← Book details Hauwa Kulu Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 23

Sashe 3

Hauwa Kulu Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

alhalin yana ikirarin zamansa take yi, yana aurenta har tsayin shekara guda da sunan ba sonta yake yi ba, in this regard, mu iyayen ta da kai Yayanta wane mataki ya kamata mu dauka??? Kuma kaima ka fada ka sake har a gaban idona da gaban idonta cewa kai kanwar jini ka dauketa ba mata ba. Don haka nake ganin, abu mafi maslaha shine Sarham ka sahalewa Hauwa aurenka, yadda dana gama bikin Surayya itama in zo in fara shirin nata itada Sumayyah. Wannan karon aure zan yi mata na gata da soyayya da wanda yake sonta itama take son shi da zuciya daya. Don haka Sarham, ina jiran takardar sakin HAUWA-KULU daga nan zuwa gobe kafin ka fita daurin aure". Dr. Sarham tun daga yatsar kafarsa har zuwa tsakiyar gashin kansa gumi ya shiga karyo, ya rasa a yanayin da kalaman mahaifiyar sa suka jefa shi. SAKI! Saki fa. Kai tsaye Mama ke nema tsakaninsa da Hauwa-Kulu. Shi ai babu saki tsakanin sa da Hauwa koda babu soyayyar aure. Da wane ido zai dubi Inna Safiya da Malam Bilyaminu yace dasu wai yau ya saki Hauwa???". Mama bata kara bi ta kansa ba, ta tashi ta bar masa dakin jin shigowar Abba Prof. Ko motsi ya kasa daga inda yake zaune balle ya fita don ya gaida Abba. Abban ne da kansa ya karaso har kofar dakin Mama sai ya ganshi a zaune kamar sassakakken gunki. Ya ce "a'ah, mutanen Jiddah ne? Maraba lale da Lelen Abba, Jabbama-jabbama, yaya hanya da kuma amaryata-uwata Hajiya KULU?" Sai lokacin Abba ya lura da irin jibi (zufa) wato gumin da Dr. Sarham keyi daga zaune. Kamar wanda aka fiddo daga tanderu. Abba Prof. yace a hankali. "Ko lafiya?" Sarham bai san sanda ya zube gaban Abba Prof ba yana rokonsa, kan don Allah ya baiwa Mama hakuri. "Me ke faruwa? Me kayi mata?" Idanunsa sun kada sunyi jajir, yace "Abba koma wane irin laifi take tuhumata dashi na amsa laifina. Amma don Allah ka roketa ta janye kalmar SAKI tsakanina da Maijidda. Zan iya yi mata komai amma banda saki tsakanin mu. Auren mu na har abada nake burin ya zama. Me zance da su Malam Bilyaminu idan Mama ta takura min na saketa?" Mama ta dawo dakin tana cewa da babbar murya mai cike da bacin rai daya dade yana cinta a zucci; "ai kawai cikakken bayani zaka yi musu na irin rikon auren da kake yi mata tunda suka baka ita, cewa kai kanwar jini ka dauketa ba mata ba, suyi hakuri kawai, zaifi musu alkhairi, su karbeta daga hannunmu su aurawa dan Malam Munkaila a kan ka. Na tabbata zai kula da ita zai bata hakkin ta na aure kamar yadda addini ya ce yayi, ba zai bi son zuciyar sa a kanta ba wai don zumuncinsa da iyayenta. Ba zai zauna yana rusa mata rayuwa ta hanyar rashin bata gurbin matar aure, at the same time yana rusa lahirar sa ba da sunan wai yana taimaka mata". Idanun Mama a warwaje take magana kamar zata kife Sarham da Marika, ko ta samu ya shiga hankalin sa ya gane meye a zuciyar sa game da Hauwa-Kulu. Budar bakin Abba Prof. Sai cewa yayi "Da kyau Mamansu, ina bayanki anan Mai Shari'ah uwar kowa. Ai mu saidai mu ce maka Allah yayi maka albarka ka kawo mana diya abar alfaharin kowadanne iyaye. Don haka ka sahale mata shi yafi alkhairi in yaso ta cigaba da zama tare damu tana karatunta har Allah ya bata mijin dake sonta da gaskiya. Ko jiya an tambayeni ko tanada aure? Wannan al'amari daman ya isheni, don ko na ce tanada aure ba yarda ake yi ba". Iyakar tashin hankali Dr. Sarham ya shigeshi irin wanda bai taba shiga ba. Mama ta saka murya ta kwalawa Hauwa kira. Mardiyya ta fito da ita da hanzari ta zaunar a gaban Mama ita kuma ta koma daki jikinta na bari. Mama ta ce cikin zafin rai "ga ni, ga ka, ga Abba ga kuma Hauwa. Inaso ka sahalewa Hauwa aurenka". Ta dubi Hauwa wadda ke tsugunne kan kujera a dofane cikin firgita, don ta kasa gane me akeyi, ta san dai abinda zaisa Mama fushi irin haka ba karamin abu bane har dakinta take jiyo tahin fadanta. Mama ta daka mata tata tsawar "ke Hauwa! Nace wannan mutumin ya sake ki haka, ko kinason cigaba da zama da aurensa?" Hauwa ta hadiyi miyau da kyar, ji kake, mukut, da kyar ta daga manyan idanunta a daidai saitin da take jin sukar idanun Sarham a jikinta. A lokacin shima ya dago, goshi duk zufa, cikin kidima da tsoron abinda zata ce. Da kyarmar murya Hauwa tace "a'ah, bana son auren, Yaya Doctor ai Yayana ne babu son aure tsakanin mu". Kai kace Mama ta karanto mata abinda zata fada ne kafin ta kira ta, yadda take maganar tiryan-tiryan cikin kyarmar murya. Mama tace "to kaji, don haka daga yau zuwa gobe kafin fita daurin auren Surayyah ka rubuta takardar sakinta ka bani hannu da hannu, umarni ne ba zabi na baka ba". Daga haka Mai Shari'a ta bar wurin cikin tafasar zuciya kai kace Hauwa ce diyarta ta cikinta ba Sarham din ba. Abba Prof. Ma ya gyada kai kawai ya shige dakinsa don Mama ta gama yimasa jarumtar da shi ya kasa akan Sarham saboda yadda yake sonsa. Ya saura daga Sarham sai Hauwa a dakin Mama, ya ciro hankicinsa daga aljihunsa yana share zufar goshinsa. Ya dubi Hauwa cikin takaici tana kokarin tashi yace "koma ki zauna, nace ki tashi ne?" Hauwa ta koma ta zauna a kujerar dake fuskantarsa. Babu digon nadamar furucinta a tare da ita. "Da hadin bakinki Maijiddah aka shirya dagamin hankali haka? Daga zuwa na? Me nayi miki haka da zafi Maijiddah?" Hauwa tace cikin mamakinsa, "kamar yaya da hadin baki na? Wallahi Yaya Doctor kirana aka yi, bansan me ake yi ba, ta tambayeni ne kawai nikuma na bata amsa, nima Yayana na jini nake kallonka, banga amfanin cigaba da aurenmu ba". Ta kara da cewa "Yaya ka baro su Anti Madinah da Takwara ta Waheedah?" Takaici ya hanashi amsa mata, ya tsura mata Ido kawai yana cewa a ransa ita ko dan irin kishin nan nasa irin na Madinah bata yi. Bai taba jin Madina ta ce ya take ba balle lafiyar ta. Daga bisani ya mike ya finciki hannunta zuwa dakinsa, suna shiga ya maida kofar ya rufe, yace "Hauwa open your blank eyes, look into my eyes kice kin yarda mu rabu ki auri wani!". Hauwa ta fiddo manyan gululun idanunta a kansa tace, "ni Hauwa Bilyaminu, na yarda in rabu da auren Yaya Doctor sabida hakan zai fi mana alkhairi". Sarham ya sake mata hannu cikin mutuwar jiki yace "wallahi bazaku hadu keda Mamanki ku haukata ni ba". Muryarsa bakidaya ta dushe a sanda yake fadin hakan ya dafe kirjinsa dake zafi. Ya rasa me zai cewa Hauwa ya huce kawai sai ya girgiza kai yayi mata wani sakaran kallo kamar tana ganinsa y ace fitar min daga daki!. Ta kuwa juya da lalube ta kama handle din kofar ta bude tayi ficewarta. Bakin gadon sa ya koma ya zauna, kafin ya tashi ya kulle kansa ya rasa abunda yake masa dadi, haka ya rasa inda zai saka ransa. Ya rasa ta inda zai bullo musu. Abu na karshe da yasan bazai iya ba koda za'a dora masa wuka a makoshi shine sakin Hauwa. Ya samu kansa da daukar wayarsa yana kiran layin Hauwa karo na farko tun bayan tafiyar sa, shi kansa saida yaji kunyar kansa da kansa da yaga number dinta da sunanta na yawo akan screen din wayarsa. Mardiyya ta amsa wayar sannan ta miko mata kenan Mama ta shigo dakin, HAUWA na yin sallama batareda ta san wanda yayi kiranta ba. Da sauri Mama ta fauce wayar ta kashe sannnan ta rufe Hauwa da fada. "Yanzu don bakida hankali, kin rako mata, yau sai ya kiraki a waya ki dauka??? Wata goma sha biyu yayi ba kwana sha biyu ba tareda ya kira ki ba. Zuciyar ki kare ya cinye ne halan, ko kuwa mata kika rako duniya don kawai bakida Ido???" Hauwa batasan sanda hawaye ya tsinke mata ba. Ta sa gefen mayafin ta ta rufe fuska tana kuka. Mama tace "to daga yau na kwace wayar, in da ita zai bi ya samu lagonki ta hanyar bata miki lokaci. Dole in san matsayinki cikin rayuwar sa ko kuma ya bani takardar sakin ki". Bayan fitar ta daga dakin itama Mama Mai Shari'ah sai taji hawaye ya balle mata, kuma ba na komai bane na tausayin Hauwa ne. Ta san ba don nakasarta ba da yanzu wani zancen ake ba wannan ba. Itama har ga Allah bata so auren ya mutu, tana kwadayin samun tsatso dasu Inna da dawwama da rayuwa tareda Hauwa matsayin surukarta. Amma fifita bukatarta bai yuwuwa, hakan bazai hana ta kwatowa Hauwa 'yancin ta ba wanda addini da al'ada suka bata, don ta lura bata san ciwon kanta ba Sarham ya gama raina mata hankali. Kasa barci yayi a daren, ya kasa zaune ya kasa tsaye a dakinsa, daga karshe ya canza kayan jikinsa zuwa na barci, ya rufo dakinsa zuwa dakin Mama. Ya sameta tana karkade gadonta zata kwanta tana hawaye bata ko sharewa ba tareda ta san shigowarsa ba. Ba karamin tashin hankali Sarham ya kara shiga ba ganin Mama na kuka bata ko damuwa wani zai iya shigowa ya ganta. Ya zube gwiwoyinsa a kasa gabanta ya kasa cewa komai. Mama tayi karfin hali tace "Yaya dai? Takardar ka kawomin ince ko?" "Kiyi hakuri! Kiyi hakuri! kiyi hakuri Mama. Na tuba na bi Allah na biki". "Ai ba maganar inyi hakuri bane Sarham, amma in tambayeka. Shin Hauwa gunki ce ko dutse ko kuwa sassakata akayi? Bata da feelings kamar na kowacce mace?" Ya girgiza kai da sauri cikin jin kunya ya kara dukar da kai kasa. "To kaje kayi tunani kamar yadda nace daga yau zuwa gobe da safe, in bata da gurbin soyayya ko yaya a zuciyarka ka sahale mata qaddararren aurennan, ka koma inda ka fito". Haka ya taso ya fito daga dakin Mama cikin gigita, baya ko ganin gabansa sosai.
Chapter 3 · 0% Book details