← Book details Jarabta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 49

Sashe 15

Jarabta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yau Monday bata da lectures amma sabida Farida data kirata tamanta da presentation dinta dake cikin file akan table Kuma yau zasuyi yasa ta tashi ta shirya tana tsaki.
Sauka falo tayi tadau presentation din akan table tafito Bala ne ya dauketa suka fito daidai yay parking motar shi a kusa da gidan su batama lura dashi ba suka wuce, ajiyar zuciya ya sauke sanan ya kunna motar ya bisu har AUN. Parking Bala yayi a parking lot tafito hanunta rike da file dakuma waya data kara a kunne, kasa dauke kanshi yay daga kanta bata lura dashiba sabida glass din motar shi tinted ce. Maida wayar tai cikin jaka tadan jingina da wata mota tasa kumbanta abaki tanaci dan taga yadanyi tsayi, Farida data hango tadan taho da gudu gudu, yasa ta karasa wajenta file din tabata ta karba ta bude tagani murmushi tayi sanan ta mikama Islam hannu suka tafa tace "bari nai sauri an fara amma ba'akai group dinmu ba" tana fadin haka tama Islam bye ta wuce ta tafi dadan sauri dawowa motar Islam tayi ta shiga Bala ya kunna sukabar wajen. ba karamin mamaki yayiba dayaganta da Farida, wayar shi yaciro da sauri neman number ta yafara dan baitaba kiranta ba, da kyar yagane number yay dailing, Farida data kusan class dinsu tanajin ringing ta duba wayarta ganin superman ne wani farin ciki ya rufeta da sauri tai picking, "Hello Mk" ahankali yace "how you" murmushi tayi tareda yin wani fari ta cigaba da tafiya tace "fine, yasu Ihsan" shiru yadanyi kafin yace "inaso nadan tambaye ki wani abu" baki tawani washe tace "ok" yace "ina parking lot din school dinku.." "school dinmu?" ta katse shi yace "yeah, naganki da wata, I think kaman tabaki wani folder ne, who is she?" "Farida Maikano" taji ana kiranta is time for her presentation kenan da sauri tace "Mk I will call you later, zanyi presentation ne bye".

*JARABTA*

Maman Abd Shakur

27...

Sai yamma ranan tabar school tana komawa gida taci abinci bacci yay awon gaba da ita, Islam bata tasheta sabida tasan bata salla.
Atare yau suka fito Bala ya dauke su waige waige tadinga yi awaje ganin yauma bata ganshi ba tabe baki tayi tace "hala yagaji ya hakura ne" ahaka suka kai makaranta kowacce tai department dinta.
Misalin 11 Mum na zaune adakin ta wayar wata baban kawarta senior lecturer ce itama ta kirata dauka mum tayi tace "Hajiya hope baki shiga school bayau?" "ahh'ah ban shiga ba yau banda lectures" matar tace "kin ganni nan ma fitowa ta kenan driving ma nake wlh wani good student of mine yazo yake cemin nabar school din now, wai student zasuyi protesting sabida party dasukaci SUG wai cuwa cuwa sukayi, an kinsan yaran nan Allah kadai yasan mesuka shirya" arude mum ta mike tsaye tace "Hajiya sadiya yata na makaranta" katse wayar tayi tadau car key dinta dake kan carbod tadau hijabi tafita arude, taja mota dawani irin gudu tafita, number Farida tai dailing cikin sa'a ya shiga tana dauka tace "kina ina?" murmushi tai tace "gani nan mum nama fito daga massallaci ne zan koma class" da sauri mum tace "Kifito yanzun nan kizo baki gate, right now" yanda Mum tai magana yasa tace "Mum lpy?" tsawa Mum ta dakamata "nace kifito bakin gate yanzun nan am coming right now" juyawa Farida tai da sauri tadinga tafiya harta kai bakin gate tafita, tsayawa tayi abakin titi daidai lokacin Mum ta iso, wining glass down mum tayi tace "get in" bude kofa Farida tayi ta shiga tana kallon fuskar Mum, kunna motar mum tayi sukabar wajen ta kalli Mum tace "Mum lpy mesa kika kirani lectures gareni fa" batare data kalleta ba Mum tace "riot students zasuyi i just got d information yanzun nan saisa nazo daukar ki dakaina" da sauri Farida tace "Mum Islam fa? Turn d car muje mu daukota tana lecture theater department dinsu sunajiran lecturer" tabe baki Mum tayi ta cigaba da tuki abinta, "Mumm" Farida ta kirata dawani irin murya, ahankali tace "she always considered her mum" mum ta harareta tace "and nikuma yata mace dayane which is u, Kuma kimin shiru anan wlh kona wanke miki fuska da mari" wani hawaye mai zafine ya zuboma Farida tace "Mum I tot kinason Islam, inhar bazaki koma mu daukota ba to ki saukeni nakoma koma menene yasamemu tare" wani mugun kallo mum tamata tace "waya cemiki bana sonta?? Kawai dai danka danka ne" sosai Farida taji kuka yazo mata da kyar ta hana kanta yi wayarta ta ciro daga jaka Mum tace "wlh inkika kirata saina bata miki rai, ita yarinya ce once anfara riot din she will find her way out so karki sake ki kirata, I know wat am doing" sosai taji tanajin haushin uwartata ahankali tace "ni dama ba kirama zanyi ba, watsapp zan shiga" wani irin kukan zuci ta dingayi tayaya yanzu zata taimaki Islam? Mk ne yafado mata rai, text yes text zatamai, da sauri ta shiga massage tafara typing
"Mk zaka iya tuna fuskar wacce kace kaganmu jiya tare? If yes please help me get her out of the school now, riot students zasuyi, please nasan wat am asking is a bit much but you are my superman, taimakon mutane is ur periorty, tana theater din Home economics department, thank you" ta turamai.

Yana kwance akan gado yana danna wayar sakon ya shigo mistakenly hanunshi ya danna sakon ya bude dan baiyi niyyar budewa ba. "subhanallah" yafada bayan yagama karanta text din da sauri yadau car key yafita daga dakin.

Zaune take achan sama, last roll din sit din lecture theater, bata sami gaba ba sabida taje massallaci tai salla bata shigo ajin dawuri ba, sai hayaniya ake chaaa ana jiran malamin, Class chairman dinsu daya fita siyo kati dan yakira lecturer awaya ne yaleko ta window yana numfarfashi sama sama yay ihu yace "everybody run yaki sukeyi, wlh teargas zasu wurgo yanzun nan" dudda yan ajin basu gane kan zancen shi ba amma numfarfarshin da akaga yanayi yasa aka tattashi tsaye ana gudu, tashi tsaye Islam tayi tana Kalle kalle, ta window sukaga wasu students dasuka fenfenta fuskokin su dan kar aganesu sun wurgo teargas ta window yafado ajin, fuuufuufuu yafara wani irin popping yana fitowa yana hayaki, ihu yan ajin suka fara, ture ture ake kawai kowa na neman takanshi ga waje yan protests din na dambe da securities, hijabin ta tasa ta taushe hancin ta dan batama gani da kyau sosai tana sakkowa daga matattakalan tsakiyar ajin, tari tafara yi sosai idanunta na juyawa, bangajeta akayi hakan yasa tai gefe zata fadi wasu students dasuma sun haukace suna neman hanyar fita sabida tarin dasuke suka kara bigeta luu taji hannunta yay kasa tai dayan bangaren, hakan ya bayyanar da hancin ta ta shaka, ga idanunta dake wani azaban yaji ga hayaniya ga tarirrika Kala Kala, ga ihun mata daban daban, tsugunnawa tayi anan tsakiyar stairs tafashe da kuka zuciyar ta kaman zai fito sabida tsoro da fargaba, gawani irin tari datake yi tace "wayyo Allah Mamana" wayansu student da basa ganine sukazo wucewa tuntube sukayi da ita hakan yasa dukansu kusan su bakwai suka fada kanta duka kowa na tari.

Ba lallai nai typing gobeba sabida yau nakuma da mugun yawa lol😜
[6/16, 8:30 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

28 & 29
Chapter 15 · 0% Book details