← Book details Jarabta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 49

Sashe 46

Jarabta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanaki sunja lokaci nata tafiya yau kimanin wata daya da kwanaki biyar kenan rabonta da Khaleel, yaukam zazzabin data tashi dashi ne yasa Anty Hindu da kanta ta fadanma Abba nan aka kira Dr, bayan ya dubata yace "maleria ne" magani yarubuta mata Abba yasiyo Anty Hindu tasa tasha, Mum dai zamanta tai afalo tana marking script ko agefen kwalanta, Farida kuma ta debomata abinci dan sosai tabata tausayi takawo mata. (har yanzu fa wanan son dake tsakanin su nanan kawai dai Son Khaleel ne matsalan two sisters dinan)
Wuraren 6 ta tashi na yamma tadanji dadin jikinta, hakan yasa ta shiga bayi tai wanka da ruwan dumi tafito dan pink gown dinta na gida tasa dake tsayama ta a gwuiwa tasaka dogon hijabin ta dake sharan kasa tai sallan la'asar jin anfara kiran magrib yasa tayi sanan tayi azkar din yamma tacire hijabin ta linke ta ijiye ta kwanta akan gado tana maida numfashi, gabaki daya duk tayi wani irin laushi ga jikinta har yanzu da sauran dumi, lumshe ido tayi har bacci yadan soma tafiya da ita sama sama taji ihun Farida daga kasa "oyoyo MK, oyoyoo" da sauri ta tashi ta zauna, kasa hakura tayi tadan mike tsaye tareda saka silifas tabude kofa kadan maganganu taji kasa kasa kaman muryan su Abba, komawa tayi ta zauna abakin gado gabanta na faduwa sosai, bude kofa akayi hakan yasa ta daga kai Farida ne tashigo dakin da gudu jikinta har wani rawa yake tana murmushi tace "Mk yadawo Islam kinga yanda yay kyau kuwa, laa banma bashi ruwa ba" da sauri tajuya tafita daga dakin, harara Islam tabi bayanta dashi jin wani irin kishi ya turnike ta saikace mijinta ne yazo taja tsaki, tashi tayi afusace taje gaban wardrobe dinsu wani ubansu soft material taciro blue da akabishi da zanen flowers gold, zama tayi agaban madubi ta chanchara uban kwalliyan da ita kanta batasan ta iyaba tasaka red janbaki tadan shafa lip gloss akai hakan yasa lips din na wani irin maiko maiko yana kyalli kaman sabon candy da aka gamayi, tashi tayi tabuga uban dauri sanan ta dauko turaren khumar da Husna ta bata na matan aure ta shafe jikinta dashi dakin yadau kamshi sanan tadan kalli kanta amadubi dudda tarame amma baihana kayan karbanta ba tareda fito da kyanta da dirin ta dan sun dan kamata sosai, takalmi tazira sanan tabude kofan tafito tana wani irin kamshi akan bene ta tsaya hango Farida datayi ta zauna akan kujeran dake kusa danashi tanata mai hira, ta wutsiyar ido ya hangota har wani irin ajiyar zuciya ya sauke sabida yanda yay kewan ta yawani juya mata baya yabiye ma Farida suna hira harda dariya, wani irin abune taji ya tokare mata zuciya kasa daurewa tayi takarasa sakkowa daga benen da sauri ta tsaya tana kallonsu, ganin duk sunmaki lura da ita babu wanda yace mata Kala yasa taji zuciyar ta na tafarafasa ai wlh yau saita nunama Faree nan Khaleel mijinta ne ehe, da saurin ta harda wani dan gudu gudun ta taje kaman daga sama tawani fada jikinshi ta kankameshi tana kukan shagwaba ahankali tace "Ya Khaleel nai kewan ka sosai" wlh ya tabbatar da inda yay alwala babu abinda zai hana alwalan karyewa wanan irin runguma haka damafa adaddafe yay wanan wata dayan a Lagos, wani irin kara shigewa jikinshi takeyi tana hahhade kirjinsu tare, kasa daurewa yayi ya sanya hannayen shi duka biyu yay cuddling nata tareda sakin wani irin sassanyar ajiyar zuciya, tashi Farida tayi tabar falon tanajin wani iri iri hakan yasa Islam takara bin bayanta da harara tana tura baki taredayin lamo ajikinshi tana shakan kamshin turaren dayake yi.
[7/2, 2:19 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

79...

Ganin Farida tabar falon tai sama yasa yaciro ta daga kirjinshi murya chan kasa yace "me haka nazo nabaki takardar ki kin wani shishigemini jiki, is over, today we are going our separate ways abinda kikeso kenan ai, bakiga nida Farida munyi making perfect coup.." daura hanunta tayi a bakinshi tareda kara matsowa cikin jikinshi tana girgiza mai kai tana turamai baki a shagwabance, "Hasbunallahu wa ni'imal wakil yarinyar nan naneman kasheshi ne wai" Ahankali ta zame hanun daga kan bakinshi ta kwantar da kanta a kirjinshi kaman wata baby tareda sakalo hannayenta ta bayanshi tana wani irin sheshekan kuka mai taba ran miji tace "dan Allah karke sakeni, wlh natuba bazan karaba, am really sorry, dan Allah karka rabu dani i cannot live without you, u are my endocrine" idan ba kana kusa dasu bane bazaka tabajin abinda suke cewaba, da kyar ya tattaro dan karfin daya rage mai dan tagama kashemai jiki ya ture ta yace "am wicked fa kin manta ne, tunda na shigo rayuwar ki matsaloli kawai naketa jamiki" hannunta takai takama kunnuwanta biyu, bilhakki take mai kuka tana girgiza mai kai tace "nai kuskure babba dana kalli fuskar mijina, mai gidana, mai sona abin alfahari na nagaya mishi wayan nan munanan kalaman, dan Allah ka gafarceni, inda inada karfin maida lokacin baya dana tariyo wanan lokacin na goge maganar danayi da eraser, Ya Khaleel i love you please karka rabu dani, ka hukuntani amman dont live me my endocrine" ahankali ya mika hannu yacire hanunta daga kunen nata data rike ya daga habarta yana kallon kwayar idonta dawata irin murya ya kashe mata ido daya yace "dole kam inhukun taki dawan nan bakin mai tsiwa, amma agado ake hukuncin" a kunyace ta fisge fuskarta ta fada kirjinshi tana murmushi kasa kasa, bakinshi yakai saitin kunenta yace "kinman ta ina gidan sirikai nane ko kike ta mammaneni haka, sokike na saki layi ko" girgiza kai tayi tareda sakinshi tana murmushi ahankali, hanunshi yasa ya shafo janbakin kan lips dinta yakai yatsar bakinshi yana lasa yana wani irin kallonta yace "jeki dauko abubuwan ki mutafi gidan mu"
[7/3, 10:24 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

80...

Tashi tayi ahankali ta mike tsaye tana kallonshi kaman yau tafara ganinshi, shima ita yake ma wani irin kallo da kyar ta iya janye nata idon tai stairs tana murmushi kasa kasa, haka yabita da kallo harya dena hangota, shi kadai yasan yanda yakeji akan matar nan nashi.
Kofar dakinsu ta tura ahankali ta bude babu kowa aciki, dan ajiyar zuciya ta sauke ta shigo yan tarkacen ta tahada a jakarta ta sanya hijabi tafito, dakin Mummy tai sallama ta shiga Farida ta gani tai filo da cinyar Mummy idanunta sunyi jajir dasu, maida kofar tayi tarufe takaraso ciki ta tsugunna agaban Mummy tana wasa da zip din jakarta ahankali tace "zamu tafi Mum" harara Mumy tabita dashi kafin ta tabe baki tace "Allah yayi, to agaida gida" ahankali ta mike tsaye ta juya zata fita tana satan kallon Farida dataga ta lumshe ido, harta daura hanunta akan handle zata mudra taji Farida tace "Islam wait" waigowa Islam tai ahankali, sakkowa Farida tayi daga kan gadon, zuwa gaban Islam tayi ta rungumeta tsamtsam hakan yasa Islam ma ta rungumeta back tareda sauke ajiyar zuciya, wani irin zazzafan hawaye Farida taji yazubo mata da sauri tasa hannu ta share tana daga idanunta sama kokarin hana kanta kukan datake ji, bakinta takai kunen Islam dawata irin murya chan kasa tace "please take care of Mk, dan Allah ki kula dashi Islam, Allah baku zaman lpy" sakin Islam tayi takoma kan gadon ta kifa kanta akan filo tana sheshekan kuka sosai, wani irin hararan bakin ciki Mum tabita dashi kafin taja dogon tsaki ta kalli Islam din dako kwakkwaran motsi takasa kaman wacce tai mutuwar tsaye tace "bazaki fita daga dakin nan ba ku tattara kubar gidan nan kosai kun dawo mata da ciwon datake" wasu irin zazzafan hawaye ne suka zubomata kafin ta juya da sauri tabar dakin, falon Abba tayi bayan ta tsaya ta goge fuskarta tass, suna tare da Anty Hindu kafin ma tai magana Abba yace "zaku wuce kenan?" gyadamai kai tayi, Anty Hindu ta riko hannunta tace "Alhaji ka sauka gamunan zuwa" fita yay daga dakin Anty Hindu kuma taja hannunta zuwa dakinta, wasu magani dake robobi daban daban tadauko mata tace "kin gansu nan yau dinan naje airport na karbo su kawata daga Cameroon nasa ta turamin sabida nabaki, wlh idan baki shaba sainazo har gidanki na bugi kudina dakika sa nai asara" tagama maganan tana kokarin bude wani gora wani magani tace "shanye wanan agabana" karba tayi tasha tana yatsine fuska sabida dadi dadi da ne dashi, murmushi Anty Hindu tayi ta karbi goran daga hanunta tace "gud girl kinga kafin kukai yafara aiki ajikinki, tashi muje ki kula da mijinki da kyau, kimai biyayya, karki sake kisa zancen Farida aranki duk wanan hauka datake dazaran tasami miji, tasami mai sonta zata mata dama waye Khaleel ne, kizama mai hakuri da juriya, mara korafi kuma, kindaiga abinda yawan korafi da masifa yajamin sakoni akayi" dan murmushi tayi batare data bari ta ganta ba, karban jakanta tayi ta sakamata magungunan aciki sanan ta riko hanunta suka sauko falo inda Khaleel da Abba keta magana anatse, har mota suka rakasu suna musu addu'a suka tafi sanan suka koma cikin gida, dakin Mum Abba yabude ganin Farida dayayi akan gado tana gunjin kuka batare datamaji shigowan shiba yasa yajuya kawai yafita yana girgiza kai lamarin Farida sai du'ai shifai yasan ba randa zaiyi salla dabazai rokan mata Allah yakawo sauki cikin lamarin nan nataba, tareda nemamata miji nagari, yasan Allah maji rokon bayinsane watarana sai labari.
Chapter 46 · 0% Book details