← Book details Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 22

Sashe 12

Kaddara Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanyin iskar ya busa a kan fatar jikinsa. Hakan ya sa ya motsa ƙafafunsa dake cikin takalmi. Kafin ya rintse idonsa dake rufe, saboda wani ciwo da kansa ya fara lokaci guda. Hannunsa na dama ya ɗaga ya ɗora a kansa. Sannan ya ja iska ta bakinsa cike da jin zafin ciwon kan.

A hankali ya buɗe idonsa. Sannan ya rufe, ya kuma buɗewa, ganin gari ya yi haske ya sa ya yi saurin miƙewa zaune. Ya dafe kansa dake masa ɗan karen ciwo. Da ƙyar ya miƙe tsaye ya shiga banɗaki. Bayan wani lokaci ya fito. Ya yi sallahr asuba da ta wuce shi. Bayan ya idar bai miƙe daga kan dardumar ba sai da ya yi ta jero istigfar.

Saboda rashin yin sallahr a kan kari. Haka ya zauna a kan dardumar yana nazarin da bai san na miye ba. Har yanzu yana jin kamar akwai abin da ya manta, kamar akwai wani abu da aka goge daga cikin tunaninsa. Amma kuma ya kasa tuna miye. Jin an buɗe ƙofar ɗakin ya sa ya ɗaga kansa ya kalli Mariya da ta shigo. Ganinsa cikin wannan yanayin da ya kwana da shi a jiya ya sa ta yi miskilin murmushi.

“Sai yanzu ka farka?”

Ya kalleta. Amma bai ce mata komai ba. Dan ji ya yi bakinsa ya yi nauyi, ga kansa da yake sarawa.

“Ya Mu'az ya zo yana waje. Yace ya jika shiru ba ka je barrack ba, kuma ya kira wayarka baka ɗaga ba, shi yasa ya zo!”

Da ƙyar ya iya miƙewa tsaye. Sannan ya sa hannu ya cire rigar jikinsa yana faɗin.

“Ki ce masa ina zuwa!”

Mariya ta juya kai, sannan ta fita daga ɗakin. Ta dawo ƙasa. Idan ta bar Mu'az da Hilal zaune suna wasa. Ganin ta fito ita kaɗai ya sa Mu'az ya ɗaga kai ya kalleta.

“Yana ina?”

Ta zauna a kan kujera tana faɗin.

“Wanka zai yi. Amma yace yana zuwa”

Mu'az ya gyaɗa kai, sannan yace.

“Me ya same shi wai?”

“Kwana ya yi da ciwon kai, shi yasa ya makara”

Ya kuma gyaɗa kansa yana ɗaga Hilal. Suka ci gaba da wasa da Hilal ɗin, har zuwa sanda Faruk ya sauƙo sanye da kayan aikinsa, wato kakin sojoji. Kana ganinsa ka ga wanda ba ya cikin nutsuwa, ko kuma mara lafiya.

“Kaigama!”

Mu'az ya kira yana miƙewa tsaye, yana riƙe da Hilal. Faruk ya ɗan yi murmushi yana lumshe idonsa da kalarsa ta sauya. Sannan ya buɗe shi a kan Hilal.

“Idan kan naka bai daina ciwo ba za ka iya komawa ka huta”

Faruk ya girgiza kansa.

“A'a. Zan iya zuwa barrack. Mu je kawai”

“Kuma fita za ka yi ba tare da ka ci abinci ba?”

Mariya dake gefe ta faɗi. Hakan ya sa suka dubeta a tare.

“Yanzu na makara. Ki aje min abincin dare kawai”

Faɗin Faruk.

“A'a ka zauna ka ci abincika kawai”

Cewar Mu'az.

“Bana jin cin abincin ne. Mu je kawai, zan ci abincin a barrack”

Mu'az ya jijina kansa, sannan ya miƙawa Mariya Hilal. Suka mata sallama suka fita a motar Mu'az. Suna tafiya a hanya Ƙaddara tasa Mu'az tsayawa a wani boutique me sunan ‘UMMUL BANAT BOUTIQUE’. A sanda motar ta yi parking a harabar boutique ɗin Faruk ya ɗaga kansa ya karanta sunan boutique ɗin. Sannan ya kalli Mu'az yana faɗin.

“MJ me za mu yi a nan?”

Mu'az na cire seat belt ya amsa da.

“Na'im ne yace na sai masa sweater”

“Okay mu je”

Ya faɗa yana buɗe ƙofar motar. A tare suka nufi ƙofar shiga boutique ɗin. Boutique ɗin da ƙaddarar Mu'az ke zaune a ciki. Boutique ɗin da zuwansa cikinsa zai sauya rayuwarsa gaba ɗaya.

Kamar yanda Na'im ya wassafa masa yanayin sweatern da yake so ita ya ɗauko masa har guda biyu. Rigunan na riƙe a hannunsa suka nufi wurin cashier. Ya juya kansa yana yi wa Faruk magana. Ya ji ya ci karo da mutum. Kuma a lokaci guda abinda ke hannun mutumin da sukayi karon, wanda yake da tabbacin ya fishi tsayi ya zube a jikin rigarsa.

A lokaci guda zuciyarsa ta tafarfasa har ta fara shirin ƙonewa. Hakan ya sa ba tare da ya duba da wa ya ci karo baya ɗaga hannunsa da bai riƙe rigar da shi ba, ya sharara wa budurwar dake tsaye a gabansa mari.

Wata iriyar ƙamewa ta yi. Ta saki kofin ruwan dake hannunta, wanda ruwan cikin ya zube a jikin rigarsa. Sannan ta ɗora hannunta na dama a kan kuncinta. A take hawaye suka soma zubowa daga raunannun idanuwanta. Da ƙyar ta iya ɗaga idonta ta saka su cikin nasa.

Kuma shi ma sai a lokacin ya samu damar kallonta. Wata farar matashiya ce, da a shekaru ba za ta ɗara Mima ba. Hawayen da suka wanke mata fuska ya sa ya ga fuskar tata har wani ƙyalli take. Sanye take da farar Oxford shirt. Da kuma baƙar straight skirt. Ta yafa baƙin veil a kanta. Kuma ya lura da kamar kayan su ne wanda masu aikin wurin suke sakawa.

Ƙwayar idonta dake rawa a kan fuskarsa, da kuma hawayen da ya taru a cikin idonta da yake ƙyalle saboda hasken fitilun wurin yasa ya ji kamar yana nitsewa cikin wani abu me kama da gajimare. Akwai rauni, haɗe da neman taimako a cikin idonta. Sannan ya ga fata da kuma sa rai a cikinsu. Yanayin yanda ta turo fatar bakinta ta ƙasa zai sa ka san cewa shagwaɓɓaɓɓiya ce tun tana da ƙarancin shekaru, ko kuma wadda gata ya yi wa yawa.

“Mu'az!”

Faruk ya kira yana taɓa kafaɗarta.

“Humm!”

Ya amsa kamar wanda ya dawo daga WATA DUNIYA. Ya kalli Faruk, sannan ya sake kallon budurwar dake tsaye a gabansa har zuwa lokacin. Tana dafe da kuncinta. Ga hawayen da take zubarwa, sannan bakinta da ta turo cikin shagwaɓa yana rawa kaɗan. ‘Oh lord have mercy!’ Ya faɗi a zuciyarsa.

“Wai me ya faru ne?”

Faruk ya tambaya. Amma sai Mu'az ya kasa magana. Ya ci gaba da kallonta. Har zuwa sanda wata murya ta kira sunan.

“Halima!”

Daga bayansa. Hakan ya sa ya juya, yayin da ita kuma budurwar me suna Halima ta kalli Kairat ƙawarta da ta kirata. Dan haka sai ta sauƙe hannunta daga kan fuskarta. Ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta raɓa Mu'az ta wuce wurin Kairat.

“MJ!”

Faruk ya kuma kira. Mu'az ya juyo ya kalle shi. Sai kuma ya kalli rigunan da yake riƙe da su, haka kawai ya aje rigunan a kan wasu kaya. Ya nufi hayar fita. Kai a kulle Faruk ya bi bayansa. Dan shi sam bai ga tahowar yarinyar ba, ballantana ya ga sanda suka yi karo da Mu'az ɗin.

“Me ya faru wai?”

Kairat ta tambayi Halima da har zuwa lokacin bata daina hawaye ba. Sai ta juyo mata da ɓarin fuskarta na dama. Inda shatin hannun mutumin da ya mareta ya fito har guda huɗu. Wurin har ya yi ja. Ya kuma kumbura.

“Na shiga uku? Wai wancan sojan ne ya mareki haka?”

Kairat ta tambaya tana zaro ido. Tare da kama gefen fuskar ƙawarta tana ganin yanda wurin da aka mareta ya yi ja. Cike da shagwaɓar da ta zame mata jiki Halima ta gyaɗa kai tana goge ƙwalla. Sannan cikin murya me sanyi tace.

“Haka kawai bawan Allahn nan ya sharara min mari, wai dan na bige shi. Kuma fa sai da na kauce masa, shi ne bai kula ba!”

“To Allah ya saka miki. Ya hana masa sukuni saboda marainiyar Allah da ya cutar!”

Kamar an kunna famfo haka ta ci gaba da zubar da ƙwalla. Kuma da ma ita can haka take. Abu kaɗan kan iya sakata kuka, ballantana yanzu da ta sha mari. Har zuciyarta ta jawa wannan azzalumin sojan Allah ya isa ta fi sau dubu.

MARIYA POV.

Kukan Hilal da ya cika ɗakinta ne yada ta ja dogon tsaki. Sannan ta juyo ta kalle shi. Yanayin zaman da ya yi kaɗai ya sa ta gane cewa bayan gari ya yi a cikin diapers ɗin dake jikinsa. Wani tsakin ta ja, sannan ta ci gaba da latsa wayarta hankali kwance. Kukan nasa da ya ci gaba da tashi ya sa ta kalle shi a hasalle, sannan ta daka masa tsawar da za ka dafa ƙur'an kan cewa ba ita ta yita ba.

“Ka rufe min bakinka a wurin!”

Amma bai yi shirun ba. Sai kukan nasa da ya ƙarawa volume. Wani dogon tsakin ta kuma ja. Sannan ta miƙe tsaye ta fita daga ɗakin, ta kulle ƙofar ɗakin. In yaso ya je can ya yi ta yi shi kaɗai.

Tana taka stairs tattoo ɗin dake bayan wuyanta ya soma haske. Hakan ya sa ta ƙame a wuri ɗaya. Domin ta san kira ne daga shugaban bayin shiaɗan. Bata raba ɗayan biyu ba suffar Wahash ta bayyana a tsakiyar falo. Hakan yasa ta sauƙa ƙasa da gudu. Sannan ta yi saurin zubewa a ƙasa, ta yi wa shugaban bayin shaiɗan sujjada.

“Giram gareka Wash. Duk wani shugaba da ba kai da shaiɗan ba ba a kan gaskiya yake ba!”

(A'uzubillah!)

Wahash ya sa hannu ya ɗago da ita, ya miƙar da ita a kan ƙafafunta. Amma kanta a ƙasa cike da girmamawa irin tasu ta 'yan wahala a duniya.

“Rezor!”

Wahash ya kira. Hakan ya sa ta ɗaga idonta ta kalli fuskarsa.

“Mijinki da ɗan uwanki, da kuma wani jami'in ɗan sanda na shirin haƙa ramin binne kansu!”

Cike da rashin fahimta tace.

“Ban gane ba shugaban bayin shaiɗan!”

Wahash ya juya bayansa. Sannan ya yi taku biyu gaba. Ya ɗan juyo kaɗan ya kalleta.

“Duk da na sa a goge duk wata shida da za ta nuna cewar ke kika kashe Munira da kuma Danesh sai da suka yi ƙoƙarin zaƙulo wani abin. Yanzu haka shi ɗan sandan da suka ɗora a kan aikin yana ta binciken gano wanda ya kashe Danesh da Munira, domin kuwa duk sun gane cewa makasan nasu mutum ɗaya ne ko biyu. Ko ma sama da haka, kuma da alama suna daf da cimma gano ki. Ganoki kuma yana nufin gane ƙungiyar jajayen bayin shaiɗan!...”

Mariya ta girgiza kanta da sauri, sannan ta tsaya avbayan Wahash tana faɗin.
Chapter 12 · 0% Book details