← Book details Jarabta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 49

Sashe 17

Jarabta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da magrib yatashi yana karema dakin kallo Yusuf daya gani akan kujeran dakin yana kallonshi, yace "wat happen?" dan murmushi Yusuf yamai yace "kasha uban teargas ne ka sume ma mutane" tashi yay ya zauna yana dan yatsine fuska sabida yanda ciwon kafarshi kemai zafi, Yusuf ya nunamai wata white t-shirt daya fita ya siyomai yace "ga riga kasa ka dauro alwala see dadduma kazo kai sallan asri da magrib mutafi gida dan an riga an sallamemu" rigar ya saka sanan ya shiga bayin dakin ya dauro alwala yazo yay salla. Bayan ya idar yana kan dadduma wayar Islam dake kan gadon tai kara hannu ya mika ya dauko "My Heart beat" wani irin bugawa kirjinshi yayi dayaga sunan, duk yanda yaso ya hakura yakasa saida yay picking call yasa a kunne daga dayan bangaren Fahad yace "princess inata miki text baki replying, I miss you yau ba muyi wayaba" wani abune yaji ya tokare mai zuciya, "Hello my princess are u there luv?" "mallam karka kara kiran layin nan, an riga an mata miji am her husband to be, so be very careful" yafada cikin fushi ya katse wayar, tashi yay ya linke daddumar yabama Yusuf dake kallonshi baki bude yadau wayar shi batare daya kalli Yusuf ba yace "muje" fita sukayi sanan ya juyo ya Kalli Yusuf ahankali yace "am coming" zama Yusuf yay akan kujerun dake reception din shikuma yay hanyar dakin da Islam take, ahankali ya bude kofar, dayar gajeren sallama dan bama tajishi ba tana zaune kan gado da doguwar riga ajikinta na atampa kanta da bakar hula da aka dan matsar dashi baya sabida bandejin goshin, ta mikar da kafafunta taja doguwar rigar zuwa saman gwuiwowinta tana hura ciwon dataji dake mata zafi. Ahankali yake daga kafa haryakai bakin gadon ya tsaya yay folding hanunshi a kirji cikin sanyin murya yace "is it paining you?" gyada kai tayi tana yarfe hannu tana hurawa batare data dago kaiba dan gabaki dayan hankalin ta nakan ciwon, dago kai tayi da sauri ta kalleshi da katon bandejin dake goshinta da sauri ta saukar da rigarta ta rufe kafafun ta, dan murmushi yayi sanan ya zauna abakin gadon yana fuskan ta hararan shi tayi tace "waikai duk inda nake sekazo, tracker kake amfani dashi ne? Wlh ko kafita daga dakin nan kona kirama Abbana nahadaka dashi komame zai faru ya faru" murmushi yasake yi sanan yace "how are you feeling now?" dauke kai tayi ta turo baki, sosai yake kallonta sake juyo dakai tayi ta kalleshi tace "wai bazaka fitaba sai su Abbana sunzo, okay bari na kirasu" bude baki tayi zatai ihu yadaura hannu akan lips dinshi alamun tai shiru, kasa magana tayi kaman wacce yama magic saima dauke kai datayi daga kallon dayake mata jitake kaman ta makeshi, hanunshi yasa a aljihun wandon shi yaciro wayarta ya mika mata juyowa tayi tana ganin wayarta ta karba da sauri akuma dan rude tace "a ina kasamo wayata?" baice komiba yatashi tsaye yana kallonta yace "waye My heartbeat" da sauri ta kallai sanan ta harareshi tareda murguda mai baki tace "meruwan ka and kafita daga nan" kallon cikin idonta yayi yace "well I told him karya sake kiranki because am ur husband to be" kwalalo ido tai ta kalleshi da so much pain a idanunta tace "Fahad din nawa ka fadanma haka?" gyada mata kai yayi yace "yes" azuciye ta juya tana waige waige pillow dake bayanta ta raruma ta jefamai da duka karfin ta ya chafe yana murmushi har saida hakoranshi suka bayyana daidai lokacin Anty Hindu da Abba suka shigo, Abba yace "Ummi Khaleel din kike bugama pillo mutumin daya taimakeki dabadan shiba da Allah kadai yasan mezai sameki" da sauri ta kalli fuskarshi, dan murmushi yamata sanan ya tako yadan duka ya ijiye filon abayanta ahankali yace "I will come and check you tomorrow, I love you" yay maganar ta yanda ita kadai zata iyaji ya juyo ya Kalli Abba da Anty Hindu yace "Abba saida safen ku" addu'a sosai da godiya Abba da Anty Hindu sukamai sanan ya juya zai fita daga dakin dan waigowa yay ya kalleta daidai lokacin itama tadan dago kai suka hada ido hannu yadaga mata alamun bye, kawad dakai tai da sauri murmushi kwance kan fuskarta. [6/17, 6:38 PM] Maman Jedda: Novels *JARABTA* Maman Abd Shakur 32 & 33 Kaman mai rada yace "I love you so much, zuciya ta bazata iya jure rashin kiba, nasan baki sanni ba but please give me a chance, ina sonki sosai" dan hawaye taji ya gangaro mata, girgiza mata kai yayi ahankali yace "will u marry me please" dan lumshe ido tayi tareda dagamai kai maganar Anty Hindu dataji tawaje ya mai do da ita hankalin ta da sauri ta tashi ta zauna ta kawad dakai kirjinta na bugawa sosai tashi tsaye yayi shima yana kallon fuskarta, bude kofa Anty Hindu tayi ta shigo ita da Dr, dubata Dr yayi sanan yace "Hajiya babu wata matsala, nan da yan kwana biyu yan ciwukan nan zasu warke zaku iya tafiya" Anty Hindu tace "to nagode Dr, bari nakira Bala yazo ya dauke mu" da sauri Khaleel yace "basaikin kirashi ba nina kaiku Hajiya" yay maganar yana kallon fuskar Islam da har yanzu taki kallonshi, "to shikenan, ke tashi mutafi" ahankali ta mike tsaye tadau Hijabin ta tasaka shiya fara fita sai ita da Anty Hindu dasuka fito suna biye dashi abaya kofar baya ya bude musu suka shiga sanan yarufe sanan yakoma gaba yabude motar ya shiga ya kunna yafara driving har suka fita daga hospital din, ta mirror gaban mota yaketa kallonta amma taki dago kai saima wasa da yatsun ta da taketayi, har cikin compound ya shiga dasu suka fiffito da sauri tai cikin gida dan bataso su sake hada ido, Anty Hindu ce tamai godiya cike da fara'a da addu'a sanan ya kunna mota yafita daga gidan. Afalo taga Farida ta zauna taci uban tagumi tsakanin jiya da yau duk tai zuru zuru tana ganin ta ta taso da gudu ta rungumeta tsam tsam sakinta tayi ta kalli fuskarta tace "sannu Islam ya jikin?" dariya ma tabama Islam hakan yasa tai dan dariya tace "ke dalla am fine ciwo fa kawai naji, Ina Mum?" jiki a sake tace "tana daki" tace "bari naje na gaishe ta" sama tayi saida ta gaida Mum tamata ya jiki sanan ta wuce dakinsu bayi ta shiga tai wanka da ruwa mai dumi sanan ta fito, light kaya tasa tazo ta kwanta akan gado dan bacci takeso tayi ta lumshe ido, fuskar Khaleel tagani yana mata murmushi da sauri ta bude ido tajuya dayan gefen tasake lumshe ido tuna sanda ta daura fuskar ta akan hanunshi tayi, bude ido tayi da sauri ta tashi ta zauna tareda jan uban tsaki dan mugun haushin kanta takeji tayaya ma tai hakan wat was wrong with her, waya ta dauka tasake dailing number Fahad bai dauka ba, message ne ya shigo wayar ta bude bakuwar number ce hakan yasa ta bude "I love you so much. Khaleel" wirgi tai da Wayan akan gado tareda yin tsaki "mutum sai shegen naci anaci" Misalin 9 na dare Yusuf ya shigo part dinsu ya sameshi yana zaune yana daddana waya gefenshi kuma tea ne daketa kamshin su citta, zama Yusuf yay kusa dashi yadau tea ya kurbe hakan yasa ya kalleshi batare dayace komiba, murmushi Yusuf yayi yay gyatsa sanan yace "idan ma masifa zakamin naji amma kafara zuwa Abba na kiranka" filon dake kan kujeran yadau ka ya naka mishi akai sanan yabar dakin. Sallama yayi ya shiga dakin Abban, shi kadai ne sanye da farar jallabiya idanunshi acikin medicated glass yana karanta littafin addu'oi samin waje yay ya zauna akasa. Saida Abba yagama sanan yarufe ya ijiye gefe ya kalleshi yace "Son" "Na'am Abba" Abba ya gyara murya yace "ahh dama magana nakeso nai dakai kan yar abokina, nafison naji daga gareka ne dan mahaifinta yacemin yayarshi tace kun dan dade da sanin juna dan har gidan su kajema" shiru yadanyi yana nazarin fuskar Khaleel din sanan yace "kana sonta ne?" sosai yaji kunyar maganan Abba hakan yasa yadanyi murmushi yana sosa keya, dan dariya Abba yayi yace "a'a to to to, wanan murmushi haka Khaleel ta eh ce ko" dan gyada kai yayi kanshi akasa Abba yace "to masha Allah dama nariga nai magana da mahaifinka ran sati zaizo sai muje nema maka auran ta, banason awani nisanta bikin sabida dazaran anyi auren kukadan yimana kwana biyu anan saika koma bakin aikin ka ko" gyada ma Abba kai yayi Abba yay murmushi yace "saura dan uwanka yanzun nan nagama dashi nabashi wata daya idan Bai fito da mataba nizan nema mai" dariya Khaleel yayi wanan karan, Abba yace "tashi katafi Allah muku albarka". Sheshekan kuka datake ji yasa ta farka cikin tsakiyar daren nan, ahankali ta mika hannu ta kunna wutar dakin hakan yasa baccin idonta ya washe sosai, wawwaigawa tayi bataga kowa akasa ba hakan yasa ta sakko daga gadon, Farida tagani ke kuka a kwance da sauri tahau matattakalan bonk din tahau kan gadon ta dago ta, ta zaunar da ita takai hannu arude ta taba wuyan ta tace "baki da lafiya ne?" girgiza kai Farida tayi tana goggoge hawayen dake zubowa kaman an bude famfo, komawa tayi zata kwanta Islam tariko hanunta tace "talk to me please, problem shared is problem solved" fadawa tayi jikin Islam tafashe dawani irin kuka harda shesheka hakan yakara ruda Islam ta kankameta tace "Faree konaje na taso Mum ne?" girgiza kai Farida tayi ahankali tace "wlh Islam ina mugun sonshi, son da bazan iya kwatanta miki ba, amma kwata kwata bama ya daukan wayana yanzu, baya kulani na rasa yanda zanyi da kaina" kama fuskarta Islam tayi tace "listen listen kidena kuka kinata wahala shi baimasan kinayi ba, ki manta dashi jor, kanme zakizo kina wahala, ki manta dashi" girgiza kai tayi tace "bazan iyaba, I tried but nakasa I love my superman so much Islam bazaki gane bane" shiru Islam tayi cike da tausayin ta ahankali tace "to kinfada mai kina sonshi?" girgiza kai tai alamun a'a, tace "to duk randa kika sake ganinshi kinfada mai am sure zaisoki back" murmushi tadanyi ahankali tace "thank you Islam" kwantar
Chapter 17 · 0% Book details