← Book details Jarabta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 49

Sashe 13

Jarabta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Atare da Farida yau duk suka tafi school dan itama tanada lectures yau.
Wuraren 3 tagama lectures dinta Farida ta kira tace mata ta wuce ita bata gamaba hakan yasa tafara tafiya har tafito bakin gate, Keke napep takeson ta tare tahau. "Assalamu Alaikum my Princess" daukar mai muryan yasa ta juyo murmushi kwance akan fuskarta, wani dogon guy ne mai farar fata, yanada jiki ga saje daya yawaita a fuskar shi, ya sanya wani lallausan yadi brown sai kamshi yake, baki ta bude zatai magana ya girgiza mata kai yana hararan ta dawasa yace "karma kifaramin wanan dadin bakin naki, shall we" Ya nuna mata motar shi, murmushi kawai tayi ya bude mata gaba ta zauna sanan ya zaga ta dayan bangaren ya shiga ya zauna hakan yasa yace "Ya jikin Abba?" wani irin kallo yamata sanan yace "Alhamdulillah yaji sauki" shiru sukadan yi tana wasa da yatsa shikuma yana kallon dogayen yatsun ga fararen dogayen kumbunanta dake mugun birgeshi, jingina yay da kujera anatse ya kira sunan ta "Islam" dago kai tayi ta kallai ganin ita yake kallo yasa ta mayar da nata idanun kasa ajiyar zuciya ya sauke yace "mesa kika zabi azabtar da zuciyata sabida kinsan kece ke mulkata? Islam!" Yasake Kiran sunan ta dawani irin yanayi yace "nagaji inaso nai aure, niba yaro bane, banyi kokari ba tun kina secondary school fa muna tare, please my princess ki yarda naje nasami su Dad ayi finalizing everything kinji" ahankali tace "school dina fa" gyara zama yay ya fuskanceta yace "kina tunanin bazaki cigaba da school bane bayan kinsan yanda nakeson karatu eh princess" girgiza mai kai tayi yace "muna komawa chan zan nema miki University mai kyau kifara yi kinji My Islam" murmushi tamai sanan tace "tom amma please kabari nafara ma Mum maganar kaji" murmushi yamata yace "to naji rabin raina" yawani daga mata Gira, ahankali tace "Ya jikin Abba yaji sauki sosai?" "Alhamdulillah an sallamemu inama ajiye su agida nataho na ganki, I missed my princess so much" rufe fuskarta tayi da hannu sabida yanda yabata kunya, kunna motar yayi yana murmushi yafara tafiya fira sukeyi jefi jefi gwanin ban sha'awa yana shiga kwanar layinsu yay parking dan dama anan yasaba fakin bata bari yakai ta har kofar gidan su, tafito, daga mai hannu tayi shima haka yana wani murmushi jiyayi inama gidan su zasu haka saida yaga ta bude gate ta shiga sanan yatada motar yabar anguwan su.

Maman Miemie da Anty Hindu tasamu a falo gaidasu tayi tawuce sama danyi wanka gashi ana Kiran sallan la'asar hakan yasa ta shiga bayi, muryan Farida dataji itama ta dawo yasa tai sauri tagama wankan ta dauro alwala tafito da saurin ta dan tabama Farida labarin yanda sukai da Fahad akan gadonta taga Farida ta kwanta tana bacci ko kaya bata cireba, murmushi kawai tayi ta girgiza kai tace "lazy gurl" gaban wardrobe taje dan pink rigar ta data kaimata har gwuiwa tasaka sanan tadau zani ta daura tasaka hijab tahau kan dadduma tai sallan la'asar. Koda ta idar sauka kasa tayi dan debo abinci, jellof rice ta debo da fried plantain tadawo sama ta zauna tanaci, ture kwanon gefe tayi ta daura kanta akan gado tana duba watsapp messages dinta.

Sama da awa daya da rabi kenan yana bakin anguwan su dan ko la'asar ma anan masallacin bakin titin yayi, yana sanye cikin wani farin yadi mai kyau ya daura hula akai, agogon dake hanunshi wanda Eesha ta bashi ya kalla 5:25, kunna motar yayi yay kwana ya shigo anguwan nasu yay parking a kofar gidan su shiru yayi yakasa fitowa, toshi yanzu wama zaice yazo nema baima san sunan ta ba, yafi minti uku a zaune ganin zuciyarshi takasa hakura yasa ya fito ya rufe motar. Mai gadi dake zaune kan benci a kofar gidanne yataso da sauri dan yagane shi mutumin daya gani jiya da Islam ne lokacin daya fito daga kewaye, washe baki yayi yace "yallabai barka dazuwa, wajen hajiya kazone?" shiru yadanyi dan baigane wace Hajiya yake nufiba, zaiyi magana mai gadi yace "koba Kaine wanda nagani tareda hajiya jiya kasa kayan kwallo?" murmushi yamai yace "eh nine" mai gadi yace "to biyoni dan Alhaji yacemin na dinga kai baki cikin gida bayason yaran shi na tsayawa a waje" bai jira amsar Khaleel ba yabude gate ya shiga Khaleel yabi bayanshi har suka kai wajen kofar shiga dakin mai gadin ya juyo yace "bari nagaya musu" bude kofa yay ya shiga ciki Anty Hindu da Maman Miemie ne suke dan hira ya gaidasu yace "hajiya dama wanine yake neman hajiya Islam, gashi nan ma" zama Anty Hindu ta gyara tace "okay shigo dashi" fita mai gadin yay yace "ance kashigo" sosai yaji kirjinshi nabugawa ahankali yabude kofar ya shiga mataye biyu yagani Babbar daya gani wacce daga gani kasan tama girmi Ammin shi yadan duka kadan yace "ina yini Hajiya" murmushi Anty Hindu tayi tace "Lpy Lau" ta kalli Maman Miemie dake zaune gefenta tace "jeki kirata" ta kalli Khaleel dake tsaye har lokacin kanshi akasa dan wani irin kunya yaji yakamashi tanuna mai kujera tace "bismillah zauna mana" ahankali ya zauna itakuma ta bude newspapers dake kan table din gabanta ta cigaba da karanatawa.
Bude kofar dakin tayi Islam dake gyangyadi ta shigo ta tabata tareda kiranta tace "Islam Islam" Farida cikin bacci tace "maman Miemie kuna damuna plzz" maganar Farida ne yatada Islam Maman Miemie tace "Anty Hindu na kiranki tana palo" da sauri ta mike tsaye, da dan gown dinan iya guiwa da gashin ta datai parking yana lilo tafito daga dakin, dayake daga sama Anty Hindu kadai zaka iya hangowa danshi yana kan kujeran dake ta ciki sakkowa tayi ta shigo falon kai tsaye tazo gaban Anty Hindu ahankali tace "gani Anty" rufe jaridar Anty Hindu tayi tace "banike neman kiba game neman kinan" ta nuna mata Khaleel da tunda ta shigo idanunshi ke kanta, juyowa tayi ganinshi yasa numfashin ta ya tsaya chak zazzaro idanu tayi tana kallon shi unbelievably, wawwaigawa tayi hijabin Maman Miemie data gani akan stool din dake kusa da Anty Hindu ta dauka da sauri ta saka dan juyawa tayi ta kalli fuskar Anty Hindu ganin ita take kallo yasa ta daburce cikin inda inda tace "uhnn dama dama" ta nunama Anty Hindu shi da hanunta tace "uhn, dama brother yar ajinmu ce, ta turoshi ne yakawo min note ko" ta kallai ware ido yay ya kalleta zaiyi magana tai sauri tace "yauwa ina note din data baka ka kawomin din?" kasa magana yayi dan baima san mezece fa, kara kallon Anty Hindu tayi ganin ita take kallo har yanzu yasa tace "ahhh yana mota? Muje na amsa saika tafi ko" tai hanyar fita daga dakin ahankali ya tashi ya kalli Anty Hindu yace "sai anjima Hajiya" murmushi tamai tace "daga zuwa ka tsaya kasha drinks mana" da sauri Islam tace "yana azumi ko, yau Monday" ta kalleshi gyada kai yayi yana dan murmushi, murmushi itama Anty Hindu tamai tace "to shikenan mun gode agaida su Mum" bude kofa Islam tayi tafito yabiyo ta abaya yana wani irin murmushi.
[6/16, 8:26 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

23 & 24

Saida takai bakin gate sanan ta juyo ta kallai cikeda masifa tace "wai wat is ur problem with me ne eh? Dan Allah ka rabu dani" "I can't" yafada tareda folding hanunshi a kirji yana kallonta, kwafa tayi tace "okay shikenan duk randa nama kara saka ka a idona sainai reporting dinka to police station" dan murmushi yayi dan baiso tadena magana ba, ta gefenshi tazo zata wuce yariko bakin hijab dinta da sauri ta dawo tana waige waige ko akwai wani a tsakar gidan ta kalleshi tace "na shiga uku wanan wai kai dan Allah wani irin mutum ne, wlh wlh kaga na rantse sau biyu niba nice wacce kake nemaba, Allah zan hadaka da Abba nafa this is not norm...al" hanunshi dayasa akan bakinshi yamata alamun tai shiru yasa takasa karasa maganan da kyau kirjinta nawani irin mugun bugawa gashi yaki sakin bakin hijab din nata balle ta gudu, ahankali yadan zo kusa da ita kadan, sosai taji kirjinta ya cigaba dawani irin mugun racing gashi takasa magana kaman yay mata magic dawani irin murya yace "will you marry me plz?" jin maganan tai daga sama da sauri ta kalleshi danta tabbatar shiya fada inko dai shiya fada to mutumin nan baida lpy, dawani irin murya yace "plzzzzz" wani karfi taji yazo mata ta fizge hijabin ta tana wani irin hararan shi da manyan idanunta, batare datace komiba tazo zata wuce ajiyar zuciya yadan sauke yace "at least kifada min sunan ki to kafin kitafi" juyowa tai ta kalleshi taja tsaki ta wuce fuuuuu, yafi minti uku a wajen da kyar yadaga kafan shi ya bude gate yafita kanshi nawani irin ciwo, shi kadai yasan me yakeji.
Ahankali ta bude kofa ganin Anty Hindu bata falo yasa da gudu tai sama ta shiga dakinsu, Farida tagani zaune tanacin abinci tace "waye yazo wajen ki Fahad ne?" tsaki tadanyi tacire hijabin Maman Miemie ta ijiye tace "wani unwanted guest ne" tai tsaki tawuce bathroom dan tadan wanke fuska jin har yanzu kirjinta na bugawa.

Yau dasafe takeda lectures while Farida Kuma sai 11, da wuri ta shirya cikin atampa ta daura Maroon hijab akai dayay mata kyau Bala ya dauketa a mota aka bude musu gate suka fito, hada ido sukayi da Khaleel dake sanye cikin sport wears kafarshi cikin Nike sport shoes yana jogging agaban gidan su, gadan towel dinshi akafada yana goge zufa idan yayi, wani heart melting murmushi ya sakar mata daya fito dayar wushiryar shi, ya daga mata hannu alamun Hi, sanan ya cigaba da jogging abinshi kaman da gaske, dauke kai tayi daga kallonshi ta turo baki tacema "Bala mutafi" samun kanta tayi da kallonshi ta mirror mota taga ya daga mata hannu da sauri ta dauke kai.
Chapter 13 · 0% Book details