← Book details Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 22

Sashe 18

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muktar ya karɓi wayar da dukkan zumuɗin duniya. A zatonsa zai ga abin da zai kawo ƙarshen matsalar ne. Bai sani ba cewa yanzu ne ma matsalar za ta soma. Saboda tonuwar asirin makashin ba ya nufin zuwan ƙarshen matsalar. Sai dai ma ya zama wani sabon mafarin tarin matsaloli.

Da farko da ya ga videon da fuskar macen dake cikinsu bai yarda ba. Sai da ya dawo da shi baya ya sake kalla, ya sake sakewa, wai dan ya tabbatar da abin da yake gani ko gaskiya ne. Duk da sau ɗaya ya taɓa ganin matar Faruk ya ganeta. Saboda kwanaki da yake ta neman layin Faruk ɗin ba ya samu ya sa ya tafi gidansa. Kuma a nan ya fara ganinta. Duk da ba wai ya tsaya ya ƙare mata kallo ba ne a wancan lokacin ya ganeta a nan.

Kuma idan zai iya tunawa, Faruk ya sanar da shi cewar Mariya matarsa ƙanwar Mu'azzam Gimba ce. Kuma ya san waye Alhaji Jibrin Gimba Gashuwa GG. Mutumin arziƙi me halin ƙwarai. Me dattaku da halin girmamawa ga naƙasansa ba ma ga wanda ke samansa ba. Lalle akwai magana!.

Yanzu me zai sa matar soja. Ƙanwar soja, 'yar babban mutum kamar GG ta aikata garkuwa da ɗan adam, da kuma kisan kai?. Gaba ɗaya ya kasa ganewa. Idonsa ya ɗaga ya kalli Abdul dake faɗin.

“Lokacin da suka tsayar da motarsu a ƙofar gidan nan na fito. Ganin suna shirin saceta ya sa na yi saurin komawa gida, na ɓuya a bayan ƙofa na naɗi wannan videon...”

Idonsa ya sake ɗaukewa daga kan Abdul ɗin. Sannan ya mayar da shi kan wayar ya na kallon bidiyon a karo na barkatai. Kansa ya jinjina yana miƙawa Ali wayar. Wai ko shi ma zai kalli videon dan ya tabbatar da fuskar wa cece a videon.

MARIYA POV.

Kamar yanda ta saba damawa Hilal custard haka yau ma shi ta dama masa. Sannan ta haɗa shi da shi. Wai ko ya yi shiru kunnuwanta su huta da kukan da yake mata tun safe. Tana saka masa baby bottle ɗin a baki ya yi sarin saka hannunsa ya dafe ya fara sha.

Ta juya idonta cike da gajiyawa da halin yaron. Ita ba dan tana so ta sadaukar da shi ga shaiɗan ba ma da ta kasheshi rana ɗaya kowa ma ya huta. Ba jimawa da fara shan custard ɗin nasa tafara jin ɗoyi. Hakan ke nuna mata cewar kashi ya yi.

Cike da jin haushi ta sa ɗan yatsanta ta dungure masa kai tana hararsa kamar ta samu abokin faɗanta. Ai ko ka zauna da shi daga nan har zuwa sanda ub*nka zai dawo ya wanke maka. Dan ni bani da wannan lokacin.

Ta faɗi a zuciyarta tana tashi daga kan kujerar da take zaune. Ta haye sama ta barshi zaune a falo yana shan custard ɗin. Juyawa ta yi ta saka sakata a ƙofar ɗakinta bayan ta shiga ciki. Ta juyo tana baza idonta a cikin ɗakin. Saboda jikinta ya bata cewar Lawan abokinta na ƙungiyar bayin shaiɗan na cikin ɗakin. Kuma shi ne dalilin da ya sa ta kulle ƙofar ɗakin.

“Gani a nan”

Ta juyo muryarsa a bayanta. Hakan ya sa ta juya. Tsaye ta ganshi a jikin ƙofar yana kallonta, fuskarsa ɗauke da murmushi. Ita ma murmushin ta yi tana nufarsa.

“Saƙo ne daga fadar shugaban bayin shaiɗan!”

Jin hakan ya sa fara'ar dake fuskarta ta ɗauke. Ta maida hankalinta duka kansa, domin jin saƙon da ya sa Wahash ya aiko shi gareta.

“A jiya Shugaban bayin Shaiɗan ya sa ɗaya daga cikin bayin shaiɗan ya je ya kashe wannan ɗan sandan. Amma kuma sai aka yi rashin sa'a ya sha. Kuma a yanzu haka yana da hujjar da take nuna cewa ke ce kika sace Munira, sanin cewa ke ce kika sace Munira na nufin ke ce wadda kika kasheta...”

Cike da razani Mariya ta zaro idonta. Ganin Lawan na murmushi ya sa tace.

“Amma Lawan me ya sa za ka na murmushi a cikin irin wannan yanayin?”

“Haba rezor. Ai abin bai kai mu tada hankalinmu ba. Kada ki manta da cewar shaiɗan na tare da mu. Da ƙarfin tsafin da ya bamu ni da ke za mu iya kawowa ƙarshen ɗan sandan nan”

Idonta ta juya tana jin kwanciyar hankali ta fara nufo inda take.

“Yaushe za mu je gare shi ke nan?”

“Da zafi-zafi a kan daki ƙarfe. Dan haka a daren yau zai baƙunci barzahu. Gobe da safe sai dai a samu labarin jana'izarsa!”

Mariya ta yi murmushi.

“Sai na jika zuwa an jima”

Lawan ya yi murmushi. Kuma ba tare da ya sake cewa komai ba ya ɓace daga ɗakin. Mariya ta zauna a bakin gadonta. Abin da ya shiga tsakaninta da Munira a wacan ranar na yawo a cikin tunaninta.

*Wata ɗaya da ya wuce...*

*BB Paradise Hotel, Abuja.*

A gaggauce Munira ta fito daga cikin motarta, wadda ta faka a parking lot, bayan da ta shigo harabar hotel ɗin. Kuma ba komai ya sa take saurin ba face saƙon gaggawa da tasamu daga wurin saurayinta Mubarak.

Da yake ya faɗa mata lambar ɗakin da yake ciki sai bata sha wahalar neman lambar ɗakin ba. Kai tsaye ta wuce zuwa ɗakin. A bakin ƙofar ɗakin da ya bata lambarsa ta tsaya. Sannan ta yi knocking. Ta ja baya tana jiran ya zo ya buɗe. Jim kaɗan aka buɗe ƙofar daga ciki, idonta ya sauƙa a kan Mubarak ɗin da ya buɗe ƙofar. Murmushi ya mata, sannan ya buɗe ƙofar gaba ɗaya tare da faɗin.

“Shigo mana My love”

Fuska ta ɗaure. Dan da ma sun samu matsala kwanan baya, yanzu kuka da ya kirata yace yana son ganinta sai ta yi zaton yana cikin wani hali ne.

“Me ya sa zan shigo ciki?”

“Ke dai ki shigo. Magana nake so mu yi”

Kamar ba za ta amince ba. Can kuma sai ta gyaɗa kanta. Sannan ta raɓa shi ta wuce. Mubarak ya kulle ƙofar ɗakin ya biyo bayanta. A tsakiyar ɗakin ta tsaya ta fuskance shi.

“Wace magana za mu yi?”

Ta tambaya fuskar nan a haɗe. Duk da dama can haka yanayin fuskarta yake, kasancewarta soja. Mubarak ya yi murmushi.

“Sai kace ina korarki? Ko ba komai ai kya zauna mu tattauna ko?”

Ta sake ɓata rai.

“Mubarak! Ba na son wasa da hankali. Kawai ka faɗi abin da yake bakinka... Ina da abin yi a barrack!”

Mubakar ya sunkuyar da kansa.

“Shike nan tun da kin dage My love. Da ma, ina so in baki haƙuri ne, na gane cewa ni ne me laifi, da fatan za ki yafe min!”

Ta kalle shi na sakkani. Kafin ta ɗauke kai tana harɗe hannayenta a ƙirji.

“Da ma ni ban ƙullaceka ba ai. Kawai dai na ji haushin abin da ka min ne!”

Mubarak ya yi murmushi ya na kamo hannayenta.

“To ki yi haƙuri. Ba zan sake ba”

Munira ta yi saurin janye hannunta da ya riƙe.

“Mubarak wai sau nawa zan ce maka ba na so ka na riƙe hannuna?. Ba na so ka na taɓani irin haka, duk wanna abin kamata ya yi mu bari sai bayan aure.”

Mubarak ya sake kamo hannunta.

“My love ya kamata ki fahimceni. Wai kwana nawa ya rage auren nan namu ne? Ki sani fa cewa baki da miji bayan ni.”

Ta sake janye hannunta.

“Mubarak kar ka sake taɓani. Ba na so”

Ta faɗa tana ja da baya. Ya nufota yana shirin rungumeta ta kauce. Sannan ta hankaɗa shi baya ta fice daga ɗakin da gudu. Kuma a sanda ta fita daga ɗakin, ƙaddarar da za ta kawo ƙarshen rayuwarta ta wanzu.

MARIYA POV.

Zaune suke a cikin motarsu da suka faka a harabar BB hotel ita da Lawan. Lawan ne zaune a driver seat. Yayin da ita kuma take zaune a ɗayar kujerar. Dukansu sanye da baƙaƙen kaya. Baƙar hand glove ta ɗauka ta saka a hannunta. Sannan ta ɗauki baƙar p-cap ta saka a kanta. Ta ɗora hular hoodie ɗin dake jikinta. Ta juyo ta kalli Lawan da yake rufe fuskarsa da glasses.

“Mu je Rezor”

Lawan ya faɗa yana buɗe ƙofar motar. A tare suka fita daga cikin motar. Suka nufi ƙofar shiga hotel ɗin ta ƙofar baya. Kai tsaye ɗakin da Vishal Kumar ya kama suka nufa. Saboda da ma shi ne target ɗinsu. Kuma Wahash ne ya aikosu domin su zo su kashe shi. Saboda ya saɓa dokar ƙungiyarsu. A dai-dai ƙofar ɗaki me lamba 24 suka tsaya. Mariya ce a kan gaba, Lawan kuma na tsaye a bayanta.

Ita ta ɗaga hannunta ta ƙwanƙwasa ƙofar. Suka tsaya suna jiran a buɗe. Suna jin alamun za'a buɗe ƙofar suka gyara takunsu. Vishal na buɗe ƙofar Mariya ta kai masa wani naushi a hanci. Hakan ya sa ya yi baya yana dafe hancinsa da ya fara zubar da jini.

Yayin da Mariya da Lawan suka shiga cikin ɗakin ba tare da sun rufe ƙofar ba, dan sun san cewa ba jimawa za su yi ba. Vishal na ganin fuskokinsu ya zaro ido. Sannan ya sauƙe hannunsa daga kan hancinsa. Ya yi kan Mariya zai daketa.

Amma yana zuwa daf da ita ta kama hannunsa da ya ɗaga zai dake ta shi, ta murɗe hannun har sai da Vishal ya yi ƙara. Sannan ta sa ƙafarta ta daki ƙafarsa. Kafin ta sa hannunta ta riƙo gashin ƙeyarsa, ta ɗaga ɗaga kansa sama yana kallonta.

A hankali ta kai hannunta da bata riƙe gashin kansa da shi ba, ta ɗaga harshenta kaɗan, ta ɗauko wata sabuwar reza da har ɗaukan ido take a cikin hasken ɗakin. Ta ɗaga sama, sannan ta yanka wuyan Vishal da ita.

A dai-dai lokacin Munira da ta fito daga ɗakin Mubarak da gudu ta dakata a ƙofar ɗakin. Ganin an yi kisan kai ya sa ta ƙwaka ihu. Ihun da ta ƙwala ya sa Mariya da Lawan juyowa suka kalli bakin ƙofar. Ganin fuskar Mariya ya sa tsoro da tashin hankalin Munira ninkuwa.
Chapter 18 · 0% Book details