← Book details Hauwa Kulu Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 23

Sashe 9

Hauwa Kulu Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar da Madinah ta fahimci wai soyayya ake tsakanin Sumayya da Usman ta sha mamaki, at the same time a take anan ta nuna wa Usman rashin goyon bayanta, da hujjarta na cewa Sumayyah tun fil azal ba ta kaunarta, kuma an gaya mata ita ce ta hannun daman matar wulakancin da sarham ya auro mata.
Usman kuma ya ce mata, a gaskiya shi bai son gutsiri tsoma irin na mata ba, ya ga Sumayyah ta yi masa, komai nata ya yi masa ba ruwanshi da shirmensu, Sarham kawai yake jira ya dawo ya gabatar da kansa.
Madinah ta lashi takobin ita kuma sai bayan ranta Usman zai auri makiyarta. Ko mata sun kare a duniya bazata bada goyon baya ba, dama dai Surayyah ce kuma tayi aure ita.
**** **** ****

KANON-DABO
A
ka kawo masa visa din Hauwa a wayewar garin litinin, bayan an gama bugawa. Mama na shirin fita office sallamar Sarham ta dakatar da ita. Ya shigo dakin da karfin gwiwarsa yau dai, da kallon marairaita da karbar laifi, suka gaisa shi da Mama ba yabo ba fallasa.
Cikin brown envelope ya mika mata abu,
Ga shi Mama na karbo!.

Mama ta amsa ba tare da ta san meye a ciki ba, tana kokarin budewa ta gane passport ne.
Za ta fara fadan har yaushe aka je aka yi passport din ita bata sani ba, ta tuna subutar bakin Hauwa na cewa, sun fita da Sarham kwanaki. Ta yi kwafa kawai ta aje a gefe ko bude visar ba ta yi ba balle ta ga wace iri ce ko ta wata nawa ce. Murya fal ladabi Sarham ya dukar da kai yace,
Mama kin yi izni za mu iya tafiya tare? Already na yi mana booking jibi ne tashin namu insha Allah.
Mama ta yi shiru, ya ci gaba da roko, da ban hakuri da ban baki da alkawarin bazai kara maimaita kuskurensa ba kuma zai kula da Hauwa tsakaninsa da Allah. Da kyar Mama ta ce,
To karatunta fa?
Ma yi wannan shawarar daga baya in mun je naga yadda abubuwa zasu kasance.
Mama sai ta kasa musantawa, tunda abin da ta ke rokon Allah dare da rana ne yau Ya amsa musu. Sarham ya dawo kan hanya kuma ya fahimci kansa. Ko bai fada ba ta ga ‘seriousness’ a kan Hauwa wannan karon a tare da shi sosai.
Duk da haka ta kawo nata kalubalen na cewa, ya zai tafi da Hauwa babu Mardiyyah?
Wa zai dinga taimaka mata?
Sarham ba tare da tunanin komai ba, ya ce, I will take care of her, my self Mama, for the mean time, kafin in yi deciding akan ko zan iya daukar Mardiyyar a gaba. I will do everthing to undo the hurt I caused you Sweet Mum.
Mama tayi ajiyar zuciya a karshe, ko bata ce ba hakan na nufin amincewarta.

Hankalin Mardiyyah ba karamin tashi ya yi ba jin Mama ta ce ta hada wa Antinta kaya za su tafi Jeddah.
Mardiyyah tana kayan Hauwa a jakar matafiya tana kuka wiwi, amma ta danne bakin da dankwalin ta kada Hauwa taji kukanta, amma saida taji sheshsheka. A kwance take amma saida ta tashi zaune tace Mardhiyya lafiya? Ta gaya mata abinda aka ce da ita. Hauwa kanta jikinta yayi wani irin sanyi. Mama ta alkawarta ma Mardhiyyah tafiya Saudiyyah tare da ita duk lokacin da za ta je umrah, kuma ba za ta mayar da ita Shanono ba ko ba Hauwa a gidan, za ta ci gaba da zama tare da ita ne har aurenta.
Hauwa kanta na kasa, ko dagowa ta kasa yi sabida nauyin Mama da damuwar data cika ranta. Mama lakca guda ta hau yi mata a kan ta zauna lafiya da kowa da zama ya hada ta da shi, kuma ta girmama Madinah tunda ko a girme ta girme ta, ba a aure kawai ba.
Ta ce, Na san ba ki da matsala ko kadan a kan girmama na gaba da ke Hauwau, amma zaman mata biyu karkashin inuwar miji daya sai an daure an kai zuciya nesa ba kusa ba. in ba haka ba duk zaku taru ne ku kai junanku wuta. Ki sa a ranki ibadah ki ka je yi domin zaman aure ibada ne Hauwa, balle wanda ya zamo ku biyu ne a wurin mijin.
Jikin Hauwa bakidaya ya yi laasar ta soma hango babban kalubalen dake gabanta, nan take ta ji kamar ta ce da Mama babu inda za ta je, amma ganin yadda Mama ke ta kai da komowa wajen yi mata shirin tafiyar, da bata magungunan da bata san ma kona menene ba da yadda Sarham din kansa ya dauki komen nata Jeddah da matukar muhimmanci sai ta kasa magana, duk da Mama ba ta kara bari sun kebe ba, ta maida Hauwa dakintama kwata-kwata ana saura kwana biyun su tafi, tana ta yi mata kyakkyawan shiri da tsumi kala-kala da tukudi.
Ita kanta Hajiyar Abba, wato Hajiyar Gadon Kaya cewa tayi ba ta ga dalilin zaman Hauwa tare da su ba, in makaranta ce ai babu inda babu ita. Kada su sake su bata mata rai su tattara mishi Hauwa ya dau kayarsa. In don rashin ido ne ya sa Mama ajiye ta shekara guda a daki ai ya fi kowa sanin ba ta da idon ya je ya auro ta.
Ranar sun sha fadan Hajiya Kulu wadda ta yi tattaki har gida ta sille Mama da Abba don Sarham ya gaya mata takunkumin da Mama ta saka masa na saki, da yaki kuma ta kuma hana shi ko magana da Hauwa.
Shi ya sa ma ranar da ya kawo visa mama ba ta yi dogon jainja ba, don Abba ya ce a daina yin duk abin da zai saka Hajiya Kulu yin fada, saboda BP dinta.
**** **** ****

Duk wani shiri na tafiyar hauwa Mama ta gama sbhi cikin lokaci, komai da tasan zata bukata ta tanadar mata. Kuma ita da kanta ta kai su filin jirgin Malam Aminu a ranar tashin nasu. Bata dawo gida ba sai da aka kira fasinjoji domin shiga jirgi.
A daren ranar duk kokarin Sarham na samun Madinah a waya bai yiwu ba, ko network ne ko wayar tata a kashe take? Ya so tun a daren ya gaya mata cewa tareda Hauwa zai dawo. Ta shirya mata daki daya cikin dakuna biyun da bata amfani dasu. A zuciyarsa baabu fargabar komai, don yarda zuwa yanzu dole ya kara zama namijin duniya a tsakanin matan nasa kuma ya zauna da Hauwa cikin iyalinsa cikin adalci, bai yarda da raba gida ba shi raayin sa shine samar da kyakkyawar muamala ta fahimta da taimakekeniya tsakanin Jiddah da Madinah kasancewar Hauwa nada lalura. Ba zai kaita wani gida ta rayu ita kadai ba.
Yana fatan wannan din ya hada kan iyalin sa da samar da zaman lafiya da kaunar juna a tsakanin su. Don shi wai bai yarda da hargagin Madinah na cewa ita Madinah tafi Hauwa komai ba, wai don tana takama da tanada zurfin ilmi da iyaye masu kudi yen-yen-yen to shi ina ruwansa da wadannan din, tunda dai shi ko wani nasa bai taba aikawa gun Daddy neman taimako daga ISDB ba, itama ba su ne dalilan da suka yi mujazar auren shi da ita ba.
Dr. Sarham Abbas ne rike da hannun matarsa Hauwa Bilyaminu, suna taka matattakalar jirgin ‘emirate’ wanda zai tashi da su zuwa kasa mai tsarki a daren yau.
Hauwa kankame ta ke da hannun Sarham cikin tsoro na rashin sabo take taka matattakalar, shi kuma ba tare da damuwa da kallon da ake musu ba ya rike hannun nata sosai yana gaya mata cewa,
Mind the stairs (ki kula da matattakalar).
Lokacin da jirgin ya karci kasa zai tashi, Hauwa ba ta san sanda ta saki salati ta kara damqo Sarham ba. Wasu Larabawa mata da miji a kusa da su, sai da suka yi mata dariya, don sosai ta ke cikin gigita da karar tashin jirgin. Wani hargagi ne da bata taba ji ba mai barazanar buga dodon kunnenta.

A cikin jirgin, shi ya sanya hannu a kwibin Hauwa ya daura mata belt, lokacin da larabawan na kusa da su suka fahimci cewa matarsa ce kuma bata gani ba karamin burgesu Sarham yayi ba sabida yadda yake kula da duk wani motsinta. Ga idanun nata a bude tar masha Allah dasu. Sai da matar ta karbi adireshin su na can Jeddah suka ce su kuma a Taif suke zaune In sha Allah suka shigo Jeddah Sayayya watarana zasu kawowa Hauwa ziyara har gida.
Ba su tsaya a koina ba wato babu transit sai a airport din Sarki Abdulaziz.
Hannun Sarham still cikin na Hauwa, a lokacin da suke (passing immigration checks) na shiga kasar Saudiyyah har suka kammala. Taxi (Ajrah) suka hau, mai Ajrah ya ja mota zuwa hanyar gidanshi da ke cikin gidajen likitoci na Saudi-German.

Tunda suka hautiti Hauwa ta cire yatsunta daga cikin na Sarham. A lokacin shi yanata kokarin saka layin shi na Saudiyyah a wayarsa. Ta mika cikin tunani. Ba kuma tunanin komai take ba face tunanin irin tarbar da matar likitan nata zata yi mata. Da kuma irin zaman da zasu yi tare, duk da cewa na dan takaitaccen lokaci ne wato hutun ta na semester inji Mama.
Shikuma ya sa a ransa Hauwa ta zo Jeddah kenan, wato bazata koma Najeriya ba. tun a cikin motar ya soma browsing din makarantu a cikin birnin Jeddah don nema wadanda ke hada karatun su da speciality na masu bukata ta musamman wato makarantun da ke yin (Inclusive Education).
**** **** ****

KAFIN SAUKAR SU DA AWANNI BIYU

S
umayyah na goye da Waheedah tana goge dining, Madina na daki tana waya da Usman cikin zafin rai, sai Allah ya baiwa kunnuwan Sumayyah damar zuqowa.
Chapter 9 · 0% Book details