← Book details Jarabta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 49

Sashe 20

Jarabta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maman Abd Shakur

40 & 41

Wani mugun kallo ya watsama Faridan batare daya damu da maganan mutanen wajen ba ya juya zai tafi, kafarshi Islam ta rike gam gam tareda daura fuskarta akan gwuiwar shi tafashe da mugun kuku harda shesheka tace "bakace kana sona ba, inhar kanasona son gaskiya, so sabida Allah to ka yarda ka auri Farida, dan girman Allah do it for me" fincike kafarshi yayi yakara juyawa zai tafi da sauri tabishi da gwuiwa ta kama kafarshi again gam sanan ta dago kai ta kallai suka hada ido, ahankali ta saki kafarshi tahada hannayenta tace "inhar kanasona da gaske, ka aure ta karta kashe kanta, yar uwata ce bazan taba yafema kaina ba idan wani abu yasa metaba, dan darajan Allah am begging you" yanda take kuka tana rokanshi yasa ya tsugunna ya dagota sama kallon cikin idonta yay yace "stop crying" ahankali ta tsayar da kukan tana kallon fuskarshi yace "abinda kikeso kenan na auri Farida?" Ya tambayeta "jama'a zataci shinkafar fa" da sauri Islam ta juya ganin Farida na kokarin kai shinkafar bakinta ta daga hannu tace "stop, stop Faree ya yarda, zai aureki" kallon ta Farida tayi sanan ta kalli Khaleel din tana goge hawaye, Islam ta kallai tace "please tell her ka yarda" yadade yana kallon fuskar Islam din kafin ahankali ya juyo ya kalli Faridan da kyar ya iya cewa "yea na yarda I will marry u" murmushi Islam tayi tana goge hawayen dataji ya zubo mata, Farida takara goge hawayen dasuka ki dena zuba tace "and kayarda dazaran na sakko zamuje gida direct ku fadama Abba kun yarda" yadade yana kallon fuskar ta sanan yace "yea, now come down" yasa hannu ya danne mata ladder, murmushi Farida tayi ta kabar da shinkafar rice din dake hanunnata tafara sakkowa saida ta sakko kasa ta fada jikinshi ta rungumeshi tana kuka sosai tace "I love you so much Mk, wlh Ina mugun sonka, Allah ya jarabceni da sonka, I love you my superman" ihu mutanen wajen sukeyi suna tafi da sauri Islam ta sanya hijabin ta tarufe fuskarta jin kuka yazo mata sosai, da sauri ta juya zatabar wajen karaf taji anrike hanunta hakan yasa ta dago da rinannun idanunta taga Khaleel ne wanda Farida ta shige jikinshi tana kuka yana kallon kwayar idonta, fizge hanunta tayi da gudu tabar wajen tai bakin titi Keke napep ta tare ta shiga ciki tacemai suje sosai take kuka mai Keke na tambayan ta lpy.

Cireta daga jikinshi yayi batare daya kalli fuskarta ba yace "mutafi" yana gaba tana biye dashi suka karasa har wajen motar ya shiga itama ta bude gaba ta shiga sai murmushi take tana kallon fuskarshi kaman yau tafara ganinshi, kunna motar yayi sukabar wajen, a kofar gida suka ganta zaune akan bencin mai gadi, parking yayi suka fito ta kalli Farida tace "dama kunake jira mutafi wurin Abban" da sauri ta bude gate ta shiga batare data kalleshi shiba Farida ta kallai tace "muje my superman" Atare suka shiga cikin gidan direct falon Abba sukayi suka shiga da sallama, yana zaune tareda Mum dake tayashi arranging some business papers. Daga Abba har Mum din binsu sukai da kallo ganin yanayin idanun yaran nasu.

Gaban Abba Islam taje ta tsugunna ahankali tace "Abba dan Allah kahada Farida da Khaleel aure bada niba please Abba, don't ask me why amma dan Allah kahada su aure ni banaso" tunda take maganan Khaleel yay folding hanunshi akirji yana kallonta idanunshi sunyi jaa, with so much confusion Abba ya kalleta sanan ya kalli Farida da Khaleel dake tsaye sanan yadawo da kallonshi ga Islam yace "wai meke faruwa ne Ummi, wanan wace irin magana ne kikazomin dashi haka, meke faruwa?" gyara zama Mum tayi tace "Alaji zan fadama" dan shiru tayi tana kallon fuskar Islam sanan ta kalli Alhajin tace "ni dama ban fadamaka bane sabida banason kaga kaman na tsangwami Islam ne, ka tuna fadan da ita da Farida sukayi kwanakin baya, to ashewai Islam ce bayan Farida tagama bata labarin soyayyar ta da Khaleel shine Islam taje ta kwacema Farida dake son Khaleel sosai Khaleel" shiru Abba yayi yana nazarin maganar Mum sanan ya kalli Islam yace "haka abin yake Ummi?" ahankali ta gyada kai ganin yanda Abba ke kallonta yasa tace "am sorry Abba" batare daya kalleta ba yakira Farida, ahankali Farida tazo gabanshi ta tsugunna Abba yace "haka zancen yake?" gyada kai tayi sanan tace "Abba inason Khaleel sosai shine ta kwacemin shi" tafashe da kuka tareda daura kanta akan cinyar Abba, shiru Abba yayi sanan ya kalli Islam ahankali yace "kinason Khaleel ko baki sonshi, tell me the truth?" ahankali ta juya ta kalli Khaleel da ita yake kallo sanan ta kalli Mum data jeho mata wani uban hararan, kallon Abba tayi sanan ta girgiza kai tana kokarin hadiye kukan dake zuwan mata tace "a'a bana sonshi" da sauri Abba yace "dama kinyi hakane dan ki bakan tama yar uwarki rai ko?" da sauri ta girgiza kai, dago kai Abba yayi ya nunama Khaleel kujera, kasa zama yay akujeran ya zauna akasa, ahankali Abba yace "Wakake so cikin su wazaka aura? Banason tauyema kowa hakkin sa, yaran zamanin nan kuncika matsala wlh, ka fadamin gaskiya Khaleel wakake so acikin su wazaka aura?" kallon Islam yayi hadamai hannu tayi sanan ta girgixamai kai tana hawaye da sauri ya dauke kai, ya kalli Farida dake kallonshi kirjinta na bugawa idanunta sun cicciko da hawaye ahankali yace" "Farida" murmushi Abba yayi yace "shikenan Allah Sanya albarka, Allah muku albarka dukan ku saikaje ka sanar da iyayenka" Ahankali yatashi yafita daga dakin, sauka yayi yafita daga gidan ya shiga mota ya daki sit din motar yafi sau dari, wani bakin ciki mara misultuwa yaji yanaji da kyar ya iya tuka kanshi yakai gida.

Abba ya kalli Islam yace "mesa kika aikata irin abin nan Islam?" Mum tace "Alaji bawanan ma kadai ba da Farida tamata magana shine fa takifa mata mari ranan harda fasamata baki, haba haka ake abu a duniya, daga yar uwarki tabaki labarin saurayin ta saikibi takasa kije ki kwace mata shi, kasan shi namiji wawane hala saisa lokacin ya biyemata ya yarda har aka turo, yanzu dai alhaji tunda komi yay daidai basaika hukuntata ba nariga na yafemata, faridama ta yafe mata shikenan magana ta wuce a cigaba da shagulgulan biki zamu aurar da ya" Ahankali Abba ya sauke ajiyan zuciya yace "hakane kutashi kutafi" fita sukayi daga dakin Farida ta bangajeta ta shige dakin Mum binta tai da kallo kafin ta wuce dakinsu a daddafe ta fada gado taci kukanta tai bacci.

Manya manyan hajiyoyi masu gyaran jiki Mum ta daukoma Farida nan fa aka fara gyara amarya ciki da waje idan kunga Farida en tai mugun kyau bakin fatarta har kara walkiya take, ko tak baya hadata da Islam idan Islam zata wuni tana mata magana bazata kulata ba hakan yasa kullum Islam na daki, Maman Miemie nema idan tazo aiki takan dan kawomata Miemie ta dauketa suyita wasa, Khaleel bai kara zuwaba, Farida bata damuba tunda wani zubin yanadan picking call dinta suyi magana daya biyu ya katse.

Yau saura sati daya biki yaune aka kawo akwatin Farida saitin goma sha biyar, su Umma da Mujiba datai kini kini da rai dawasu kawayen sune suka kawo inda Mum da kawayenta lecturers suka tarbesu akaci akasha, akasha guda, dazasu tafi aka basu tukuici. Da daddaren ranan Anty Hindu tadawo daga dubai da kayayyakin daki data siyo anata murna Koda Islam tazo gaishe ta kallonta tayi daga sama har kasa tace "ke ciwo kikayine haka wanan rama" murmushi tayi tace "eh amma naji sauki" tsaraba Anty Hindu tabata sanan ta wuce dakinsu ta kwanta.

Washegari da safe Abba yafita da wurin kasancewar yanada aiki, Mum ce ta turo akwatinan Farida ta shigo dasu dakin Anty Hindu one by one tace "ga akwatin Farida nan Anty?" kallonta Anty Hindu tayi cike da mamaki tace " Farida Kuma wace Faridan?" kama haba Mum tayi tace "au Abban su bai fadamiki ba, ai Anty Kwai ne yafashe gaskiya ta futa, ashe fadan nan da yaran nan sukayi kan Khaleel ne, wai Islam kwacema Farida Khaleel fa tayi, shine da kanshi Khaleel din yay tattaki yazo yafadi ma Abba shifa Farida yakeso ba Islam ba" tunda take maganar Anty Hindu ke kallonta tace "Khaleel din yace hakan" "eh" murmushi Mum tayi tace "ga akwatin ki duba kisa mana albarka" tabe baki Anty Hindu tayi tace "nayafe fitanmun dasu daga daki" tabe baki mum tayi tafita dasu tana kunkuni tace "yar bakin ciki kawai" sosai Anty Hindu taji ranta ya baci da zancen, wanan wani irin abune.

Family Khaleel kodaya fadan musu abinda ke kasa basu wani damuba kasancewa sunsan Faridan dama.
Yau thursday da kyar Yusuf ya tirsasa Khaleel yatashi suje gidan su kaima Farida kudin fati, da wasu yan abubuwa, da kyar yatashi ya shirya dan wlh bayason yamaje gidan balle yamaga Islam shiryawa yay cikin shadda Light brown shadda daya mugun amsan shi ba karamin kyau kayan sukamai ba sai uban kamshi yake, fara tsayawa sukayi sukai isha'i sanan suka tafi.
Farida taci uban lalle dan gobene walima tasanya wata atampa da tasha uban stones, kallon Sameer dake kusa da ita tayi ganin kiran Khaleel ya shigo wayarta tace "jeka cemusu su shigo falo Ina zuwa" fita yay da gudu, ta zauna agaban mirro tana shafa hoda.
Chapter 20 · 0% Book details