← Book details Hauwa Kulu Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 23

Sashe 17

Hauwa Kulu Part 4 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sabuwar kulawa, sabon amarci ya balle wa Sarham da Hauwa a dalilin wannan niimar da ke tattare da mace mai yaron ciki. Sarham da Hauwa sai sam-barka, a yayin da Dr. Madina ta yi nisa kan ayyukanta na Dr. Siddiqah, da ayyukan tiyatar ido na sa-kai (philanthropic eye surgery) da takeyi don taimakon marasa karfi bayan ta warke daga tiyatar da aka yi mata.
Daddy ya tabbatar mata tunda Sarham yaki sakinta ta ruwan sanyi kamar yadda ya bukata, wallahi kotu zaiyi kararsa sai ya saketa. Bazai zuba ido ya kashe masa ya ba.
Hankalin Madinah yayi matukar tashi gashi an hanata sauraron Sarham. Aka ce tsakanin mace da miji sai Allah, lokacin da ta sauko tana son ta karbi mijinta ya dade da sabawa da Hauwa, irin sabon da ko ita Madinah da ya kwashi ‘decade’ yana soyayya da ita bai yi shi da ita ba.
Kasancewar shi ne komai din Hauwa a gidan, dakinsu daya makwancinsu daya kullum, kullum kafin ya fita sai sun karya kumallo tare wanda shi yake sarrafawa da kansa, da rana kuma zai sa ‘mudam’ din cikin estate dinsu su yi mata home delivery’ na abincin rana, idan kuma ya dawo da daddare ya girka musu. Yayi musu wanki a injin wanki ya zauna zaman goge mata abayoyinta da hoover.
Ita da kanta Madina ta koma tunanin anya wannan sabuwar rayuwar ta zaman gida da iyayenta suka zabar mata mai billewa ce? Gashi mijin ba sakinta yayi ba yanata bin Daddy har office da ban hakuri itama Madina yana bata. Ta soma tuno yadda yake saka apron ya shiga kitchen yana girki tukuru domin hidimtawa miskiniyar matarsa. Duk a kokarinsa na sauke nauyinsu su duka da Allah ya dora masa da kuma cewa da tayi baza basu abinci duk ranar girkinHauwa ba.
Ta yarda Sarham ba mijin yadawa bane domin nagartarsa ta wuce ta sauran mazan da ubanta ke mata hange. Don haka ta soma tunanin mafita, wato yadda zata koma dakinta ba tareda daddy yayi fushi da ita ba don ita kanta ta san Sarham bai yi mata laifin komai ba laifinsa daya ne kara aure na tawaliu. Don haka ta koma lallashin Daddynta, ta tuna sanda Sarham ya ce in har ba za ta dinga dafawa tare da Hauwa ba kuma ba za ta yi muamalar makwabtakar musulunci da ita ba, to ya yafe cin abincin nata shima da take ajiyewa a dining ta fita.
Ta tuno irin kalaman batancin data ke masa amma duk Sarham ya shanye bai taba korarta daga gidansa ba. Irinsu;
A wane dalili za ka ce wai lallai sai na zama kukun matarka? Ka gaya min inda shariah ta dora min wannan nauyin.
A wane dalili za ka dage lallai sai na yi muamala da matarka? Na gaya maka in na raina kasuwa ko sauti bana bayarwa a cikinta.
Shin ajin rayuwata da na matarka daya ne da za ka ce sai na muamalanci wadda ko matsayin zama yar aikin gidanmu ba ta kai ba?
Ire-iren kalamanta kenan gareshi tun zuwan Hauwa, da saidai Sarham ya daga ido a hankali ya dubeta da wani irin kallo na mamaki da disappointment.
Ya ce,, In wani ne ya gaya min cewa Madinah za ta rasa hankalinta, kyakkyawan tunaninta da iliminta na jin kan alumma kai har ma da imaninta, a dalilin KISHI wallahi zan musa. Sai dai kash! Im witnessing it myself to the mere of my disappoitnment.
Ina fatan wannan halin da ki ka ara ki ka yafa babu gaira babu dalili ba zai shafi rayuwar yayana ba, wato ba zai sa ki raba min kansu ba. Da sunan Mamar wadancan ba ajinki ba ce. Ya Allah ka cire rabon shaidan daga zuciyar matata Madinah.
Ya Allah Ka raba ta da GIRMAN KAI da superiority complex wanda shi ya hallaka Kakanmu Annabi Adamu A.S.
Daga fadin hakan sai ya sa kai ya bar mata dakin. Jikin Madinah ya yi matukar sanyi yau, da tunaninta yazo nan, irin sanyin jikin da rabonta da shi har ta manta, tunda Hauwa tazo zuciyarta ta zama gardamammiya ta tsaya cur a kirjinta sai yau ta russuna.
Dr. Madinah Attahiru. Ta soma kokarin tattaro ragowar mutuncinta wanda ta san, har abada ba mai gushewa ba ne daga idanun Dr. Sarhamu.
Itada Usman sukayi shawarar Sarham ya gayawa Haj. Lailah hukuncin da Daddy yayankewa auren ta. tace ita kuma tanason komawa dakinta bazata kara tada hankalinta ba.
Haj. Lailah suka shiryawa zuwa Saudiyyah itada Usman musannan don ta lallashi Daddy tayi sasanci, har bukatar Usman na auren Sumayyah sun gayawa Haj. Lailah ita kuma ta kama Attahiru da fada tace wannna ba gata yakewa yaransa ba yaranma sun fi shi hankali, ita Madina wacwcw data fi karfin ayi mata kishiya? Taga Nana Aisha da Nana Khadija ma duk da kishiyoyi suka zauna. Tayiwa Daddy kaca-kaca ta kuma saka shi ya kira Sarham a waya yace ya zo ya dau matarsa.
Sarham a take ya baro office yaje ya taho da Madina daga gidan mahaigfinta. A hanya kuma kafin su iso gida suka kara dinkewa, suka fabhimci juna, ya kara yi mata kyakkyawan bayanin da yafi na baya akan Hauwa da muhimmancinta ga rayuwarsa kuma ba wadda za iya bari saboda yar uuwarta.
Abu na farko da Madinah ta fara yi bayan dawowarta gidan shi ne, in za ta fita office ta kan leka ta ce wa Hauwa za ta fita, Hauwa da yake bata kullace ta kamar yadda ita ta kullace ta ba sai ta amsa har da adduar.
Allah yasa a dawo lafiya”.
Chapter 17 · 0% Book details