← Book details Jarabta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 49

Sashe 10

Jarabta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tun jiya da daddare duk ringing din da wayar ta zaiyi da gudu take dubawa taga ko bakuwar number ne amma duk wayanda tasani ne, babu sallan dazatayi da bazatai addu'a Allah yasa ya kirata ba, ko bayi zata shiga wayar na hanunta dan Karya kira yaga baa dagaba. Koyau da safe data tashi saida tai mafarkin shi hakan yasa tana bude ido ta duba wayarta bataga any miss call ba tsaki taja duk ranta adagule.
Batai niyyar zuwa Saturday lecture da aka samusu ba amma sabida yanda duk taji batajin dadin komi ne yasa ta tashi tai wanka ta shirya cikin wani brown Abaya da aka bishi da stones ba karamin kyau yamata ba gyale ta yana akai Islam dake nannade cikin bargo tace "ina zaki?" turare ta fesa sanan tadau jaka ta kalli Islam tace "inada Saturday lecture ne, bye baby girl" ahankali Islam tace "bye" tafita tayi dakin Mum ta shiga tamata sallama sanan tafito Bala driver ne ya dauketa suka fita, jakar ta tabude tasake ciro wayar ganin har yanzu babu miss call yasa ta ijiye wayar akan cinyar ta ta dafe kai dan bakaramin daci taji zuciyar ta namata ba, sun kusa kaiwa school ta tuna bata dauko calculator ba sabida bakin ciki gashi calculation course zasuyi hakan yasa tacema Bala "malam Bala please danyi parking agaban super market dinan bari nasiyo abu" gaban wani babban super market Bala yay parking purse dinta da waya kawai ta riko tafito ta shiga ciki, bangaren littatafai taje nan taga calculator ta dauka, wajajen su ice-cream tayi tadanyi tsaki maybe zata dan rage zafi da ice-cream din, fridge din tabude ta ciro ice-cream ta juyo zata tafi wajen biya kaman ance ta daga kai ta hango Khaleel tareda Yusuf sunci sky blue shadda gizna da aka musu dinki half jumper ga wata hula kube sun kafa akai sai kace zasuje biki suna kwasan su snacks da littafi dan zasuje ma Fa'iza visit a boarding school ne. Wani irin farin ciki ne ya lullube zuciyar ta ajiye abubuwan tayi a kanta din accounter tace "am coming" da sauri tai wajen su da murmushi akan fuskarta tace "Hi MK" Yusuf ne yafara juyowa saikuma Khaleel daya dago kai ya kalleta yana kokarin tuna fuskar, kamar zatai kuka ta kalli Khaleel tace "shine baka is kirani bako MK" sai alokacin ya tunata, dan murmushi yay yace "how you?" har cikin ranta takejin muryar shi da yanda yay maganan tace "fine" Yusuf ta kalla sanan ta kalli Khaleel din tace "dan uwanka neko" gyada mata kai yayi Yusuf ta kalla tace "ina yini" cikeda fara'a yace "Lpy Lau sis, yasu Mum nd Dad" purse din hanunta taketa wasa da igiyan sanan tace "suna lpy" dan kallon Khaleel dake kokarin dauko gwangwanin Milo tayi tace "shine baka kirani bako MK" ajiye milon yay a cart sanan yace "sorry battery na was flat jiya ne saisa" murmushi tamai har cikin zuciya sanan tace "okay" Yusuf ne yace "how about nabaki number shi dan ya iya mantuwa kina ganinshi haka, incase ya manta baikirakiba sai kimai flashing ko" kama rigar Yusuf yayi tabaya yanda bazatai ganiba hanunshi Yusuf ya bige ya shiga karanto mata number tana saving sanan ta kallesu tace "okay kayana nachan bye" ta daga musu hannu cike da fara'a, bye suka mata sanan tawuce tatafi, turashi Yusuf yayi yace "at least be a gentle man kabiya mata kudin abinda tasiya" zaiyi magana Yusuf yakara tureshi hakan yasa yajuya yatafi badan son ranshi ba, murmushi Yusuf yay ya dunkule hannu ya saki a iska yace "yess".
ATM card taciro tana shirin biya da POS ya mika nashi, ahankali ta kalli gefenta ganin shine yasa wani dadi ya lullubeta, samata akai a leda aka bata ta karba sanan ta juyo cike da dan kunya tace "thank you, am going to school karnai latti, bye" hannu yadaga mata yana mata calm murmushi dake melting heart tai hanyar fita security ya bude mata kofan.
[6/12, 1:16 AM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

17...
Hararan shi Yusuf yayi daya dawo yace "shine ko abani labari, who is she?" dan yatsine fuska yayi yace "a girl I met yesterday" da sauri Yusuf yace "and??" tsayawa da tafiya Khaleel yayi ya kalleshi yace "and wat, nace jiya muka hadu I just helped her out ne da wani guy ya kwace jakarta shikenan" murmushi Yusuf yay suka cigaba da tafiya chan yace "she is nice" ahankali yace "yea ga shegen surutu ba" dariya Yusuf yayi batare daya kara cewa komiba sukaje suka biya kudin kayan sanan suka wuce school dinsu Faiza.
Tsabagen farin cikin daya mamaye zuciyar ta batamasan me aketayi a class ba dan murmushi kawai take tana kara kallon special number Khaleel datai saving da my superman.

Haka tai wasting 4 hours lecture dinan tunanin Khaleel barinma yanda yawani zo ya mika ATM card yabiya kudin nanne yafi tsumata.
Koda daddare Islam bacci tayi ta barta ido biyu sabida jira take Khaleel ya kirata ganin har 11 bai kirata ba yasa ta dialing number shi har tagama ringing bai dauka ba, sake kira tayi nanma bai daukaba wani iri taji sosai ahankali ta ijiye wayar taja bargo ta kwanta ta rufe ido da kyar bacci ya dauketa.

"Goggo jikan ki yay kawa fa" ajiye maficin datake fifita musu wani dan kasko data daura ruwan shayi akai anan tsakiyar falon ta tayi tace "kai da gaske Yusufa" kallon Khaleel dayay kaman bejishi ba yayi yace "gashi nan ki tambaye shi, wlh Goggo yarinyar badai hankali ba, ai in sha Allah watarana zan kawo miki ita ki ganta" sosai Goggo taji dadi, batace komiba ta sauke shayin daketa uban kamshi ta zuzzuba musu a cup, dauka yayi yay sipping kadan sanan ya ijiye saida yadanyi sanyi sanan ya dauka ya shanye ya goge baki ya tashi ya Kalli Yusuf yace "zanje Gym" kafin Goggo takirashi yafita daga dakin da sauri dan bayason surutun su, part dinsu ya wuce ya shirya cikin kayan gym, wata gym singlet ne dake kama jiki mai ruwan toka tadan budemai kirji sosai yasaka, sai dogon wandon shimin, yasa sport shoe na Nike, yadau wani dan madaidaicin towel ya daura akafada yadau car key da wayar shi, da sport bottle dake cike da warm water na glucose and lime yafita.

"ke Farida, Farida, wai bataji nane" tana zaune a dining itada Islam suna hira taji Anty Hindu na kwala mata kiran nan kaman ana yaki, da sauri ta tashi tana amsawa, sama tayi tai sallama tabude dakin Anty Hindu dake zaune da Dad suna magana, kudi Anty Hindu ta mika mata tace "ki kira bala ya kaiki inda nake siyo fruit a kasuwa yasan wajen kisiyo, babu fruits agidannan yau" karban kudin tayi tajuya tafita daga dakin, dayake tariga tai wanka tunda sassafe yasa Hijab dinta kawai ta dauko da wayarta ta sakko, dining tazo tasami Islam na taya Mum yanka kubewa ta kalli Mum tace "Mumy Anty Hindu ta aikeni kasuwa plz Islam tarakani" Mum ta kalli Islam tace "zaki?" gyada kai tayi "tashi kutafi to, amma kuyi sauri" da gudu Islam tai sama Hijab ta dauko milk daya kai mata gwuiwa tadaura akan atampa dayake jikinta tabita suka fita waje bala ya dauke su suka tafi. Suna zaune a motar takara dailing number Khaleel saida wayar ta kusa katsewa ya dauka, ajiyar zuciya ta sauke mai kara har saida Islam ta kalleta, dawani irin calm voice tace "good morning Mk" ahankali yace "ya kk" murmushi tayi daya bayyana fararen hakoran ta tace "Alhamdulillah" "gud" yafada tareda yin shiru itama shiru tayi, hayaniyar dataji ata bangaren shi ne yasa tace "ina kake haka da ake hayaniya sosai?" wlh kawai dan bayason wulakanci ne saisa amma dis girl is really disturbing him, kaman bazaiyi magana ba chan dai yace "gym" da sauri tace "wani gym?" shiru yayi hakan yasa ta kalli wayar ganin yana kan line har yanzu yasa ta mayar kunne tace "hello are you there" batare daya amsa ba yace "infinity gym, bye gat to go now" Ya katse wayar. Bala ta kalla tace "dan Allah Bala dan kaini infinity gym" da sauri Islam ta kalleta tace "ba kasuwa aka aikemu ba" yarfe hannu sama tayi tace "dalla forget kasuwa, I wanna see my superman face tukun" tabe baki Islam tayi ta juya ta cigaba da kallon hanya, agaban wani babban building da aka rubuta infinity gym ajiki bala yay parking. Hannu Islam ta daura akan kirjinta sabida yanda taji yana bugawa.
[6/13, 8:48 AM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

18...
Chapter 10 · 0% Book details