← Book details Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 22

Sashe 2

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana nan kwance ta ji sanda Gambo yayanta, kuma tilon ɗan Auwwa ya shigo gidan. Tana jin sanda ya ɗauki abincinsa ya fita daga gidan, saboda shi ba ya kwana a gidan. Sannan tana jin sanda Auwwa ta gama cin nata abincin ta koma ɗaki ta kwanta.

Sai da ta tabbatar da Auwwa ta wuce birnin sin a duniyar bacci, sannan ta saci ƙafa ta fito daga ɗakinta. Ta ɗauki takalmanta ta fita daga gidan. Sai da ta yi nisa da layinsu ta saka takalmanta. Sannan ta ci gaba da ɗingisa ƙafarta ta nufi unguwar Fanisau dake haɗe da unguwarsu.

Dan ba wani banbanci tsakanin unguwar Fantai da Fanisau ɗin, kawai dai an raba unguwar ne. Kuma ita unguwar Fanisau ta fi unguwar Fantai kyawawan gidaje. Wani babban layi ta nufa. Inda ta tsaya a bakin gate ɗin gidan da ya fi ko wanne girma a layin.

Tana hawayen famun ƙunan hannunta da ta yi ta ɗaga hannunta ta ƙwanƙwasa ƙaramar ƙofar shiga gidan. Tana tsaye a wurin ta ji muryar ne gadin gidan daga ciki yana faɗin.

“Waye a nan?”

Ta goge hawayenta tana faɗin.

“Baba Habu Maimuna ce!”

“Ah-ah! Maimunatu? Me ya faru?”

Baba Habu ya buɗe ƙofar yana faɗa. Hasken fitilun dake ƙofar gida suka haske masa fuskarta. Ya dubeta yana mamakin abin da ya fito da ita da wannan daren.

“Baba Auwwa ce ta ƙonani. Shi ne na zo wurin Mummy!”

Ta faɗi tana nuna masa hannunta da ya ƙone. Baba Habu ya kama baki cike da tausayawa marainiyar Allahn yace.

“Assha! Assha! An ya kuwa Auwwa tana so ta gama da duniya lafiya?”

Ita dai bata sake ce masa komai ba, sai zubar hawaye da take. Saboda ji take ma kamar yanzu ta yi raunin. Baba Habu ya buɗe mata ƙofar tare da faɗin.

“Shigo Maimunatu! Sannu!”

Ta shiga cikin katafaren gidan tana ɗingisa ƙafarta ta hagu.

“Ita kuma ƙafar me ya sameta?”

Baba Habu dake rufe ƙofa ya tambaya. Sai ta tsaya tana faɗin.

“Yau da safe na tashi tana min ciwo!”

“Sannu kin ji”

Sai ta gyaɗa kanta tana nufar cikin gidan. Da ƙyar ta iya buɗe ƙofar falon shiga cikin gidan, sannan ta shiga da sallama. Mutum ukun dake cikin falon suka amsa sallamar suna dubanta. Matar gidan Mummy ce da yaranta biyu, Sadiq da Maryam.

“Mummy ina wuni”

Ta gaidata tana durƙusawa. Cike da mamaki Mummy ta aje wayarta a kan sofa tana kallon Maimuna ƙawar 'yarta Maryam.

“Lafiya kalau Maimuna. Me ya faru da hannunki?”

Mummy ta tambaya tana duban hannunta na hagu da ta riƙe. Maimuna ta ja hanci tana faɗin.

“Auwwa ce ta ƙona min hannuna, saboda na bayar da kunu bashi!”

“Allah ya saka miki!”

Faɗin Maryam tana nufar ƙawarta. Mummy kuma ta miƙe ta isa gaban Maimunan tana duban hannun nata, kasancewarta nurse a general hospital Haɗejia.

“Mts ba zan iya treating wannan raunin naki ba Maimuna. Abin da za ayi gobe idan kin fita tallar safe, sai ki bawa wata daga cikin abokan tallar taki ta jire miki kayanki, ki je asibiti ki sameni a can!”

Maimuna ta jinjina kai tana faɗin.

“To Mummy. Na gode”

Mummy ta ci gaba da kallon yarinyar cike da tausayawa.

“Kin ci abinci?”

Mummy ta tambaya tana kallon idonta da ya yi ja alamun tana jin yunwa. Maimuna ta sunkuyar da kanta ƙasa tana girgiza shi.

“Maryam ki je ki zubo mata abinci”

Mummy ta bawa Maryam dake dafe da kafaɗun Maimuna umarnin tana zaunawa. Maryam ta gyaɗa kai tana jan hannun Maimuna zuwa jikin kujera.

“Zauna a nan na je na zubo miki”

Maimuna ta zauna. Kuma da ma haka aka saba. Tun bayan fara ƙawancensu da Maryam ta fara zuwa gidan. Har ta kai ga ta saba da mahaifiyarsu da kuma yayan Maryam ɗin wato Sadiq.

Kasancewar Mummy mace ce me tausayi ya sa take tallafawa Maimunan. Tun da ta fahimci cewa tana cikin matsatsin rayuwa. Hakan ya sa a duk sanda rayuwa za ta mata zafi babu inda take kai kukanta da ta wuce gidan su Maryam ɗin. Kakarta Hajja wadda ta haifi mahaifinta kuwa ta tsufa sosai, idan tana zuwa mata da ƙorafi a kan Auwwa zai iya sawa ciwon Hajja ta tashi ta hawan jini.

Kawunta ƙanin mahaifinta kuwa ba sosai ta cika ganinsa ba. Dan idan ba gidan kakar tata dake unguwar Chadi nan kusa da Fantai ta yi ba, ba ganinsa take ba. A wasu lokutan ma sai ta yi sati tana zuwa gidan Hajjan ba tare da ta gan shi ba. Dan shi kullum yana gona ko kasuwa wurin aikinsa.

A wasu lokutan ma shi da kansa yakan zo domin ya dubata. Idan kasuwa ta yi kyau har kyautar kuɗi yake mata, ko ya sai mata wasu daga cikin magungunan cutarta...

“Ƙafar ma ciwo take?”

Tambayar Ya Sadiq ta dawo da ita zahiri. Hakan ya sa ta kalli ƙafarta ta hagu sanna tace.

“Yau da safe na tashi tana min ciwo”

“Ai da ma da sanyi sai a hankali. Ita sickler ba ta son sanyi, ga shi ke kuma rabin rayuwarki a cikin sanyi take... Ki yi ta haƙuri kin ji Maimuna. KADDARA CE!. Kuma da yardar Allah za ki cinye wannan jarabawar!”

Faɗin Mummy.

“Kina shan folic acid ɗinki?”

Ya Sadiq ya sake tambaya. Maimuna ta girgiza masa kai.

“Ban sha ba. Saboda aikin da ya min yawa yau ya sa ban sha tun safe ba. Kuma yanzu da na duba inda nake ajewa sai na ga ta ƙare. Saura palludrine kawai!”

Mummy na latsa wayarta ta girgiza kai tana faɗin.

“Allah ya kyauta”

A lokacin Maryam ta fito daga kitchen riƙe da plate. Ta aje mata a gabanta tana faɗin ga shi Maimuna.

“Na gode”

Maimuna ta mata godiya kamar yanda ta saba. Da yake tana jin yunwa sosai. Sai ta cinye abincin da wuri. Maryam ta bata ruwa ta sha ta gode Allah. Sannan ta godewa Mummy. Da za ta tafi Maryam tace za ta rakata. Sai Mummy tace wa Ya Sadiq ya tashi ya rakasu. Sannan ta bawa Maimuna kuɗin napep. Wanda za ta yi amfani da shi wurin zuwa asibitin.

Su uku suka fita daga gidan. Sai da suka raka Maimuna har layinsu. Sannan suka yi sallama suka juya. A sace Maimuna ta shiga gidan. Ta saka sakata. Sannan ta shiga ɗakinta ta ɗaura gidan sauro. Ta shiga ta kwanta tana jin yanda sauraye ke cizonta. Saboda net ɗinta da yake a ɓule.

Ga kuma sanyi da ya dameta. Ita fa tun ba yau ba ma ta riga da ta san cewa ikon Allah ne ya sa take rayuwa har yanzu. Amma ba dan ikon Allahn ba bata jin me cuta irin tata zai kasance a halin da take ciki, kuma ya ci gaba da rayuwa.

*No.42, Inuwa Wada crescent, Utako, Abuja.*

FARUK POV.

A hankali ya tura ƙofar ɗakinsa da ya fito daga ciki ya rufe. Sannan kai tsaye ya soma taka strais zuwa ƙasa. Abu na farko da ya fara arba da shi a ƙasan shi ne. Matarsa Mariya da kuma ɗansa Hilal.

“Babana”

Ya faɗi yana ɗaukan ɗansa ɗan wata goma sha ɗaya da haihuwa. Kafin ya juya ya kalli matar tasa dake zaune a kan sofa.

“Mary!”

Ya kirata da sunan da shi kaɗai yake kiranta da shi. Mariya ta ɗaga kai ta kalle shi. Kafin ta aje wayarta da take latsawa a kan sofa ta miƙe tsaye.

“Fita za ka yi?”

Ta tambaya ganinsa sanye da kayansa na aiki. Wato kakin sojoji. Kasancewarsa soja. Ya shafa kan yaronsa da ɗayan hannunsa yana faɗin.

“Eh zan fita”

“A dawo lafiya”

Kawai ta faɗi tana karɓar Hilal ɗin dake hannunsa. Sannan ta koma ta zauna tana aje yaron a gefenta. Faruk ya kalleta sanna ya girgiza kansa ya juya ya fita.

Shi har yanzu ya kasa gane abin da yake damun Mariya. Yanzu kusan shekaru uku da aurensu shi da ita. Amma har yanzu babu wata shaƙuwa ta musamman irin wadda ake buƙata tsakanin miji da mata a aurensu.

Bayan kuma auren soyyaya suka yi shi da ita. Kasancewar ita Mariyan ƙanwa ce a wurin abokinsa Mu'az. Kuma ta hanyar Mu'az ɗin ya fara ganinta. Har ta kai ga ya fara sonta. Kuma ba tare da ɓoye-ɓoye ba ya furta mata cewar yana sonta.

Kuma ita ma ta nuna amincewarta kan hakan. Shi ya sa ba a daɗe ba aka yi aurensu. A farkon aurensu ba zai ce babu soyyaya ba. Amma tun bayan da ta samun cikin Hilal komai ya sauya. Duk da da ma can ita ba mace ce me yawan magana ba.

Gaisuwar da sojoji biyun da suke gadin gidansa ke masa ce ta dawo da shi zahiri. Ya dube su yana amsawa. Kafin suka buɗe masa gate ya fita da motarsa daga gidan. Sai da yafara biyawa ta gidan mahaifiyarsa Hajiya dake kusa da nasa gidan.

Ya gaisheta kafin ya wuce wurin aiki. Kasancewar akwai wani aiki na binciken mutuwar abokiyar aikinsu dake gabansu ya sa yana zuwa barrack bai nemi kowa ba sai Mu'az. Aboki, kuma abokin aikinsa.

_Share fi sabillilah❤️_

______________

Za ku iya karanta wannan littafin a ArewaBooks, da ma wasu litattafaina na baya @SalmaAhmad. Sai kuma Wattpad @Salma_Ahmad_Isah.

Saboda page ɗin can za su fi na nan tsayi. And don't forget to follow, like, share and comment.

*Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.*
*CANDY CE🦋.*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*ƘADDARA CE!*

*©SALMA AHMAD ISAH.*
*CANDY🦋*

_ArewaBooks @SalmaAhmad_
_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_

*Paid book*

*02*

*No.53, off Justice Clara Ogunbiyi street, Asokoro, Abuja.*

MU'AZ POV.

Mutum biyar ne zaune a kan dinning table suna yin breakfast. Shi kaɗai ne a cikinsu yake cin abinci da hannunsa. Yayin da kowa yake ci da spoon. Mahaifiyarsu Hajiya Hauwa, wadda suke kira da Mummy ce ta dube shi.

Yanda ya dage yake cin abincinsa bil haƙƙi da gaskiya. Dan idan kana so ku saɓa da Mu'az a ƙi ba shi abinci lokacin da yake jin yunwa. Idan kuma kana so ka burgeshi ka masa kyautar abinci ka ga ƙauna. Shi da abinci 5 and 6 ne.
Chapter 2 · 0% Book details