← Book details Jarabta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 49

Sashe 34

Jarabta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ahankali yatura kofar ya shiga dakin bata kangadon ma hakan yasa ya ijiye teddy akan gado, maganar nurse dayaji tana cewa gently raise your head yasa yaja kujera ya zauna yana kallon kofar bayin, wajen 3 min da zaman shi sanan nurse din tabude kofa ta gunguro ta akeke an chanza mata rigar asibiti zuwa pink amma desame design ne fuskar ta dadan ruwa ga nurse din rike da karamin farin towel a hanunta saida takawo ta bakin gadon sanan nurse din ta gaida Khaleel daya kasa cire idonshi akan Islam dan gani yay bakin yadan sabe jan dayayi ya ragu sosai, tsugunnawa nurse din tayi zata share mata ruwan fuska da towel din hanunta ya tashi tsaye yana tattare hanun doguwar rigar dayasa yace "may i" yay maganar tareda mika ma nurse din hannu murmushi tai tace "sure" tabashi towel din tsugunnawa yayi yana kallon fuskar ta yakai towel din kan fuskar yana share mata ruwan ahankali, lumshe ido tayi tadan saukar da ajiyar zuciya wuyarta ya share sanan ya dauketa ahankali daga kan kujeran sabida karya fama mata ciwo ya mike tsaye yana kallon fuskarta, ahankali tadan bude ido takallai kara gyara kanta tayi akan kirjinshi tasake sauke ajiyar zuciya, kwantar da ita yay akan gado ya rankwafo yamata runfa batare daya dagoba yace "good morning wife" hanunshi dayaji ta rike yasa yadan dago ya kalli hanun, murmushi yamata sanan ya zauna yakai hanunshi kan filon ya budemata yana kallonta, ahankali tasake matso da fuskarta tadaura kan hanun sanan ta lumshe ido tareda sakin ajiyan zuciya takara kankame dayan hanunshi data rike within 1min bacci yay gaba da ita, batare datamaga teddy ba.
Murmushi Nurse din dake tsaye tana kallonsu tayi cikin turenci tace "her mind is at ease anytime u are around, inhar tana ganinka haka kullum zaiyi helping recovery nata" murmushi yamata batare daya dena kallon fuskarta ba hakan yasa nurse taje ta bude wardrobe din dakin ta ciro wani ruwa dake cikin farin gora ta ijiye akan table din gefen gadon tace "wanan ruwan zata sha dazaran ta tashi, bari naje inta tashi ka danna mana alerm" tana fadin haka tajuya tafita daga dakin, yadade yana kallonta kafin ya daura kanshi agefen gadon shima bacci yay gaba dashi dan jiya kasa bacci yayi sabida tunanin ta.

Yau kwana su sha bakwai a asibitin, sosai condition din Islam ke improving dan bakin tass ya warke babu kumburin babu zubar yawu tana iya hadeye magani yanzu, cikin ne yanzu ake kai, kullum Khaleel na tareda ita abinda ke dagashi daga dakin salla ne kokuma idan zaije siyo magani a pharmacy hospital, shima idan zaije to Ihsan na wurin, Ihsan taita karanta mata novel tana murmushi kadan kadan, idan kaga yaci abinci to coffee ne yadan sha, baya iyacin wani abinci ko Ihsan ta girka saidai yay wasa da abincin kawai yatashi yabarshi, jiyake kaman ciwon yadawo jikinshi.

Zaune suke adakin itada Ihsan dake karanta mata wani novel tana kwance kan gado suka bude kofa suka shigo hakan yasa ta dago kai ta kallai shida Dr Om ne suna dan magana, murmushi Dr yay ya kalleta suna karasowa jikin gadon yace "how's my patient doing" dan murmushi tamai tana kokarin gyara kanta akan filo, ya makala mata wani abu kaman camera karama a hannu sanan yace "Gud, I need you to do something for me, inaso kitashi ki tsaya naga" karamin tablet din hanunshi ya daddana sanan ya kalli Khaleel yace "dago min kanta" ahankali Khaleel ya dago kanta ya zaunar da ita, kafarta Om yanunamai hakan yasa ya sauko da kafarta kasa yana kallon fuskar ta, kallonta Dr yayi yace "now try and stand on your feet" dan dafa bango tayi Khaleel ya tsaya kusa da ita dan karta fadi ya sakin mata murmushi tare da nunama ta thumb dinshi alamun good, ahankali take daddafa bango harta dan tsaya amma aduke tana dan ciccije lebe sabida zafin datake ji, dadi Dr Om yaji yace "gud now try and raise ur head, stand straight, inaso naga inda yarage dabai warke bane acikin" fuzar da iska tayi tareda karasa mikewa ahankali ahankali Khaleel yace "sorry wife" Dr Kuma na duba tab din hanunshi, kasa daurewa tayi jin zafin yay yawa tacire hanunta daga bango tai luuu zata fadi Khaleel yatare ta da sauri hakan yasa ta fado kanshi wani irin shocking yaji tunda ga yatsar shi har brain dinshi sabida yanda hanunshi yakama kirjinta mistakenly, itama wani iri yarr taji duka karfin ta tasa tadan juyar da jikinta ta yanda abin ya sauka daga hanunshi ta lumshe ido tana sauke numfashi, yafi 3minute ahaka sanan ya kwantar da ita ahankali yaja bargo ya lullubamata yana kallon idonta dasuke alumshe, maganar Om ce yadawo dashi daidai yace "Khaleel zokaga" zuwa yay ya kalli tab din yace "kaga wanan mucus dinne keda inflammation dazaran ya sabe shikenan zata iya tana mikewa tana komi saimuyi focusing kuma a dawo da maganarta" rungume shi Khaleel yayi cikeda murna yace "Alhamdulillah, Dr am grateful" fita Om yay daga dakin yanata dariya.
Cikin sati daya cikin ya warke fess, takan tashi tai tafiya ahankali ta shiga bayi da kanta tai alwala tai salla, kuma takanci abincin dan har tuwo ranan nan Ihsan tamata Kuma taci sosai danyamata dadi, Khaleel ko babu wanda ya kaishi murna harda yima nurses kyauta.

Zaune suke adakin yana bata tea abaki kiran Om daya gani yasa ya dauka ahankali yace "okay" sanan ya katse wayar Ihsan yamika mug din tea yace "zoki bata am coming Om nason ganina" fuskar Islam ya kalla dake kallonshi da idanunta masu kama danamai jin bacci yace "am coming wife" fita yay yawuce office din Om shiga yay ya zauna, Om ya bashi wayansu hotuna yace "kaga wanan hoton damukama wuyan tane, babu any damage a vocal dinta so Ina suspecting infection ne awuyan dake hanata magana, yanzu abinda zanyi shine zan bata magunguna sanan zan sallameku inyaso every every week zaka dinga kawota chech up tunda for now ai babu wata matsala saita maganan ko" kasa boye murnanshi Khaleel yayi hakan yasa Dr yafara rubutu akan paper asibiti yace "ko aje ai amarce hmm" yagama rubuce rubucen ya mikamai yace "your discharge letter, I will be expecting you guys next week Thursday" ahankali ya karba yana murmushi sanan ya mikamai hannu sukai musabaha tareda kara godemai sanan yafita daga dakin, dakinsu ya shiga Ihsan dake zaune agefen gado tana nunama Islam wani hoto yazo ya daga yana jujjuya ta yana murmushi dariya tayi tace "Ya Khaleel menene wai?" murmushi yamata yace "an sallamemu" yay maganar yana kallon fuskar Islam ahankali yaga taja bargo ta rufe fuskarta tana murmushi dan wlh tagaji da asibitin sosai itama. Ihsan ya kalla yace "tashi kitayata shiryawa bari naje nakira taxi" fita yay daga dakin yana Satan kallonta, shiryawa tayi cikin dogon black skirt din kanti na jean tasa shimi fari tadaura sweater akai pink dan garin da sanyi sanan Ihsan tamata rolling black gyale sanan tasamata flat slippers, tahade yan littatafai da kayansu dasu tea dake dakin ajakan trolley ta kulle ta daga, shigowa dakin yay yana kallonta tana zaune akan gado kanta akasa hanunta rike da teddy daya saimata kallon Ihsan yayi yace "fita da jakan taxi din na waje" jan jakan tayi tafita shikuma ya karasa cikin dakin har gaban gadon ahankali ya daura hannayen shi akan nata ya dagata tsaye ya karbi teddy ya ijiye akan gado kasa daga kai tayi ta kalleshi, jinta tayi kawai ajikinshi ya rungumeta tsamtsam tareda kissing gefen wuyanta.
[6/25, 2:22 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

55 & 56

Ya sakin mata light kiss gudun karya ji mata ciwo sanan ya dago kai ya kalleta murmushi kwance akan fuskarshi, jiyay duk wani ciwon kan da yakeji yabace, sake kai hannu yayi ya share hawayen daya gangaro mata tareda girgiza mata kai yace "am here for you now, koma inane I don't care saina kaiki koda bangon duniya ne inhar zaki sami lpy, zakiji sauki in sha Allah, stop crying..." dan kwankwasa kofa akayi Anty Hindu ta shigo takaraso inda suke ta kalli Khaleel sanan tace "Dr nason ganin ta, za'a wanke mata bakinne, kaga yanzu ma yadan warke tadan iya hadiye tea mai sanyi yau, amma tunjiya babu abinda take iyaci da bakin danyay jajir kaman kuna, bari nakaita" da sauri yatashi yakoma bayan keken yace "zankai ta Hajiya" dan hararan shi Anty Hindu tayi tace "banason gardama Muhammad, ba gamunan ba duka, salla yakamata kayi tukun yanzu sai asan abinyi, oya shiga bayi ka dauro alwala saika wuce massallaci, idan ka Ida aisai kazo kasamemu a dakin nata" tana fadin haka ta gungurata suka fita daga dakin, zama yay akan gado ya dafe kanshi tareda fuzar da iska shikadai yasan yanda yakeji, wayarshi ya dauko dake gefen gado yay dailing wani number yafi minti biyar yana magana aharshen turenci sanan ya katse wayar ya shafa kanshi yana fuzar da iska, ahankali yatashi ya shiga bayin dakin ya dauro alwala sanan yafito yafita daga dakin baiga su Abba awajen ba hakan yasa yawuce massallacin dake cikin asibitin.
Chapter 34 · 0% Book details