← Book details Hauwa Kulu Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 23

Sashe 8

Hauwa Kulu Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

In ji Mama Maishariah da ta sawo kai dakin da zummar bai wa Hauwa hakuri, donta san an mata abinda ba ta so. An mata GORIN IDO (ta bakinta).
Da sauri Mama ta koma da baya har tana tuntube da dokin kofa. Dukkansu kuma ba wanda ya san da shigowarta, Hauwa ce ta yi maza ta janye tana fadin,
Hasbunallah!” Motsi nake ji. Tare da dafe goshinta don tabbas taji motsin mutum a kofa.
Sarham ya yi murmushi idanunsa a lumshe, ya ce, Yarinya tun ba a je ko ina ba ta fara sanin dadin kiss din miji.
Hauwa sai ta dau filo ta rufe ido da shi tana fadin, Ni wallahi ba ruwana, ni ban san wannan abin ba, duk kai ka koya min yau kuma sai Allah ya saka mini in wani ne yazo ya gani, ai kasan gidan cike yake mutane, ni bana so ma ka daina dakin nan don Allah, kuma ba zan kara binka koina ba.
Har ya kai bakin kofa ya juyo. Ya kanne mata ido kamar tana kallonsa. Cikin kankanuwar murya yace.
This is light kiss, ki shirya ‘hot kiss’ later tonight!.
Hauwa ta danna kai cikin cinyoyinta tana rokon Allah ya sa kasar ta tsage ta shige yau ta huta.
Mama tana kallon wucewarsa zuwa dakinsa ta baro jamaa ta dawo dakin Hauwa. Gaba daya dakin Hauwan yanzu kamshin Sandalia ko Oud-Abyad din Sarham yake yi, wato turarukansa na dindindin (Non-alcoholic Arab perfumes).

Hauwau!
In ji Mama tun daga bakin kofa.
Ashe ni tufka nake kina min warwara?
Hauwa ta kidime iyaka, ta fara mazari na rashin gaskiya murararn. Kada dai motsin data ji Mama ce? Yau da ta kade har ganyenta.
Mama ta ce cikin takaici,
Ban taba ganin sakarar mace irinki ba, kai jamaa, Allah wadaran rashin wayo.
Sai Hauwa ta soma hawaye nan take kamar an balle famfo. Fadi ta ke,
Wallahi Mama babu ruwana, sai da na ce masa ba zani ba. Ta kifa kai a cinyoyinta tana rizgar kuka.
Mama ba ta san da zancen fita ba, rikicewa da rashin sabo da karya tasa Hauwa ta fallasa komai.
Wallahi Mama ban yarda ba, bai yi komai ba nan nan (ta nuna bakinta), kawai na bari, kuma shi ma din fin karfina ya yi.
Mama takaici kamar ya kashe ta, ta mike tsaye tana cewa, Na kuwa daina tada hakarkarina a kan a sake ki, don ki auri mai sonki da gaskiya, tunda naga kina son abinki duk rashin kirkinsa, hada kayanki kafarki kafarsa, kafin a kara yi min abin da yafi karfin idona.
Haba! Hauwa ta rushe da kuka tana, Na tuba Mama, na tuba na bi Allah na bi ki, wallahi ba inda zan iya zuwa in barki.
Mama ta yi kwafa ta ce, ji min munafurcin Hauwa-Kulu, yau da kika sa kafa kika bishi kika barni ma na sani? Ni a wa? Bi mijinki a sha soyayya lafiya, da ma tare na ganku.
Na so ki bari mu wujijjiga shi yadda zai kara sanin darajarki, to kin kwashi jiki kin bi shi kun sha soyayya ko? Bayan ya kwashe shekara bai neme ki ba, da yake ke sakarya ce wadda ta rako mata, kiss din abun banza ne da ki ka barshi ya samu a arha?.
Hauwa kuka kawai ta ke na nadama da kaka-nikayi ta kasa magana, duk sai ta bai wa Mama tausayi.
Ta sassauta ta kama hannun Hauwa, ta ce, Ba ki yi min laifi ba Hauwa kin ji, kuma ba ki yi wa Ubangijinki ba.
Karewa ma lada ki ka samu kinji.
Ni na san Sarham yana sonki duk abin da nake yi kuma ina sane. So nake in sa shi ya gane da kansa yana sonki ba auren jihadi da taimako ya yi da ke ba. So nake ya furta min da bakinsa ya janye kalaman kanwar nan da yake jifanki da ita, It does hurts me a lot!
Karshen kaskancin da namiji zai miki kenan, ya tari gaban idon ki yace, ba ya miki so na soyayya. Sarham ba shi da saiti, ki bar ni in saita shi yadda ko wani ya ji ya ce ke kanwarsa ce zai musa da bakinsa yace aah matata ce abar so na.
Hauwa na kuka da sharbe ta ce,
Insha Allah Mama ba zan sake yarda ba.
Tausayi ya kama Mama don kuru-kuru ga soyayyar lelen Abba nan ta fito yau a idonta, da ko gani ba sa yi, ina ga suna ganin cool kamanninsa da kyakkywan sajen sa da murmushinsa mai daukar hankalin mata?
Mama ta tashi ta fita kwallar tausayi fal idonta.
Mardiyya ta dawo dakin tana cewa,
Anti ba ki ci abinci ba, Anti don Allah ki daina kuka yana daga min hankali.

Ta hau share hawayen da gefen mayafi ta ce, Na daina Mardi!.
Ta ce, To abincin fa?
Sai an jima, ki kulle mu ta ciki, ko Yaya Doctor ne ya buga kada ki bude kin ji? Murajiar karatuna zan yi.
Taje ta dauro alwalla, sai ta ga cewa ba za ta iya alwala a haka ba, dole sai ta yi wanka don abin da ba ta taba gani ba ne ta gani a tare da ita yau.
An gaya mata kuma da jimawa wankan iri daya ne da na sallah.
Ta yi sallah ta dora da nafila ta zauna tana murajiar karatun da Mama ta kara mata jiya.
Cikowar yan uwansu da abokan arziki a gidan ma bai barshi ya iya sake shigowa da daddaren ba balle ya tadda kofar tasu a kulle da mukulli bisa umarnin ko ya buga kada Mardiya ta bude.
Dangin mijin Surayyah suka ce su a wannan ssatin zasu dauki amarya zuwa Ikko don haka dole aka zarce da bikin maimakon sai sati mai zuwa da mama ta saka. Don haka a washegari aka yi wunin Surayya a Gadon Kaya, da daddare dinner sai shirin kai amarya gidan su Engnr. Aliyu a Dorayi washegarin ranar.
Hauwa ba ta je dinner ba ta kulle kanta a daki, amma Mardiyya ta je. Mama ta sameshi har dakinsa ta kora masa ‘warning’ din kada ya kara shiga dakin Hauwa sai ya zo mata da hukuncin da ya yanke wa zamansu.
Shi ma kuma yana ta nasa shirin duk don ya wanke ran Mama, ya kuma yi ‘repenting’ kuskurensa, tuni ya karbo passport din Hauwa ya kai gun visa.
Yan biki duk sun watse bayan an kai Surayya family house din su mijinta. Yau kwana uku kenan Mama na gadin Hauwa, ta hana shi kebewa da ita. Ta hanashi rawar gaban hantsi. Iyakar tsaka mai wuya Sarham ya shige ta don sosai yake cikin bukatuwa da Hauwa, don haka ya maida hankali wajen sakin kudi a yi a gama visarta. Ga Abba ya ki shiga maganar, ya ce shi a bayan mai sharia yake.

*** *** ***

MUTANEN JEDDAH

Sumayyah ce kadai zaune a falon gidan Yayanta tana karatu da gilashi a idanunta, aka danna kararrawar son shigowa, Sumayyah ta mike ta aje littafin da ke hannunta tana fadin, Naam, ina zuwa. A zatonta Madinah ce ta dawo daga unguwar data tafi.
Tana budewa suka yi tozali da wani sardidin saurayi son kowa. Amma kuma fuskarsa looks so familiar to her.
Ya yi mata murmushi, ya ce, Salam, how are you? Tana ciki ne matar gidan? Na kasa kama ta a waya”.
Sumayyah ta kasa magana, don gayen ya kai makura wajen kyau, ga tsafta ga sanyin murya.
Da kyar ta iya cewa, Ba ta nan!.
Sai ya mika mata wata leda ya ce, ok. Please ga shi ki bata, kice in ji Hajja Ramlah.
Hannun Sumy na rawa ta karba sai ya ce, Ke bakuwa ce suka yi halan daga Nigeria?
Eh. Kawai ta ce.
Ya ce, Ok, toh. Ki gaya mata zan dawo bayan magriba. Sunana Usman Attahiru, yaya sunan malamar?
Oh! Are you? Usman?
Ya ce, Yeah.
Anti na yawan zancenka, ina ji kullum. Nice meeting you.
Ya ce, Na gode, kin san sakuwata ce. Kullum fada muke a baya, ina cin zalinta in more, shiyasa yanzu nake kyautata mata, na maida kaina ma direbanta at times, don in wanke kuruciya mara dadi da muka yi nida ita.
Duk suka yi dariya mai sanyi.

Ya ce, Ya sunanki?

Sumayyah Abbas.

Oh-oh! Ko ke ce Sumayyah kanwar Baban Waheedah?
Eh ni ce.
By the way, nice to meet you too Sumayya, I love the name.
Cikin murmushi Sumayya ta ce, Na gode Uncle Usman. A gaida gida.
Bayan tafiyarsa Sumayyah ta adana sakon, amma sai ta kasa zaune ta kasa tsaye, Usman Sorondinki da muryarsa ya tsaya mata a rai farat daya, irin yadda wani namiji bai taba shiga ranta ba.
Madinah na dawowa Sumayyah ta bata lokaci ta kintsa, kafin ta kai mata sakon har dakinta, karonta na afarako da sanya kafarta a dakin Madinah tun zuwanta gidan. Ita kanta Madinah ta sha mamaki.
Ya zo nan kadan kafin dawowarki, yace shi Yayanki ne, wai Osman sunansa.
Oh! Zai dawo an jima, mun yi waya na manta da zuwansa ne na fita.
Sumayyah ta ci gaba da shiru a tsaye, ta kasa tafiya, Madinah ta ci gaba da sabgoginta ta manta da ita. Ganin haka ta ja matattun kafafunta ta fito daga dakin.
Ko da ya dawo kamar yadda ya ce zai dawo, Sumayyah ya cimma a falo Madiah tana daka tana sallah don haka suka balle da hira shi da Sumayyah, kan kace meye wanan sabo ya fara shiga tsakanin Usman da Sumayyah, bini bini ya zo gidan bayan ada sai in Madinah ce ta kira shi ko Hajjah Ramlah ta aiko shi, ya zama suna dasawa sosai har ta kai su ga karbar lambar wayar juna.
Kafin ka ce me? Madinah ba ta ankara ba aka soma yi mata midnight call’ a gida. Sumayyah har mantawa ta ke Usman Attahiru Yayan Anti Madinah ne, gabadaya ta rufta nan take, kafin dawowar Sarham.
Chapter 8 · 0% Book details