolenta, dan haka ba za ta dawo nan ta zauna ba, yanzu bayan talla da Auwwa ke ɗora mata har da su hukunci da wuta take mata, ya kamata mu yi wani abin a kan lamarin me sunanki Hajja. Ko da wannan cutar dake damunta aka barta ya isheta ƙaddara, ballantana a ƙara mata da izayar matar uba!”

Hajja ta ci gaba da kallonsa har ya kai aya, sannan tace.

“Barau! Ba wai na ƙi amincewa da shawararka ba ne. A'a, ni akwai abin da nake hangowa. Yanda Auwwa take da masifar son abin duniya za ta iya cinyewa wannan gidan. Bayan kuma shi ne kaɗai gadon da mahaifinsu ya bar musu ita da Gambo. Ina da tabbacin idan har Maimuna ta bar gidan nan Auwwa da ɗanta za su iya mallake mata gado. Kuma ko ba komai ɗa a gidan ubansa ya fi daraja, idan tana can ɗin ita kanta sai ta fi jin cewa a gidan ubanta take!”

Kawu ya yi shiru. Can kuma yace.

“A gaskiya Hajja ni na fara tunanin yi mata aure. Dan na lura da auren shi kaɗai ne zai kuɓutar da ita daga wanna baƙar azabar da take sha!”

Hajja ta girgiza kanta.

“Barau kenan! A auren yanzu masu lafiya ma ba auruwa suke da daɗin rai ba. Ballantana ita da take da jinya. Jinyar da iyaye ma kan guji 'ya'yansu idan suna ɗauke da ita, saboda gudun wahala, ballantana kuma miji. Kuma a irin auren yanzu ba na jin akwai wanda zai iya kula da Maimuna. Ka sani ba sai na nanata maka ba cewar cutar da Maimuna ke da ita na matuƙar bukatar kulawa. Kuma fa ni tun da nake da ita ban taɓa ji tace yau ga wani saurayi yace yana sonta ba, saboda kawai tana da sickler!”

Hajja ta ƙarasa maganarta a raunane. Saboda tausayin jikarta dake ƙara kamata. Shi dai Kawu shiru ya yi kawai, dan a zahirin gaskiya ya fara gajiya da abubuwan da Auwwa takewa 'yar ɗan uwansa. Kuma yana ganin kamar lokacin da zai ɗauki mataki ya yi.

MARIYA POV.

Zaune take a kan kujerar falo. Ta saka Hilal dake wasa a cikin car toy ɗinsa a gaba tana kallo. Kamar ta samu tv, a hankali ta ciro yatsun hannunta biyu da ta cusa a cikin gashin kanta.

Sannan ta gyara zamanta tana kallon yaron, sai kuma ta kai hannunta saitin da motar wasan nasa take. Sannan ta motsa hanun nata. Na take motar ta iyo gabanta kamar yanda ta motsa hanun nata.

Kallon yaron ta ci gaba da yi, kamar yanda shi ma yake kallonta. Sannan a hankali ta ɗaga hannunta na dama, ta saka a cikin sumar kansa me laushi, sannan ta ciro gashin kansa da mugun ƙarfi. Amma kuma ko gezau yaron bai yi ba.

Ya yi shiru kawai yana kallonta, hannunsa riƙe da rattle yana karkaɗawa. Gashin ta ɗaga tana kallo. A take ƙwayar idonta ta sauya kala zuwa ja. Sannan ta kalli Hilal, ta buɗe baki da shirin yin magana, fiƙoƙin haƙwaranta na sama suka ɗan ƙara tsayi kaɗan.

“Na gode Hilal. Saboda da ban haifeka ba da ba zan zama ta hannun daman shugaban bayin shaiɗan ba. Ina sonka!”

Ta ƙarashe tana shafa gefen fuskarsa. Shi dai kallonta yake kawai, kamar me fahimtar abin da take faɗi. Mariya ta janye hannunta daga kansa, sannan ta yi amfani da ƙarfin tsafinta ta tura car toy ɗin nasa inda take da.

Ta miƙe ta fita daga falo, ta zagaya bayan gidan, sai ta tsaya ta waiga hagu da dama, sanna ta rufe idonta, ta ɗora hannunta a bayan wuyanta, inda tambarin ƙungiyarsu ta bayin shaiɗan ke zane a wurin. Sannan ta furta.

“Mishk baksh hushk!”
Chapter 7 · 0% Book details