← Book details Hauwa Kulu Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 23

Sashe 12

Hauwa Kulu Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wannan ya sa Hauwa ta dan saki ranta, jin cewa za su fita su mike kafafunsu. Don dama sai mutsuka suke mata na zaman jirgi.
To ka fita zan yi wanka
Allah ya yarje min inga komai na jikin matata Hauwa
Ya fada yana sirka mata ruwan wanka.
Saida ta hada da rokon shi Allah Annabi ya bata waje sannan ya fita ya rufo mata kofar.
Ta yi wankanta da kyau da ruwa mai zafi domin warware gajiyar da zaman jirgi ya haddasa mata, tana wanka tana tunanin yadda zamanta da Maman Waheedah dinnan mara kirki zai kasance a gidan, wadda a zahiri ba ta marabci zuwanta ba, kuma ba ta shirya zama tare da ita ba, kafin maigidan ya kawo ta meyasa bai gaya mata matarsa bata da kirki ba, kuma bai nemi yardarta ba ya daukota ya kawo mata gida?
Wannan ya nuna shi Sarham mutum ne mai yin abin da ya sa kansa a gidansa ba tare da shawara da mata ba. Ita dai ta san za ta yi ‘tolerating’ komai, za ta yi wa Madinah biyayya kamar yadda Mama da Inna suka nusarsheta, abu daya ne ba za ta lamunta ba, Madinah ta keta rigar mutuncinta ko ta ci gaba da kiranta da duk sunayen wulakancin da ta ga dama
Wata doguwar rigar atamfa Hauwa ta sanya Chiganvy da aka yi wa wani ubansun dinki wanda ya fiddo kyakkyawar surarta sosai ba tare da ta san yadda kayan suka karbi jikinta ba, ta dauki mayafin da Mardiyyah ta manna a cikinsu ta yafa.
Tana cikin fesa turare Dr. Sarham ya shigo sanye da farar sabuwar jallabiya mai matukar tsada, sai tashin nasa kamshin na musamman yake yi.
Oya lets go, kin gama ai ko?
Idonsa ya kai ga dressing dinta ya kankance ido, Me-ji! Cire wadannan kayan maza-maza, kin manta a Saudi-Arabia ki ke? Ko ba a can ba ne in aka ce ki fita da wannan dinkin jikinki na juyawa a cikinsa sai ki fita don hankali ya wadace ki ko?
Hauwa ta hau shafa dinkin jikin nata wai ta ji me ye laifinsa.
Ka yi hakuri, ka san dai ba na gani.
Umh! Da wani ne ya fada da yanzu cibi ya zama kari, canza su maza-maza ina jiranki.
Ya ci gaba da tsayuwa kuma bai fita ba.
Hauwa ta rausayar da kai gefe, To a gabanka zan canza ne Yaya Sarham?
Ya yi wani dan murmushi cikin rashin jin dadi ya juya ya fita yana cewa,
Na ba ki wuri, Mrs., matsayina na Yaya har yanzu yana nan bai canza ba kenan ko?
Bai kuma tsaya sauraron amsarta ba ya juya zai fita tayi maza ta riko shi.
Za ta so kwarai ta ga fuskar likita Sarham a yau, ta tabbata wanka ya dauka ko daga niimtaccen kamshin da yake zubawa a dakin.
Hauwa ta yi ajiyar zuciya tana ji a jikinta lalurar makantarta ta har abada ce ba ta da magani, don ba ta taba ji ko ganin makahon da idonsa ya bude ba.
Don haka fatanta na ganin fuskar likita Sarham zai ci gaba da kasancewa fata (hope) irin wanda har dan Adam ya koma ga Ubangijinsa bai samu cikarsa ba (actualizing of dream) dinsa.
Ta hau lalubar fuskar Dr. Sarham ta saka fuskar shi a tsakanin tafukanta biyu, tana shafa tattausan sajen gefe da gefen fuskar tasa, ta ce You are my HUSBAND, not a brother, and my everlasting dream is to see you with my naked eyes.
Sarham yayi maza ya hade bakin su wuri guda, yana sakar mata mata wata irin zazzafar sumba mai tsayi da zurfi kusufa-kusufa lungu lungu sako sako a cikin bakinta.
Hauwa sai ajiyar zuciya take yi, kwalla ta taru a idonta, ta yi maza ta rike shi gamgam itama, nan ya idasa rikitata ta hanyar kai bakin shi saman kirjinta, daga wannan lokacin suka lula a wata duniyar maaurata mai ban mamaki da shiga rai. Hauwa na neman shidewa Sarham ya dauketa a hannunsa zuwa gadon dakin, har da wata irin sheshshekar fita hayyaci yake yi a jikin Hauwa kai kace bai taba rike mace ba, yana kiranta da sunayenta kala-kala. Wadanda take so (Hauwau-Jiddah-Maijiddah) da wadanda bata so (Kuluwa ta, Kulun-Majadun dina, ni ina ganin ki kuma ina son ki a hakan, ko baki ganni ba)”.

Tunda Madinah ta kulle kanta a daki ba ta kara ko lekowa falo ba, sai kukan Waheedah ka ke ji yana tashi a gidan, wadda da alama ba ta samu lallashin uwa ba. Wannan kukan na Waheeda har cikin kwakwalwarsa yake tabawa, kukan Waheedah shi ya ceci Hauwa a hannun Dr. Sarham yau kuma, ba don haka ba da tuni ta amsa sunan sauran mata yan uwanta.
Taimaka mata yayi ta canza kayan zuwa bakar abaya da mayafinta. Ya san da gayya ta kyale Waheeda take jiniya don haka ya kama hannun Hauwa suka fito ya rufe dakin suka bar gidan.
Madinah na jin rufe kofarsa ta leka waje ta tagar dakinta. Nan ta hange su suna takawa a kasa gwanin ban shaawa, ya rike hannun Hauwa cikin nasa. Ba ta san dai ina za su je ba, amma jikinta ya ba ta ‘mudam (restaurant) da ke cikin estate din nasu za su je, wato wajen cin abincin likitocin Saudi-German.
Wani abu ne da za ta iya cewa tunda suka yi aure rabon Sarham da shi wato cin abinci a Mudam, don ko ba ta dafa abinci ba zai wa cikinsa yan dabaru ne ya zauna lafiya. Sai ta shiga tambayar kanta shin abincin da ta dafa ta kwashe don kar su ci ta kyauta? Lallai kishi mai maida babba yarinya mai juya hankalin mai hankali. Kyabe baki ta yi, ta ce,
Ba hakkina ne ciyar da su ba daga shi har matar tasa.
Shi da ya ga zai iya wahala da makauniya sai ya fara tunda wuri, kafin wankin hula ya kai shi dare don in yana zaton ni zan kula masa da mata ya yaudari kansa.

Suna tafe cikin tsanaki a gefen titi, Sarham na tausar zuciyarta a kan kalaman Madinah.
Ya ce, Ki daina damuwa don wani ya ce miki makauniya, ko mara gani. Makaho bai isa ya hana alumma kiransa makaho ba, haka kurma bai isa ya hana alumma kiransa kurma ba. Thats the same with gurgun mutum (physically challanged) bai isa ya hana a kira shi gurgu ba, but accept it, like it, appreciate it. Accept your disability, enjoy it sai ta zame miki unique identification ba tare da ranki ya baci a banza ba.
Ni idon nan da ana musanye da mun yi na huta da wannan bacin ran na GORIN IDO tunda ban isa hana mutane kiran Hauwa-Jeddah makauniya ba.
Hauwa, ta daga manyan idanunnan farare kal, tayi harr! Dasu a kan Sarham da wani irin murmushin jin dadi a fuskarta. Sarham ya shafa kansa zuwa keyarsa jin wani ignition na fizgarsa, yace kada ki kashe ni da idanunnan Hauwa, I loved them, ina son daren yau in samu Safiyyah ko Maimunatu mai irin su, daga daren farko mai albarka.
Hauwa ta kai tafukanta ta rufe fuska cikin jin kunya da karuwar Son Sarham mai tsanani a zuciyarta.
Daidai lokacin da suka isa mudam din suka shiga. Akwai tsirarun mutane, amma ba su da yawa, ya samar musu waje can nesa da kowa ya zaunar da ita, sannan ya je ya yo musu order din zazzafar kazar nan ta (Kentucky Fried Chicken) da aka fi sani da KFC da Chips, aka hado da zazzafan coffee mara sugar aka kawo musu.
Yau Hauwa sai ta samu kanta da jin kunyar cin abinci a gaban likita Sarham, ba su taba cin abinci tare ba sai yau. Shi kuwa bai lura wai kunya ta ke ji ba ya dinga dauko tsokar kazar da chicken nugget yana saka mata a baki ko ya tula mata tsokar a gabanta.
Ki ci ki koshi fa, kada ki ji yunwa cikin dare.
Ta soma ci a yangance ya ce, Maijiddah ni saurayinki ne ne da ki ke min wannan yangar taunar yen-yen- alhalin na san yunwa ki ke ji?
Hauwa ta rufe ido tana yar dariya a haka ya saka mata nugget guda a baki ya cika mata bakin taf, ta hau dariya tana tauna tana rufe ido.
Da suka gama suka tako zuwa gida kasancewar ba tazara sosai tsakanin flat dinsu da mudam din.
Tunda suka dawo a falo ya zaunar da Hauwa ya fita ya rufe koina na gidan. Madinah dama ta garkame dakinta tuni amma tana jin dawowarsu kuma lokacin ta gaji da kukan Waheedah itama ta bata nono wanda hakan yasa Waheedah barci.
Suna falo tare har karfe tara na dare yana kallon labaran Aljazeerah kafin yunwa ta koro Madinah daga daki zuwa kitchen.
Ta wuce su, ko kallo ba su ishe ta ba, shi ma ya kalle ta da wutsiyar ido ya kauda kai, yana kokarin kashe talabijin ya ce da Hauwa, Mu je mu kwanta haka, don gobe insha Allah zan fita da wuri na shiga asibiti.
Chapter 12 · 0% Book details