Sashe 14
Jarabta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Around 3 tadawo kaman jiya Fahad ne ya sauke ta abakin layinsu ta dandaro da kafa, a kusa da gidan su ta ganshi tsaye ya rike wani katoton balloon da aka hura an rubuta I love you ajiki murmushi kwance akan fuskar shi yana kallonta, dauke kai da sauri tayi ta cigaba da tafiya. Biyota yay da sauri yasha gabanta wani dan Kati mai kyau pink yaciro daga aljihun shi ya bude an rubuta "please tell me your name" . Fizge katin tayi tayar ta kalleshi masifa tai niyyar mai amma saitakasa ahankali tace "please leave me alone" da sauri ta wuce shi ta shiga gida tabarshi nan tsaye.
Wuraren Magrib Farida tashigo gidan dakinsu ta shigo ta zauna akan gado batare datacema Islam dake rubutu komi ba, kallo Islam tabita dashi sanan tace "Faree wah happen a school why are you like this?" hawaye ne yazubo sharr daga idonta, ajiye biron dake hannunta tayi tadawo kusa da Faridan ta dafata tace "meya faru me aka miki" fadawa tayi jikin Farida tafashe da kuka da kyar tai shiru duk hankalin Islam yatashi tace "baki da lpy ne?" girgiza mata kai tayi sanan tace "tun jiya bayan mun rabu nake kiran my superman yaki dauka, wlh har Gym dinan saida naje yau amma bayanan ban ganshi ba, nakasa komi ko lectures ma babu wanda nagane, I don't know why he is not picking my calls" tafashe dawani kukan, ba karamin tausayinta Islam tajiba hannu tasa ta share mata hawayen tace "stop crying hala baya kusa da wayan ne kokuma ansace mai wayan, please stop crying in sha Allah zai kiraki kokuma kuhadu" gyada mata kai Farida tayi, murmushi Islam tayi tace "oya cire kayanki bari naje nakawo miki abinci ta superman".
Washegari zazzabi ne yarufe Farida hakan yasa Anty Hindu tace ta zauna kartaje school yau Abba Kuma yakira Dr.
Bala ne ya dauketa a mota ana wangale gate ta ganshi yana jogging yauma, baki ta tabe ta dauke kai abinta suka wuce shi dudda haka saida ya daga mata hannu.
Da yamma ma data dawo haka ta ganshi zaune shida mai gadi suna hira murmushi yamata yace "welcome" dauke kai tayi da sauri dan duk inta kalleshi heart dinta bugawa yakeyi ta shige cikin gida da sauri.
Ba karamin murna yay ba da Ammi ta turo mishi su Ilham da Ihsan suzu suyi hutu, ga Fa'iza ma sun suma mid term break hakan yasa gidan yacika da hayaniyan su.
Zaune suka dukan su a katoton falon Goggo wanan Karan ma harda Umma duk sai hira ake shi kadai ne ke kwance ya lumshe ido kawai yana jinsu. Yusuf ne yace "why not mu dan hada get together gobe Saturday da yamma" ihu Ihsan tayi harda tsalle tace "Ya Yusuf wlh is gonna be fun to a ina zamuyi?" shiru yadanyi yana tunani sanan yace "anan falon Goggo but zamuyi decorating, and zaku iya inviting anyone, kawai games zamu buga sai Kuma drinks and have fun shikenan" ya dakama Khaleel duka yace "Ya kagani" batare daya bude ido ba yace "yea" finciko hanunshi yayi yace "bawai Yea ba ATM dinka zaka basu suje kasuwa su siyo abubuwan decorating dakin tsohuwar nan" hararan shi yayi yace "kai maiya sami ATM dinka" dariya Yusuf yayi yace "ai am d organizer ni zanyi handling inviting guest, kai a cash aspect din kawai anan muke bakatan ka, dan ban wayar kama" mikamai wayar yayi ya amsa yace "mezakai dashi?" tashi Yusuf yayi saida yakai bakin kofa sanan yace "I want to invite your Farida" yafita da gudu, da sauri Khaleel yatashi ya bishi yana kiran shi Yusuf Yusuf.
Part dinsu Yusuf ya shiga kafin Khaleel yazo ya kulle yana jinshi yana kiran shi amma yay bedroom ya rufe kofa, zama yay akan gado ya bude wayar dan dama babu key, duba contact dinshi yayi yaga babu wani suna Farida, wajen kira yaduba nan yaga wani number daketa kirashi baya dauka hakanan yaji ajikin shi wanan ne number yay dailing ringing daya ta dauka da sauri tace "Mk" dan dariya Yusuf yayi yace "ba MK bane Yusuf neto" ahankali tace "ina Mk inata kiranshi baya dauka" yace "eh baida lpy ne saisa yasani na kiranki ma, dama munada family get together ne yace he will be happy idan you come" wani murmushi tayi tace "dagaske?" "why not ai yanzu u are part of the family, anyways karna cikaki da surutu gobe ne 4pm sharp, zan miki forwarding address din" da sauri ya kashe wayar jin Khaleel kaman zai cire kofar da bugu ya tura mata address din gidan su sanan ya ijiye wayar yazo ya bude kofan ya ruga da gudu yana kiran Goggo.
*JARABTA*
Maman Abd Shakur
25 & 26
Gayu Farida taci sosai kaman zataje gasar Islam Kam tanata dariya dan tasan wajen superman dinta zata Bala ne ya kaita har kofar gidan tacemai 5:30 yadawo ya dauketa yace mata to sanan yatafi. Wayar Khaleel dake hannu Yusuf ne tai kara dan tun safe ya dauke wayar ya boye a wurin shi dan yasan Khaleel zai iya yaki daukar wayar idan tazo, tashi yayi yaje wajen Khaleel yace "Bros tana waje fa jeka shigo da ita" wani kallo yamai danji yake kaman ya bindige shi, ganin baida niyyar magana yace "tariga tazo wulakanci ba kyau please ka shigo da ita naji na yarda koma me zakamin inta tafi Kamin please" wani kallo yamai sanan yajuya yafita daga dakin Goggo ahankali, juyowa Yusuf yayi suka kashe da kanin nasu dukan su suna rawan murna Fa'iza tace "wlh nakosa naganta" kara gyaggyara decorations din flowers din dakin sukayi sanan suka zazzauna akan baban lallausan carpet din dasuka shimfida akan tiles.
Gate ya bude yafito tunda yake takowa take kallonshi tafiyar shi kadai gusar mata da tunani yake kayan turawa ne ajikin shi white shirt ne yadan bude boturin saman sai dogon jeans blue daya saka, wani irin murmushi takemai tace "barka da yamma Mk" dan murmushi yamata yace "shall we" yana gaba tana biye dashi abaya cike da kunya har part din Goggo, wani ihu da tafi su Yusuf dasu Ilham suka dingayi hakan yasa Farida ta labe abayan Khaleel tana kukkule fuska dan ba karamin kunya tajiba, wani irin kallo yakema Yusuf dako ajikin shi saima wani dadi dayake ji, Ihsan ne taje bayan Khaleel din ta kalli Farida dake rurrufe fuska cike da kunya, tabata hannu tace "am Ihsan his sister nice to meet you" hanunta Ihsan ta rike ganin taki bude fuska, tajata takaita wajen su sunata ihu sunajin dadi, da gudu Fa'iza ta kunna music suka hau tika rawa, Yusuf yazo gaban Khaleel dake kallonshi yana wani irin kwaso mai shoki harda gwalo, Farida kuma dasu Faiza sun sata a tsakiyar su sunata rawa abinsu. Gabaki dayan su dadi sukeji Khaleel yay budurwa, sosai sukasha rawa abinsu shi waje ma yasamu ya zauna yana kallon su, Farida sai satar kallonshi take, sunyi kusan 15 minutes suna rawa sanna Yusuf ya rage karan music din Ilham ta tashi ta kwaso drinks da chicken kebab din dasuka hada. Juice kawai Farida ta iya sha sabida yanda suke nan nan da ita duk tadinga jin kunya bayan sun gama ne Yusuf yace "okay once again atafa ma our special guest Farida... Daaaa" yawani kara gunna, suka wani kwashe da tafi, sanan yace "oya time for our game" yan matan suka mimmike suna yeee. Akan carpet suka zazzauna sukai circle Yusuf yakamo hanun Khaleel batare daya kalli fuskar shi ba ya zaunar dashi, sanan ya dauko wani bowl dake dauke da papers da akai folding ya daura ma kowa one one paper ajiki harda Farida sanan ya ijiye bowl din ya zauna kusa da Khaleel yay folding leg kaman yanda kowa yayi yace "papers din nan each of them contain a question da dole saika amsa mana ka fadi gaskiya so starting from me bari na duba Naga wats my question" budewa yayi sanan ya karanta "who is your best friend?" murmushi yay yanuna Khaleel yace "dis dude shine best friend dina"
Fa'iza ta bude nata tace "what do you hate most" dan dariya tayi tace "wanke wanke wlh" daka mata duka Yusuf yayi yace "lazy girl" Ilham ne tabude nata tace "izifi nawa kika haddace?" gwalo Ihsan tamata dauke kai tayi tace "ashirin, suratul Ankabut zuwa Nas" Ihsan ta karanto nata "meke saki kuka?" shiru tadanyi tace "ciwo, idan ina ciwo" sai Farida ahankali ta bude nata ta karanto "who do you love?" shiru tayi Yusuf yace "answer now is ur turn" ahankali ta kalli fuskar Khaleel da sauri ya kawad da kai murya chan kasa tace "him" wani murmushi dukan su sukayi Ihsan ne tace "him, waye him?" juyo dakai tai ta kalli Ihsan a kunyace tai murmushi taki magana, Yusuf ne yace "barta tamayi kokari ai, ya kalli Khaleel ya daga mai gira yace" Mk is ur turn" ajiyar zuciya Khaleel ya sauke ya bude takardar shiru yay ganin tambayar, Fa'iza tace "karanto muji question dinka Yaya" ahankali yace "wakake so?" shiru yadanyi kafin ahankali yace "My Eesha" sosai maganar ta daki Farida, hawaye ke kokarin zubo mata da kyar tai controlling dinsu tadanyi murmushin yake daidai kiran Bala na shigo wayanta dan biyar da rabi ya wuce har da kusan minti goma, tashi tsaye tayi ahankali tace "natafi anzo daukana" "dawuri haka ai bamu gamaba" cewar Ilham murmushi tamusu tace "zan dawo wataran" hanunta Ihsan ta kama tace "muje ki gaisa da Umman mu da Goggo mu fita daga dakin tayi tana dan waigen fuskar Khaleel, sosai Umma taji dadi barin ma Goggo sai addu'a take mata saida suka fito Ihsan tace "sis Eeshan dayake magana fa ta rasu, saisa dakika shigo rayuwar shi yanzu muke murna sosai in sha Allah dake za'ayi" batasan Sanda ta sauke ajiyar zuciya ba, ta share kwallan daya zubo mata murmushi Ihsan tamata sanan tarike mata hannu tarakota har waje, Khaleel ta gani da Yusuf jikin motar Bala suna jira su fito, dan murmushi Khaleel yamata yace "thanks for coming" murmushi tamai back yadaga mata hannu ta shiga mota suka wuce.