Sashe 15
Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amma kuma ƙwaƙwalwarsa ta kasa yarda da hakan. Gaba ɗaya shi ji yake cewar bai aikata ba dai-dai ba, tun farko wa yace ta buge shi, har ta zuba masa ruwa a jikinsa?. Sai dai kuma wani sashi na zuciyarsa na faɗa masa cewar ya aikata kuskuren marinta. Bai kamata ace tashin farko ya mareta ba, ya kamata ace sai da ya tambayi ba'asi tukkuna.
Amma ya zai yi?. Zuciyarsa ce a kusa, abu kaɗan ke sawa ya harzuƙa, kuma shi daga ya fusata yake mayar da martani. Ture wannan tunanin dake damun kansa ya yi, sana ya amsa gaisuwar Zulaihat.
“Lafiya Zulaihat... Ya gida?”
“Gida lafiya”
Ta amsa tana satar kallon idon Mima da har yanzu a tsorace take. Kuma ba ta ƙara razana ba sai da Mu'az ɗin ya kalleta.
“Mima ina Mummy?”
Ta haɗiyi yawu, sannan ta amsa masa da sauri.
“Tana ɗakinta”
“Me aka dafa yau?”
Ya kuma tambaya.
“Tuwo aka yi. Amma Mummy tasa na dafa maka jollof ɗin couscous”
“Kin saka nama ko kifi?”
Ta ɗan kalli Zulaihat, dariya na son kufce mata. Sannan ta kalle shi tana amsawa.
“Eh. Na saka maka catfish”
“Zuba min Please”
“To”
Ta faɗa tana miƙewa, sannan ta nufi kitchen. A lokacin Na'im ya sauƙo daga sama. Kuma yana sauƙowa ya yi kan Mu'az.
“Ya Mu'az ka siyo min sweatern?”
Na'im ya tambaya yana zaunawa kusa da shi. Maganar sweater ta tuno masa da yanda aka yi ya aje sweatern. Lokaci guda hoton ya taho haɗe da na fuskarta, da kuma na idanuwanta da ya fi kalla a fuskar tata. Maimakon yace wani abu sai ya dafe kansa yana faɗin.
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!”
Na'im ya taɓa shi.
“Baka da lafiya ne Ya Mu'az?”
Sai ya girgiza kansa yana ɗagowa da shi. Sannan ya ƙaƙalo murmushi.
“Lafiyata ƙalau. Na manta da siyan sweatern ne. Amma gobe inshallah zan siyo maka!”
Yana faɗin hakan ya miƙe tsaye, ya nufi hanyar fita daga falon. Mima da ta fito daga kitchen, hannunta riƙe da plate ɗin abincinsa tace.
“Ya Mu'az ga abincin!”
Sai ya juyo ya kalleta. Ba tare da ya ce komai ba ya nufeta, sannan ya karɓi plate ɗin. Ya juya ya fita daga part ɗin Mummy ba tare da yacewa kowa komai ba. Har ya fice su Mima ba su daina mamakin abin da ya hana shi sukuni ba.
A falon part ɗinsa ya zauna, ya saka abincin da ya karɓa a wurin Mima a gaba yana kallo. Ya kasa ci, kuma ya rasa yanda zai yi da shi. Can kuma sai ya ja wani dogon tsaki.
Haba mana. Ya za ayi wata yarinya ta shigo tunaninsa ta takurawa rayuwarsa, ta hana shi sukuni haka kawai dan ya mareta?. Mutum nawa ya mara a kan sun masa laifi?. Sai ita da aka ƙerata da gwal?. Za ta takurawa tunaninsa?. Idan har ta sake shigo masa tunani sai ya je har Ummul Banat boutique ɗin ya hukuntata.
Da wannan maganar da zuciyarsa ta raɗa masa ya samu sukunin cin abinci. Har ya taso ya koma ɗaki. Ya cire rigar jikinsa ya kwanta a kan gado. Ya kashe wuta da niyyar yin bacci. Amma sai baccin yace ai ba su yi yarjejeniya da shi kan zai ɗauke shi a wannan lokacin ba. Tunaninta kuma ya ƙara dawo masa. Idanuwanta da suke ƙyallin ƙwallar da take zubarwa sun fi komai takura masa.
Hannu ya kai ya ɗauki pillow ya danne kansa da shi, wai ko za ta fice masa a cikin tunani. Amma Wallahi ba ta fita ba. Daga ƙarshe ma sai ya miƙe zaune a kan gadon, sannan ya dafe kansa yana faɗin.
“Ya isa Mu'az. Ya isa!”
Ya faɗawa kansa yana shafa saitin zuciyarsa. Sannan ya ƙara da.
“Babu abin da ya haɗa hanyarka da ta waccan yarinyar. But she's innocent!...”
Wani zancen ya shigo cikin wani. Sai ya rintse idonsa yana furta.
“Oh lord of mercy. Na shiga uku ni Mu'azzam!”
Ya buɗe idonsa. Sannan ya sauƙa daga kan gadon. Ya shiga bayi, ya yi wani sabon wankan, wai ko zai samu yarinyar ta fita daga kansa. Ko da ya dawo ɗakin ya kwanta ba ta sauya zani ba.
Daga ƙarshe sai ya miƙe ya zauna a tsakiyar gadon ya shiga yin salatin annabi. Wata ƙila Allah ya dube shi ya kawo masa ɗauki. A ranar bai yi bacci ba sai da ya sa a ransa cewar zai je ya bata haƙuri, kuma ya amin ce cewar ya aikata mata ba dai-dai ba.
Zuciyarsa ma sai da ta raya masa cewa wata ƙila ma mayya ce. Shi ya sa ta hana shi baccin dare. Amma dai ko ma aljana ce zai je ya bata haƙuri, in ya so ta ci kanta ta sha baƙin ruwa.
°°° °°° °°°
_Humm Humm Humm_
_Garin daɗin kowa ya kama da wuta. In ji Malam Tsalha mijin me Koko.😂._
_Da alama Halima da Kairat sun yi addu'a a bakin 'yan amin._
_Sir MJ dodon abinci ya kasa sukuni saboda kuskuren da ya aikata mata_
_Wai ni ina Maimuna ne?_
_To a yi dai mu gani_
_Share fi sabillilah❤️_
*Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.*
*CANDY CE🦋.*
--------------------
_Kada a manta da biyan kuɗin littafi. Free pages sun kusa ƙarewa. To subscribe pay ₦300 to._
5487270431
Salma Isah
Monie point.
And send the evidence of payment via.
08130172702
#Candy
#SalmaAhmadIsah
°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*ƘADDARA CE!*
*©SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY🦋*
_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_
*08*
*Unguwar Fanisau, Haɗejia local government, Jigawa state.*
“Maryam! Maryam! Maryam ke!”
Mummy dake cikin kitchen ta ƙwalawa Maryam dake zaune da Maimuna a falo kira.
“Na'am Mummy”
Maryam ta amsa tana nufar kitchen ɗin. Ta tsaya a ƙofar kitchen ɗin, sannan ta leƙa kanta ciki.
“Mummy ga ni”
“Tsabar iskanci kina ji ana kirana amma ba za ki iya kawo min wayar ba?”
Maryam ta ɗan yi dariya irin ta marasa gaskiya ta na sosa kai.
“Yanzu za ki je ki ɗauko min wayar ne? Ko tsayuwa za ki ci gaba da yi a nan har Mahadi ya bayyana?”
Da sauri Maryam ta dawo falo, inda Maimuna ke zaune tana cin abinci. Ta ɗauki wayar Mummu dake chargy. Sannan ta kai mata wayar ta dawo ta zauna a wurin Maimuna. Ganin mahaifiyarta ce mai kiran ya sa Mummy ta bi bayan kiran. Bugu uku Hajiya ta ɗauki wayar da sallama.
“Hajiya Ina wuni?”
Mummy ta gaisheta cike da girmamawa.
“Lafiya ƙalau Bara'atu!. Ya gida ya yaran?”
“Lafiyarsu ƙalau. Alhamdullilah. Ya wurin su Faruk da matarsa, Dan Adam mun yi waya da shi ɗazu”
“Faruk lafiya, amma ba lau ba Bara'atu!”
Jin hakan ya sa girar Mummy tatarewa wuri guda. Sannan tace.
“Me ya faru da shi?”
Hajiya ta girgiza kai.
“Matsalar Mariya ce ba komai ba. Duk da dai shi da kansa bai furta min hakan ba. Amma kuma ni na gane hakan tun ba yau ba!”
Mummy ta girgiza kanta.
“To ya za ayi Hajiya?. Tun da shi ba zai iya faɗar matsalarsa ba ballantana a ba shi shawara sai a taya shi da addu'a!”
Hajiya ta sauƙe numfashi.
“To... Haka ne... Allah ya dai-daita tsakani...”
Daga gaka suka ɗan taba hira, kafin suka yi sallama. Ko da Mummy ta gama abin da take a kitchen ɗin sai ta fito. Inda ta samu Maimuna da Maryam zaune a falo.
“Maimuna ya kamata ki tafi gida. Na ga lokaci ya ƙure. Kar Auwwa ta dakeki!”
Maimuna ta miƙe tsaye tana faɗin.
“To Mummy, bari na tafi!”
“Ga shi kuma yau Sadiq ba ya gari. Ballantana su raka ki shi da Maryam”
Maimuna ta girgiza kai tana faɗin.
“Ai ba komai Mummy. Zan iya tafiya Ni kaɗai”
Mummy ta jinjina kai.
“To mu kwana lafiya”
“Allah ya tashemu da alkairi”
“Amin”
Maimuna ta yi wa Maryam sallama, sannan ta fita. Tana tafiya a hanya tana tuna dalilin fitarta cikin wanna daren, kuma ba komai ya ja hakan ba face abinci da Auwwa ta hanata kamar yanda ta saba a wasu lokutan. Dan wani lokacin idan 'yan imanin na kusa ba ta hanata.
“Assalamu alaikum”
Ta yi sallama daga soron gidan. Sannan ta shiga. Gabanta ne ya soma faɗuwa tun da ta yi arba da Auwwa tsaye a tsakar gidan. Ta ƙame a gu ɗaya. Hannunta kan ƙugu tana jijjiga kamar me shirin hawa bori. Tun da ta ga haka ta san cewa yau kam ta banu.
“Daga gidan ub*n wa kike?”
Auwwa ta tambaya. Maimuna ta haɗiye yawu jikinta na rawa. Sannan tace.
“Gi... Gi... Gidan su... Maryam na je!”
“Saboda ke gaki kwaɗayayyiya ko?... Su kuma ga su dangin waliyyai, masu zuciyar tausayi?... Shi ne kika ɗauki ƙafa kika tafi gidan...”
Ta dakata tana cafkowa hannunta. A take Maimuna ta fashe da kuka. Sannan ta soma roƙon Auwwa.
“Dan Allah Auwwa ki yi haƙuri! Dan Allah! Dan Allah!..”
Auwwa ta ɗaga ɗayan hannunta da bata riƙeta da shi ba, ta doke mata baki har sai da jini ya fara fita daga bakin nata. Maimuna ta fashe da wani sabon kuka, a sanda ta ga Auwwa ta nufi gindin murhu da ita.
A gaban murhun ta durƙusar da ita, sannan ta sa wani cokali a cikin murgun, ta ɗaiko garwashi, ta ɗora a kan hannun Maimuna. Haka Maimun ta yi ta ƙwalla ƙarar azaba tana kuka tana roƙon Auwwa. Amma ko a jikinta. Ga shi su ba maƙota garesu ba bare a ji a kawo mata agaji.
“Shegiya matsiyaciya. Allah ya sa gobe ma idan na hukunta ki da abinci ki sake zuwa can ki ci!”
Maimuna ta ƙarawa kukanta sauti. Sannan ta durƙushe a wurin tana kuka me ban tausayi. Haka Auwwa ta miƙe tsaye ta tsallaketa ta wuce ɗakinta. Maimuna ta ci kukanta ta godewa Allah. Da ƙyar ta iya tashi ta shiga ɗakinta da babu bulb.
Da akwai, amma kwana nan Auwwa ta cire shi, wai za'a bawa Gambo. Saboda ɗakin da yake kwana nasu ya mutu. Haka ta zauna a cikin sauron da take iya jin kukansu a kunnenta. Da ƙyar ta janyo ledar magungunan da Mummy ta sai mata. Ta sha tana hawaye har zuwa lokacin.